An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 13 April 2016 03:36

Dawowar Alaka Tsakanin Babban Bankin Iran Da Bankunan Turai

Dawowar Alaka Tsakanin Babban Bankin Iran Da Bankunan Turai
Gwamnan babban bankin kasar Iran ya bayyana cewa an dawo da alaka ta hada-hadar kudade tsakanin babban bankin na kasar Iran da bankunan kasashen turai.

Gwamnan babban bankin na Iran Waliyullah Saif ya bayyana hakan ne a daren jiya, inda ya ce sun cimma yarjejeniya tare da gwamnan babban bankin kasar Italiya da yake cikin tawagar Firayi ministan kasar ta Italiya da yake ziyara a Tehran kan cewa, babban bankin Italiya zai zama hanyar fitar kudaden Iran zuwa dukkanin bankunan turai, hakan nan kuma kudade daga bankunan turai zuwa Iran.

Waliyullah Saif ya ce wannan mataki yana da matukar muhimmanci ga dukkanin kasashen biyu na Iran da Italiya, kuma hakan zai kawo karshen matsalar hada-hadar kudade tsakanin Iran da dukkanin kasashen nahiyar turai.

Add comment


Security code
Refresh