An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 28 February 2016 07:57

Ko Kun San Na (348) 12 Ga Watan Esfan Ahekara Ta 1394 Hijira Shamsia

Ko Kun San Na (348) 12 Ga Watan Esfan Ahekara Ta 1394 Hijira Shamsia
Yau Laraba 12-Esfand-1394 Hijira Shamsia=22-Jamada-Ula-1437 Hijira Kamria=02=Maris-2016 Miladia.

01- Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 60 da suka gabata a rana irin ta yau wato 2-Maris-1956 Miladia. Kasar Morocco ta sami 'yencin kanta daga turawan Faransa yan mulkin mallaka. Tun karni na 15 miladia ne kasar Morocco ta fada karkashin mamayar turawan Espania. Wannan halin ya ci gaba har zuwa shekara ta 1912 a lokacinda turawan Faransa suka maye gurbnsu. Kuma tun lokacin ne mutanen kasar suka fara yunkurin samun 'yencin kai tare da daukar Makamai. Turawan sun yi ta murkushe boren da ke faruwa tun lokacin, wadanda kuma suka hada da boren da Abdulkarim Raifi ya jagoranta. Amma a shekara ta 1956 Miladia turawan sun mika ikon kasar zuwa yan asalin kasar ta Morocco.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 12 da suka gabata a rana irin ta yau wato 2-Maris-2004 Miladia. Wasu boma boma masu karfi sun tashi a haramin Imam Husain (a) da ke karbala da kuma Haramin kazimiyya da ke birnin Bagdaza, inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu. Kafin haka dai gwamnatin sadam husain ta haramtawa yan shiya na kasar raya ranakun ashoora a kasar. Don haka bayan mamayar da sojojin Amurka da Britania suka yi wa kasar Iraqi yan shia sun sami damar raya wadan na kwanani . Amma hare haren boma boman suna daga cikin abubuwan da Amurkawan suka shigi da shi kasar Iranqi bayan mamayar.

03- Daga karshe masu sauaro ko kun san cewa shekaru 7 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22 -Jamadaula-1430Hijira Kamaria. Aya. Sheikh Mohammad Taqi Bahjat Foomy, daya daga cikin manya manyan malaman addini kuma masanin ilmin erfan ya rasu a birnin Qum na kasar Ira. An haifi Aya. Bahjati a shekara ta 1334 Hijira Qamaria a garin Foom da ke yankin gilan na arewacin kasar . Iran ya fara kaatu a gida sannan ya ji biranen Karbala da Najaf na kasar Iraqi inda ya kammala karatunsa. Bayan haka ya dawo gida Iran inda ya zabi zama a birnin Qum. Aya. Bahajat ya shahara da tsohon All.. da kuma ilmin erfani. ya rasu ne bayan rayuwa mai cike da albarka yana dan shekara fiye da 90 a duniya.

Add comment


Security code
Refresh