An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 28 February 2016 07:10

KomKun San Na (347) 11 Ga Watan Esfand -shekara Ta 1394 Hijirta Shamsia.

KomKun San Na (347) 11 Ga Watan Esfand -shekara Ta 1394 Hijirta Shamsia.
Yau Talata 10 ga watan Esfand -Shekara Ta 1394 Hijira Shamsia wacce ta yindai dai da 29-Jamada ula.1437 Hijira Kamaria. Har'ila yau wacce ta yi dai daida 1 ga watan Maris Shekara ta 2016 Miladia.

10- Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 41 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Esfanfa- 1353 H. Sh. Sarki Mohammad Riza Pahlawi na kasar Iran ya bada umurnin kafa jam'iyyar masim suna «رستاخیز ملت ایران» wato Jam'iyyar mutanen Iran. Wacce kuma ita ce jam'iyyar siyasa tilo a kasar. Manufar kafa wannan jam'iyyar ita ce samun damar jujjuya mutanen kasar Iran ta hanyar amfani da Jam'iyyar. Mutanen kasar Iran da dami sun yi watsi da shiga wannan jam'iyyar sun kuma bayyana hakan ya sabawa tsarin mulkin kasar. Banda haka Imam Khomaini (q) wanda yake gudun hijira a kasashen waje a llokacin ya bada umurni kan cewa mutanen kasar Iran su yi watsi da shiga wannan jam'iyyar. Amma duk tare da cewa gwamnatin sarkin tana tialstawa mutane shiga jam'iyyar da kuma tuhumar duk wanda yaki hakan da cin amanar kasa, mutane sun nuna adawarsu da yin hakan. Wannan dai ya tilastwa sarkin kawo karshen jam'iyyar shekaru uku bayan kafata.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 201 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Maris-1815Miladia. Sarki Napolio Banoporat na kasar Faransa ya koma kasar Ta faranfa ya kuma karbi iko da kasar na wasu kwanaki 100. Kafin haka dai shuwagabannin kasashen turai sun kama napolio sun kuma tilasta masa zama a tsibirin Albat na watannin 10 kafin wasu manya manyan sojojinsa masu biyayya a gare shi su kimani dubu guda suka kubutar da shi suka kuma maida shi kasar Faransa inda a rana irin ta yau ya soma wani mulki na tsawon kwanaki 100. Bayan haka a ranar 18-yuni -1815 ma turawan sun sake karawa da sojojinsa suka kama shi , a wannan karo suka tilasta masa zama a wani yanki a kasar Holanda ya ya butu bayan shekaru 6.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 827 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21-Jamada-Ula- 610 Hijira kamaria. Burhanuddeen Abul-Fath Aliyu Matrazi , babban malamin fiqihu, adabin larabci a karni na 7 hijira kamaria ya rasu. An haifi Burhanuddeen a garin Khawarizmi wanda yake karkashin sarakunan Iran na lokacin, a shekra ta 536 hijira kamaria. Ya kuma tashi a garin, infa ya fara ya kuma kammala karatunsa a gaban babban malami na zamaninsa wato Jarullah Zamakhshari, wanda shima ya kasashen masanin ilmin tafsirin alqur'ani da kuma hadisi. Matrizi ya rubuta littafai da dama daga cikinsu akwai "sharhin makamatul hariri" da kuma «المغرب فی لغة الفقه».

Add comment


Security code
Refresh