An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 08 March 2016 12:36

Norooz

Norooz
Sabuwar Shekarar Parsiawa Ta Bana

Norooz

1

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wanann fitowar ta shirin mu leka mu gani. Shiri ne dai wanda mu ka saba bijiro mu ku da batuuwan da su ka sahfi rayuwar yau da kullum.

To bisa la’akari da cewa an sabuwar shekarar parisawa ta zo karshe, kuma za a shiga wata sabuwar shekarar, shirin namu zai maida hankali ne akan yanyin Norooz.

Sai dai shirin namu na yau, na adabi ne kaco-kau, domin zai yi dubi ne akan wakokin baka da ake amfani da su a lokacin na Norooz.

Da fatan za a kasance a tare da mu domin a ji yadda shirin zai gudana.

****

Norooz dai shi ne sabon yanayin da ake shiga a farkon shekarar parisawa, wanda ya ke kunshe da wani yanyin na musamman. Lokacin da sanyi mai tsanani ya ke zuwa karshe, kuma itatuwa da tsire-tsire da su ke mutuwa su ke sake farfadowa zuwa sabuwar rayuwa.

A bisa dabi’a, wannan ya sa al’ummun da su ke ganin sauyin dabi’a irin wanann su ke yin farin ciki da gudanar da bukukuwa na godiya ga Allah madaukakin sarki wanda shi ne mai samar da sauyi a cikin yanayi.

A duk fadin kasar Iran da kuma kasashen da su ka yi tarayyar al’adu kamar Afghanistan da Tajikistan da Kurdawa da kasashen yankin Asiya ta tsakiya, bikin Norooz dade da kafuwa. Wata daya gabanin shiga sabuwar shekara, ake fara yin bukukuwa da su ke ci gaba har zuwa kwanaki 13 na farkon shekara.

A cikin ranakun karshn shekara, matasa da kuma makada kan zagaya kan tituna suna yi wa mutane busheara da zuwan karshen shekara da kuma shigowar sabuwar shekara. Ana kuma yin wasannin kwaikwayo akan tituna akan tituna.

Manufa ta farko ta yin wadannan wasannin shi ne cewa; bada busharar zuwan karshen Norooz da kuma shigowar sabon yanayi.

Abu Rayhan al-Biruny wanda masani ne dan kasar Iran, a cikin littafinsa na “al-tafahim’ ya Ambato wasu daga cikin al’adu daban-daban da ake amfani da su a lokaci Norooz. Daga ciki da akwai abinda ya yi kama da tashe a kasar Hausa ta yadda mai yin wasan kan yi shiga ta ban dariya.

Daya bisa uku da abubuwan da bukukuwa sabuwar shekara ta Parisawa da ake kira; Norooz ya kebanta da su, shi ne wakoki na musamman da ake rerawa a ranakun bukukuwan. A cikin yankuna irin su Gilan da Mazandaran da ke arewacin Iran wannan al'ada ta rera wakokin farin ciki da su ke kunshe da yabon dabi'a da kyawun da ke tattare a cikinta, sun fi zama ruwan dare. Bugu da kari, wasu daga cikin jigon da wakokin Norooz su ka kunsa da akwai yabon iyalan gidan ma'aiki, musamman ma dai Imamai masu tsaro.

Kuma matasa da su ne kan yi wakokin, suna samun kyautuka daga hannun manya goro da tukuici. Wakokin Norooz ana yinsu ne a cikin jam'i, ta yadda mutum guda ya ke bayar da wakar sauran kuma suna yi amshi.

Wasu daga cikin irin baitocin da ake rerawa suna cewa;

"Furanni sun tsiro a cikin lambu,

Tsuntsaye sun iso cikin garka.

Ya ku al'ummar annabi Muhammadu Noroz ya iso.

Waken da ake yi na ranar Norooz dai ya samo asali tun gabanin bayyanar addinin musulunci. Sannu a hanklai wanann al'ada ta sauya ta zama ta nishadi da debe kewa. Ana kuwa yinsu ne domin kare tsoffin al'adun Iran.

Masu yin waken Norooz suna amfani da salon kida daban wanda ya ke cike da kara.

Sai dai waken da ake kaantawa, mai sauki ne ba mai sarkakiya ba ta fuskar ma'ana da adabi.

Wasu salon na wake-waken Norooz sun kunshi bada labarai daban-daban. Masu bada wannan irin labarun kuwa suna amfani da kide-kide na al'umma. Suna bda bushara ne da cewa lokacin sanyi mai tsanani ya zo karshe an shiga sabon yanayi mai cike da iska da dadi da furanni su ke cika ko ina.

Wasu daga cikin wakokin sun kunshi cewa;

Idi mai dadi da dauke da farin ciki ya zo.

Lokacin in dariya ya zo.

Ku yi wa abokanku bushara cewar Norooz ya iso.

***

Watakila za a iya cewa idan baya ga bukukuwa na addini babu wani biki wanda ake rayawa a cikin kasashen da su ka yi tarayyar al’adun tsouwar Parisa, kamar Norooz. Kasashen da su ke yi tarayya akan wanann biki, saboda salon yanyin dabi’a da sauyin da ake samu samu a cikinta a wani lokaci na musamman na shekara, ya sa suna baiwa bikin muhimmanci. Lokaci na jaddada da sabunta rayuwa da kuma yin tsare-tsare domin sabuwar shekaara da za za shiga.

Add comment


Security code
Refresh