An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 24 February 2016 08:19

Zaben 'Yan Majalisa A Iran

                                       Zaben 'Yan Majalisa A Iran
Zabukan "Yan Majalisun Shawara da na kwararru a A Iran

Zaben Iran

4

Ranar 26 ga watan Febrairu da a ke ciki ne za a gudanar da zabukan 'yan majalisun shawara da kuma na kwararru a nan Iran. Zabuka ne wadanda tun a watannin da su ka gabata su ka ja hankalin kafafen watsa labaru. Zabukan da za a yi dai su ne za su ayyana makomar majalisar shawara da kuma ta kwararru masu zabar jagoran juyin juya hali. Wadannan majalisun guda biyu suna da matsayi na musamman a cikin tsarin jamhuriyar musulunci ta Iran.

Ita dai majalisar shawarar tana kula da yin dokoki ne, yayin da majalisar kwararru ta ke kula da zabar wanda zai zama jagoran juyin juya halin musulunci.

Yin zabe, yana daga cikin muhimman batutuwa masu muhimmanci da tun farkon cin nasarar juyin musulunci jagoransa, wato marigayi Imam Khumaini (r.a) ya ke jaddada matsayinsa. Bayan wafatin Imam Khumain, Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ci gaba da bayyana matsayin da ya ke da shi.

A bisa mahangar Ayatullah Sayyid Ai Khamnei, yin zabe yana da matsayin da ya dara batun hakki da doka a karkashin tsarin demokradiyya irin ta yammacin turai. Jagoran yana fadin cewa:

" Fitowa domin yin zabe wani wajibi na siyasa da kuma na addini.. Wanann shi ne batu mafi muhimmanci akan zabe, wato fitowar mutane."

Baya ga fitowar mutane maif rinjaye a wurin zabe, wani batun mai muhimmanci shi ne; zabar wanda ya fi cancanta a tsakanin mutanen da dukkaninsu suna da inaganci.

Ayatullah sayyid Ali Khamne yana fadin cewa;

" A jamhuriyar musulunci ta Iran, ana zabar wanda ya fi cancanta ne, ba hamayya ba ce. Wajibi ne mutane su bude idanu su kuma yi amfani da basirar da su ke da ita, domin su zabi mutanen da su ke da tabbaci akansu."

Shakka babu dukkanin wadanda su ka tsaya takara an tantance su ta hanyar majalisar da ta ke kula da kundin tsarin mulki. Kuma mafi rinjaye mutane ne wadanda su ke da inganci da cancanta da rike mukami. Kuma saboda wadannan mukaman basu da yawa, sanann kuma babu yadda za a yi fiye da mutum guda ya rike su, babu makawa sai mutane sun zabi wanda ya fi dacewa a tsakanin mutanen da dukkkaninsu suna da cancanta. Domin kuwa duk mutumin da ta hanyar doka aka tabbatar da cewa zai iya tsayawa takara to yana da cancanta, don haka babu makama a duba a tsakanin wadanda su ka cancanta a zabi wanda ya fi cancanta.

Wasu daga cikin ma'aunai na zabar wanda ya fi cancanta, kamar yadda jagoran juyin musulunci ya sha bayyanawa sun kunshi imani da takawa da tausayawa al'umma da kuma iya tafiyar da sha'anin mulki da daukar nauyin da ya rataya a wuya. Da kuma yin tsayin daka wajen fuskantar makiya da fada da talauci da cin hanci da rashawa da kuma nuna wariya domin shimfida adalci da ci gaban kasa.

Kuma su kansu mutane da su ke zabar wadanda za su tafiyar da harkokin mulki na kasa ta fuskokin doka suna kara tabbatar da tsarin musulunci ne. Da haka ne tsarin musulunci ya ke kara bayyana karfinsa a duk lokacin da aka gudanar da zabe. Kuma kamar yadda jagoran juyi ne ya ke fada akan zaben da cewa, yana nuni ne akan rayuwa da kuma karfin sanin ya kamata na al'ummar Iran.

Fitowar da mutane su ke ckwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri'a a lokacin zabe, kare halarcin tsarin jamhuriyar musulunci ta iran ne baya ga kare daukaka da matsayinta, haka nan kuma yana nuni da yadda tsarin mulki kasa ya ke aiki. Wadannan su ne dalilan da su ka sanya, makiyan al'ummar Iran ba su son ganin an fito domin yin zaben.

Jagoran juyin musulunci na Iran a cikin jawabansa akan zaben ya sha yin magana akan muhimmancin fitowar al'umma kwansu da kwarkwatarsu. yana cewa:

"Abinda mutane su ke so, shi ne kada mutane su fito su yi zabe. Suna son ya zama wani makami na raunana tsarin jamhuriyar musulunci.. suna da masaniya akan cewa fitowar mutane su yi zabe, yana bai wa mutane karfi ne, saboda haka makiyan ba za su iya cimma manufarsu ba akan Iran."

**

Yau da gobe ta tabbatar da cewa fitowar mutane kwansu da kwarkwatarsu domin yin zabe, baya ga kasantuwarsa mai karfafa tsarin jamhuriyar musulunci a Iran, a lokaci gudan kuma yana bakantawa makiya juyin musulunci. A bisa mahangar siyasa ta jagoran juyin musulunci, tsarin al'umma na addini yana a matsayin wani ginshiki ne da ya ke karfafa al'ummar Iran. Hakan kuwa zai tabbata ne idan ya zamana al'umma suna fitowa zabe cikin sanin abinda su ke yi da manufar da su ke son cimmawa.

A hakikanin gaskiya, dukkanin al'ummar da su ke cikin al'umma wajibi ne su kasance masu jin suna nauyin da ya rataya a wuyansu dangane da makomar kasarsu. Hakan kuwa ba za ta tabbata ba sai ta hanyar fitowar al'umma masu yawa domin kada kuri'a.

Add comment


Security code
Refresh