An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 22 June 2015 18:48

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {16}

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {16}
Sallar Idi karama. Musulmai suna da manyan bukukuwan salla guda biyu da suke da muhimmanci a addinin musulunci, wato sallar idi karama da sallar idi babba wadanda ake kiransu da Idul-Fitir da Idul-Adhha a larabce.

 

Sallar Idul-Fitir itace karamar salla da ake gudanar da ita bayan kare azumin watan ramalana mai alfarma wato ranar farko ga watan shawwal, yayin da Sallar Adhha kuma itace babbar salla da ake gudanar da ita a ranar goma ga watan Zul-Hajji.

 

Hakika Allah Madaukakin Sarki yayi umurni da yin wata kebabbiyar salla a wadannan ranakun biyu da ake kirar sallolin da sallar Idi. Wajibi ne halattan sallar ta idi a zamanin Imami Ma’asumi {a.s} yayin da a zamanin da baya tsakanin mutane wato lokacin gaiba, sallar take mustahabi.

 

A wannan lokaci da gudanar da sallar idi take mustahabi, ya halatta mutum yayi ta shi kadai, kamar yadda ya halatta yayi ta a cikin jama’a wato jam’i. Idan kuma za a gudanar da sallar ta idi ce cikin jam’i, to ba sharadi ba ne sai an samu wasu adadin mutane na musamman kamar yadda yake a sallar juma’a.

 

Sallar Idi raka’a biyu ce kamar sallar Asubahi wanda lokacinta yake farawa daga fitowar rana zuwa gotawarta, kuma idan lokacin sallar ta idi ya fice ba a ramakon sallar. Kuma yana daga cikin ladubanta na mustahabi yin wanka kafin sallar ta idi.

 

Yadda ake yin sallar idi ita ce:-

 

Bayan kudurta niyyar sallar, mutum zai yi kabbarar harama, inda a raka’a ta farko zai karanta fatiha da surah, sannan yayi kabbarori biyar, inda a bayan kowace kabbara zai yi kunuti, sannan bayan gama kunuti na biyar sai mutum yayi wata kabbara domin dukawa zuwa ruku’u, inda bayan ruku’u zai yi sujjada biyu, sanna sai ya mike domin kawo raka’a ta biyu, inda a wannan raka’ar zai karanta fatiha da surah sannan yayi kabbara hudu, inda a bayan kowace kabbara zai yi kunuti, sannan bayan gama kunuti na hudu sai mutum yayi wata kabbara domin dukawa zuwa ruku’u sannan bayan dagowa daga ruku’u ya duka zuwa sujjada har ya idar da sallarsa.

 

Mustahabi ne da aka fi so mutum ya karanta suratush-shams bayan fatiha a raka’a ta farko, sannan a raka’a ta biyu ya karanta suratul-Ghashiya, ko kuma a raka’a ta farko ya karanta Suratul-A’alah, sannan a raka’a ta biyu ya karanta Suratush-Shams.

 

Ya halatta a kunutin da mutum zai yi yayi kowace irin addu’a ta hanyar rokon Allah da yin godiya a gare shi, amma mustahabi ne mutum a yayin kunutin ya karanta addu’ar da aka ruwaito a cikin littattafan addu’a wadda ke dauke da cewa:-

 

Allahumma Ahlal-kibriya’i wal-Azamah, Wa- Ahlal- Judi waj-Jabaruti Wa- Ahlal-Afwi War-Rahamah Wa-Ahlat-Takawa Wal-Maghfirah As’aluka fi- hazel-Yaumil-Lazi Ja’altahu lil-muslimina Idah…. Har zuwa karshen addu’ar.

 

Idan kuma mutum bai haddace addu’ar ba, to ya halatta ya dauki takardar addu’ar ko littafi yana karantawa a cikin sallar, kamar yadda mustahabi ne; daga hannaye sama a lokacin kowace kabbara.

 

Mustahabi ne idan za a gudanar da sallar ta idi cikin jam’i, Liman yayi hudubobi biyu bayan idar da sallar, inda zai rabe tsakanin hudubobin biyu da dan gajeren zama a tsakani.  

 

Idan mutum zai gudanar da sallar idi ne a cikin jam’i a matsayin Mamu da ke koyi da liman, to Liman ya dauke masa karatun fatiha da surah, amma duk sauran ayyukan salla zai gudanar da kansa.

 

Babu kiran salla ko tada Ikamah a sallar idi, amma mustahabi ne idan za a fara gudanar da sallar a jam’i ace “ Assalah” "Assalah" sai uku.

 

Ayyukan Ranar Sallar Idi Karama:-

 

Mutum ya fitar da zakkan fidda- kai wa kansa da na mutanen da suke karkashinsa, inda kowace rai zai fitar mata da sa'i guda, Sa'i guda yana nufin kilon hatsi uku, kuma zakkan fidda-kan ya kasance abinci ne misalin shinkafa, alkama, dabino, sha'ir, dawa, masara, gero ko kuma duk wani abin da mutanen kasa ko gari suke amfani da shi a matsayin abinci.

 

Ihtiyadi ne ga wanda zai yi sallar idi ya fitar da zakkan fidda- kai kafin yayi sallar. kamar yadda muka yi bayani a shirinmu da ya gabata kan fitar da zakkan fidda-kai.

 

Yana daga cikin ayyukan mustahabi na ranar sallar idi karama yin kabbarori bayan sallar Asubahi da bayan sallar ta Idi. Kabbarorin kuwa sune kamar haka:-

 

Allahu Akbar, Allahu Akbar, La'ilaha illallahu, Wal-Allahu Akbar, Allahu Akbar, Walillahil-hamdu. Alhamdu-lillahi Ala Ma Hada'na, Walahush-Shukru Ala Ma Aula'na.

 

Yin wanka kafin fita zuwa sallar Idi kuma sallar ta Idi ta kasance an gudanar da ita ce a karkashin sararin samaniya wato ba a karkashin rufi ba.

 

Sanya kyakkyawar tufa da fesa turare.

 

Cin abinci a farkon ranar Idi kafin gudanar da sallar ta Idi kuma abin da aka fi so shi ne mutum ya fara da cin dabino ko wani abu mai zaki. Mutum ya fita zuwa sallar Idi bayan rana ta fito.

Add comment


Security code
Refresh