An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 16 February 2016 04:25

Ko Kun San Na (336) 30 Ga Watan Bahman Shekara Ta 1394 Hijira Kamaria

Ko Kun San Na (336) 30 Ga Watan Bahman Shekara Ta 1394 Hijira Kamaria
Yau Jumma'a 30 ga watan Bahman Shekara ta 1394 Hijira Kamaria. Wacce ta yi dai dai da 10 ga watan Jamada-ula Shekara ta 1437 Hijira Kamaria. Har'ila yau wacce tayi dai dai da 19 ga watan Febreru na shekara ta 2016 Miladia

01- Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 6 da suka gabata a rana irin ta yau wato 30 ga watan Bahman shekara ta 1388 hijira shamsiya. Masana a kasar Iran sun sami nasarar gina jirgin ruwan yaki na zamani a karon farko, ya kuma fara aiki a yankin tekun farasi na gudancin kasar. Jirgin wanda ake kira Jamaran, yana da kayakin aiki na zamani wadanda zasu iya fuskantar makiya daga sama kan ruwa da kuma karkashin ruwa. Har'ila yau Jameran yana da kayakin aikin wadanda suka hada da rada mai saurin gono makiya, yana da filin saukar jirgi mai saukar Ungulu. Kafin haka dai irin wadan nan jiragen sun takaita ne a hannun tsirarun manya manyan kasashen duniya wadanda suka hada da Amurka da wasu kasashen turai. Wanna kuma ya sanya iran daga cikin kasashen da suke da fasahar gina irin wadan nan jirage ba tare da neman taimakon wani daga waje ba.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 543 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19 ga watan Febreru shekara 1473 Miladia. Aka haifi Nicolas Copernicus wani masanin ilmin taurari da lissafi a kasar Polanda. Nicolas ya fara karatun taurari ne sannan ya shiga neman ilmin likitanci daga nan ya sake dawowa kan ilmin taurari, inda wannan karon a shekara ta 1503 ya yi bincike har ya gano cewa duniyarmu ce take zagaya rana sannan tana zagaya kanta da kanta sau daya a ko wace dare da rana. Nicolas ya rasu a shekara ta 1543 Miladia bayan an buga littafinsa mai suna {Zagayawar jikunkuna a cikin sararin samania } da yan kwanaki.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 19 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19 ga watan Febrerun shekara 1997 Miladia. Deng-Zioping tsohon shugaban kasar China (sin) ya rasu yana dan shekara 92 a duniya. Zioping shi ne shugaban kasar sin wanda ya gabatar da gagarumin aiki na ci gaba a bangaren tattalin arziki, siyada da kuma masana'antu ga kasar China karkashin tsarin gurguzu wacce yayi mata koskorima. A shekara 1990 Miladia bayan shigar da kasar China (sin) cikin makasashen masu arzikin masana'antu da karfin tattalin arziki a duniya, shugaban Zioping ya ajiye dukkan ayyukan gwamnatin kasar da yake rike da su sabuda tsofa fa kuma rashin lafiya. A wannan halin ya ci gaba da rayuwa har zuwa mutuwar a rana irin ta yau.

Add comment


Security code
Refresh