An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 14 March 2010 10:58

Hankula Sun Kwanta A Kasar Georgia Bayan Jama'a Ta Fada Cikin Dimuwa

A yanzu dai hankula sun soma kwantawa a birnin Tibilisi da kuma sauran yankuna na kasar Georgia bayan da a yammacin jiya asabar wata tashar talbijin mai zaman kanta wacce kuma take goyon bayan gwamnatin kasar ta watsa wani mai rahoton karya mai cewa sojojin kasar Rasha sun kutsa a cikin kasar ta Georgia.A wannan rahoto da ta watsa a jiya a asabar , tashar ta talabijin mai suna Imedi TV ta bayyana cewa sojojin kasar Rasha da suka kutsa a cikin kasar ta Georgia sun kashe shugaban kasar Mikeil Saakash-vili kafin daga bisani a gano cewa wannan rahoto da tashar ta talabijin ta yada baya da tushe balantana makama. Daga karshe dai tashar ta talabijin ta ce ta watsa wannan rahoto ne domin tunawatar da al'ummar kasar cewa har kullum fa kasar Rasha na a matsayin wata babbar barazana ga kasarsu ta Georgia.A cikin wannan rahoto dai, tashar talabijin din ta yi amfani da tsoffin hotunan sojojin kasar Rasha ne a lokacin da suka mamaye yankin Osetiya ta kudu a cikin shekara ta 2008 a matsayin wani sabon kutse da sojojin na Rasha suka yi, lamarin da ya yi matukar tayar da hankulan jama'ar kasar.

Add comment


Security code
Refresh