An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 26 September 2015 18:52

Hukumar Alhazai Ta Iran: Alhazan Kasar Iran Ne Suka Fi Yawa A Cikin Wadanda Suka Rasu A Mina

Hukumar Alhazai Ta Iran: Alhazan Kasar Iran Ne Suka Fi Yawa A Cikin Wadanda Suka Rasu A Mina
Har yanzu hukumomin Saudiyya ba su bayani a hukumance ba kan adaddin mutanen da suka rasu da kuma kasashensu, yayin da wasu daga cikin kasashen duniya suka fara sanar da adadin alhazansu da suka rasa rayukansu ko suka bata a turereniyar da ta wakana a Mina.

 

Hukuma mai kula da ayyukan hajji a Iran ta sanar da cewa, ya zuwa yanzu adadin alhazanta da suka rasu sakamakon abin da ya faru a Mina ya kai 136 yayin da wasu fiye da 300 ba a san makomarsu ba, yayin da Najeriya har yanzu babu wani takamaiman bayani kan adadin mutanen da suka rasu, duk kuwa da cewa wasu amjiyoyi na cewa mautane 3, a alhazan Nijar kuma an sanar da cewa mutane 19 ne suka rasu, wasu kimanin 50 kuma baa san makomarsu ba.

Bisa irin bayanan da suke fitowa daga Saudiyya, alhazan kasar Iran ne suka fi mutuwa da kuma salwanta a wannan mummunan hadari na Mina, yayin da wasu rahotanni ke cewa daga cikin wadanda suka rasu har da jami’an diplomasiyyah 6 na kasar ta Iran.

 

 

Add comment


Security code
Refresh