An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 16 February 2016 03:44

Ko Kun San Na (335) 29 Ga Watan Bahman Shekara Ta 1394 Hijira Kamaria

Ko Kun San Na (335) 29 Ga Watan Bahman Shekara Ta 1394 Hijira Kamaria
Yau Alhamis 29 Ga watan Bahman Shekara ta 1394 Hijira Kamaria Wacce tari dai dai da 09 ga watan Jamada -Ula Shekara ta 1437 Hijira Kamaria, har'ila yau wacce ta yi dai dai da 18 ga watan Febreru shekara ta 2016 Miladia

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 90 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18 Febrerun shekara ta 1926 Miladia. Sojojin hadin guiwa tsakanin kasashen Faransa da Espania yan mulkin mallaka sun sami nasara kan yunkurin mutanen kasar Morocco na korar yan mulkin mallaka daga kasarsu karkashin jagorancin Amir Abdulkadeer Raifi. A lokacin ne suka Kama Amir Raifi suka tilasta masa komawa kasar Afrika ta kudu da zama. Da farko dai Abdulkareem Raifi ya fara gwagwarmaya da turawan Espania wadanda suke mamaye da wani magare na kasar Morocco ne a shekara ta 1912. Sannan a shekara ta 1921 sojojin Raifi sun sami gagarumin nasara a kan Turawan Espani, harma wasu yankuna a kasar sun shelanta kafa tsarin jumhuriya a kasar. Amma sai Faransawa wadanda suke da wani bangaren na kasar ta Morocco suka kawo dauki wa turawan Espania inda suka yi wa mutanen Raifi kisan kiyashi . Daga karshe a shekara ta 1926 suka kawo karshen boren suka kuma kana Amir Raifi suka kore shi daga kasar sannan suka shimfida mulkin mallaka kan mutanen kasar.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 51 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18 ga watan Febrerun shekara ta 1965 Miladia. Kasar Gambia ta sami 'yencin kanta daga turawan Ingila yan mulkin mallaka. turawan sun fara mulkin mallakar kasar Gambia ne tun shekata 1588Miladia. Kasar Zambia ce kasar ta turawan Ingila suka fara yiwa mulkin mallaka a Afrika. Sannan wannan halin ya ci gaba har zuwa karnuka hudu, inda bayan kwace dimbin arzikin da All.. ya yi kkasar Turawan suka mikawa mutanen kasar 'yencin gashin kai a shekara 1963Miladia. Sannan a shekara ta 1970 Miladia ta zama jumhuriya . Kasar Gambia tana da kadin kasa kilomita murabba'ee dubu 11295 kuma tana na mutane wadanda yawansu ya kai miliyon guda da yan kai. Mafi yawan mutanen kasar Gambia musulmi ne.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 17 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18 ga watan Febrerun shekara 1999 Miladia. Jami'an tsaron kasar Iraqi karkashin shugabancin Sadam husain sun bindige Aya. Sayyeed Mohammad Sadiqussadir babban marja'e a cikin malama shiai, inda suka kaishi ga shahada. Kafin haka dai gwamnatin Sadam husain ta kashe wasu malaman shia wadanda take daukarsu a matayin barazana ga mulkinta a kasar. Fitatun wadanda ta kashen sun hada da Aya. Garawi da kuma Aya. Burujadi. Bayan kisansu a cikin shekara guda, da kuma kisan Aya. Sadar mutanen kasr kasar sun shirya gagarumin zanga zanga inda suka dorawa gwamnatin kasar kissan babban malamin.

Add comment


Security code
Refresh