An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 22 June 2015 18:45

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {15}

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {15}
Zakkatul- Fitir Wato Zakkan Fidda- Kai.

 

Zakkan fidda-kai wajibi ne daga cikin wajibai masu karfi a addinin musulunci kuma sharadi ne na karban azumin watan ramalana.

 

Wajibi ne a kan dukkan musulmin da ya cika wasu sharudda da zamu ambata ya fitar da zakkan fidda-kai, sharuddan kuwa sune:-

 

{1} Balaga:- Fitar da zakkan fidda-kai ba wajibi ba ne a kan yaron da bai balaga ba, wato bai ciki shekarun da hukunce -hukuncen shari'ar musulmi suka hau kansa ba, don haka koda yaro yana da dukiya ba za a fitar da zakkan fidda-kai a cikin dukiyarsa ba.

 

{2} Hankali:- Fitar da zakkan fidda-kai ba wajibi ba ne a kan mahaukaci, don haka mahaukacin da yake da dukiya ba za a cire zakkan fidda- kai a cikin dukiyarsa ba.

 

{3} Rashin Suma:- Fitar da zakkan fidda- kai ba wajibi ba ne a kan wanda ya suma, suman da ya kai matsayin da ya fice daga cikin hankalinsa kafin faduwar rana har shigan daren sallar idi. 

 

{4} Rashin Bauta:- Fitar da zakkan fidda- kai ba wajibi ba ne a kan bawa da yake karkashin ubangidansa.

 

{5} Wadata:- Fitar da zakkan fidda- kai ba wajibi ba ne a kan matalauci wato mutumin da bai mallaki abincin da zai isheshi shi da iyalansa a shekara ba, ko kuma dan abin da yake samu ta hanyar albashi ko sana'a ba su isar da shi wajen ciyar da iyalansa a shekara ba, misali da za a tattara dukkan abin da mutum yake samu ta hanyar albashi ko sana'a a shekara guda, ba zai ishe shi wajen ciyar da kansa da iyalansa a tsawon shekarar ba, to irin wannan mutum shi ake kira da mabukaci don haka fitar da zakkan fidda- kai ba wajibi ba ne a kansa.

 

Hukunce-hukuncen fitar da zakkan fidda-kai.

 

Kafin fitar da zakkan fidda-kai ya wajaba a kan mutum, dole ne sai ya cika dukkanin sharuddan da muka ambata kafin faduwar ranar karshe ta watan ramalana wato kafin shigan dare sallar idi koda kuwa saura kiris ne ranar ta fadi mutum ya cika sharuddan.

 

Idan mutum ya cika dukkanin sharuddan fitar da zakkan fidda-kai kafin faduwar ranar karshe ta watan ramalana, misali mahaukaci ya warke daga hauka kafin faduwar ranar karshen watan ramalana  ko yaro ya balaga kafin shigan daren sallar idi ko kuma talaka ya mallaki abincin da zai isheshi da iyalansa a shekara kafin faduwar ranar karshen watan ramalana, to dukkaninsu idan sun cika sauran sharuddan, wajibi ne su fitar da zakkan fidda- kai.

 

Idan mutum ya cika dukkanin sharuddan fitar da zakkan fidda-kai amma ana sauran kiris rana ta fadi a ranar karshe ta watan ramalana mai alfarma sai ya rasa daya daga cikin sharudda fitar da zakkan fidda-kan, misali hauka ta bijiro masa ko ya suma ko kuma ya talauce, to wajabcin fitar da zakkan fidda- kai ya fadi a kansa, wato ba dole ba ne ya fitar da zakkan fidda-kai.

 

Mustahabi ne idan mutum ya cika dukkanin sharuddan fitar da zakkan fidda-kai bayan da rana ta riga ta fadi a ranar karshen watan ramalana wato bayan shigan daren sallar idi, ya dauki matakin cire zakkan fidda-kai, misali mutumin da ya farfado daga suma bayan shigan dare sallar idi ko wanda ya warke daga hauka bayan shigan daren da makamatansu. Kai duk mutumin da ya cika sharuddan fitar da zakkan fidda-kai bayan shigan daren sallar idi har zuwa ranar sallar idi kafin gotawar rana wato kafin shigan lokacin sallar azahar, to mustahabi ne a gare shi ya fitar da zakkan fidda-kai.

