An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 18 February 2016 06:59

Ko Kunsan Na (339) 3 Ga Watan Esfand Shekara Ta 1394 Hijira Shamsia

Ko Kunsan Na (339) 3 Ga Watan Esfand Shekara Ta 1394 Hijira Shamsia
Yau Litinin 03 Ga Watan Esfand Shekara Ta 1394 Hijira Shamsia. Wacce ta yi dai dai da 13 ga watan Jamada- Ula Shekara ta 1437 Hijira Kamaria. Har'ila Yau wacce ta yi dai dai da 22 ga watan Febrerun Shekara ta 2016 Miladia

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1426 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13 ga watan Jamada -Ula shekara ta 11 Hijira Kamaria. Fatima Zahra(s) diyar Manzon All..(s), Matar Amirul muminina Aliyu bin Abitalib (a) sannan mahaifiyar Imam Hassan da Husain (a) , bayan gajeruwar rayuwa cike da albarka da kuma alkhairi ta yi shahada. An haifi Fatima Azzahra (a) a Makka bayan mahaifinta ya zama manzo da shekaru 5. Sannan ta sami tarbiyan daga wajen mahaifinta manzon Al...(s). Matsayinta a wajen All..(a) ya kai ga manzon All.. (s) yana fadi dangane da ita kan cewa " All.. yana yarda da yardanta yana kuma fushi da fushinta. Yace ita ce shugaban matan Aljanna. Kuma ita tsoka ce daga jikinsa. Fatima Azzahra (s) ta tarbiyantar da yayanta Imam Husan da Husain (a) wadanda manzon Al...(s) ya ce sune shuwagabanin samarin Aljanna. Fatima (s) kekyawar misali ce ga mata musulmi kuma, rayuwanta na cike da darussa na zaman aure da mahaifiya mai tarbiyantar da yayanta. Bayan rasuwar mahaifinta fiyayyen halittu da kimani watanni 6 kamar yadda ya zo a cikin wasu ruwayoyi, matsalolin siyasa da suka kunno kai a lokacin suka sauya rayuwanta suka kuma yi sanadiyar barinta wanan duniya da sauri. Muna mika ta'aziyyar mu al-ummar musulmi musamman mabiya mazhbar iyalan gidan manzon All...(s) da wannan rashin.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1365 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13 ga watan Jamada-Ula shekara ta 72 Hijira kamaria. Ibrahim dan Malikul Ashtar, daya daga cikin komandojojin sojoji masu yunkurin daukar fansar jinin Imam Husain(a) jikan manzon All..(s) da sahabbansa da aka kashe a karbala ya yi shahada. Ibrahim dai ya yi yaki Mu'awiya dan abin saufyan karkashin Amirul muminina Aliyu bin Abitalib (a) da kuma mahaifinsa Malaikul Ashtar a siffin a lokacinda yake matashi. Sannan a lokacinda Mukhtar athaqafi ya fara yunkurin fansar jinin shahidan karbala ya kasance tare da shi, har ya karbi ikon garin Musil na kasar Iraqi. Amma bayan da sojojin Mus'ab bin Zubai suka kwace kufa suka kashe Mukhtar, Ibrahim ya ga bai da zabi in banda yi wa Mus'ab bin zubai bai'a amma a ci gaba da yakar Abdul Malik ban Marwan sabofa ha'incin wasu sojoji an kashe shi a yakin.

03-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 10 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22 ga watan Febrerun shekara ta 2006 Miladia. Wasu boma bomai masu karfi sun tashi a haramin Imam Al-hadi da kuma Imam Al-askari (a) a birnin Samira da ke arewacin birnin Bagdaza a kasar Iraqi. Imam Al-Hadi da kuma Imam al-askario (a) jikokin manzon Al...(s) ne wadanda suka kasance jikokin manzon All...(s) sannan su, abin girmamawa ne ga dukkan musulmi musamman mabiya mazhabar Ahlulbaiti (a). A lokacinda wadan nan boma bomai suka tashi dai sojojin Amurka wadanda suke mamaye da kasar Iraqi ne suke iko da garin. Don haka masana da dama sun bayyana cewa dun wadanda suka tada boma boman ya hada baki da su kuma manufarsu shi ne haddasa fadan addini tsakakin musulman kasar. Amma malaman shi'a sun jakunnen mabiyan kan hakan, don haka makiya basu kai ga burinsu ba.

Add comment


Security code
Refresh