 

Haka nan mustahabi ne ga matalauci wanda baya da ishasshen abin da zai ci shi da iyalansa na tsawon shekara ya fitar da zakkan fidda-kai.

 

Mustahabi ne ga mabukacin da bai mallaki komai ba sai sa'i daya wato gwargwadon zakkan fidda-kai na mutum guda, ya fitar da zakkan fidda-kai wa kansa. Idan kuma yana da iyalai wadanda suke karkashinsa, to idan ya cire zakkan fidda-kan sai ya bai wa daya daga cikin iyalansa misali matarsa, ita ma sai ta bai wa danta, shi ma ya bai wa kaninsa, haka dai har ya zagaya kan dukkanin iyalan gidan, sannan na karshe shi kuma ya bai wa mabukaci wanda baya daga cikin iyalan gidan.

 

Idan kuma a cikin iyalan gidan mabukacin akwai yaron da bai balaga ba, to idan zakkan fidda-kan ta zagaya kan wadanda suke  baligai, sai na karshensu ya bai wa mahaifinsu shi kuma sai ya bai wa mabukaci na daban da baya daga cikin iyalan gidansa a matsayin zakkan fidda-kan yaronsa da bai balaga ba. Wato lokacin da zakkan ya dawo hannunsa ya zama mallakarsa shi kuma sai ya fitar da zakkan fidda-kan yaronsa da bai balaga ba.

 

Idan kuma har na karshen ya bai wa yaron da bai balaga ba, to a nan ba za a karba a bai wa wani ba, sai dai a yi hidima wa yaron da zakkan domin yaro baya cire zakkan fidda kai wa kansa.

 

Mutanen Da Ake Fitar Musu Da Zakkan Fidda- Kai.

 

Wajibi ne a kan mutumin da ya cika dukkanin sharuddan fitar da zakkan fidda-kai, ya fitar da zakkan wa kansa da kuma wadanda suke karkashinsa kamar haka:-

 

-1- Wajibi ne mutum ya fitar da zakkan fidda-kai ga mutanen da wajibi ne ya ciyar da su daga iyalan gidansa kuma yake ciyar da su din a aikace. Wato cin su da shan su yana hannunsa. Misali matarsa da ‘ya'yansa da mahaifansa. Amma idan ya kasance su suke ciyar da kansu, to fitar musu da zakkan fidda- kai ba wajibi ba ne a kansa.

 

-2- ‘Yan uwansa da makusantansa wadanda suke rayuwa a karkashin kulawarsa kuma yake ciyar da su. Misali dan uwansa ko ‘yar uwarsa ko kuma danginsa maza da mata, yara da manya, musulmai da wadanda ba musulmai ba, dangin kusa dana nesa, matukar dai suna cikin wadanda suke karkashin kulawansa.

 

-3- Masu yi masa hidima wadanda suke rayuwa a gidansa kuma yake ciyar da su tare da daukar nauyinsu da dawainiyarsu. Amma masu yi masa hidima daga ma'aikatansa da suke zaman kansu  koda kuwa suna cin abinci a gidansa, su basu daga cikin wadanda wajibi ne a kansa ya fitar musu da zakkan fidda- kai.

 

-4- Bakinsa da suka sauka a gidansa ko wajensa kafin faduwar ranar karshen watan ramalana wadanda zasu kwana a gidansa karkashin liyafarsa koda kuwa ba su kai ga cin abinci ba, matukar dai su bakinsa ne kuma sun shiga karkashin kulawarsa kafin shigan daren sallar idi. Misali 'yan uwansa, abokanansa da duk wani bakon da ya sauka a wajensa ta kowace hanya ko sanadiyya.

 

Amma mutanen da ya gayyata domin shan ruwa a gidansa a daren sallar idi, su kam ba su daga cikin wadanda zai fitar musu da zakkan fidda- kai.

 

Hukunce-Hukuncen Zakkan Fidda-Kai:-  

 

-1- Idan aka yi haihuwa wa mutum kafin faduwar ranar karshen watan ramalana ko danginsa suka sauka a gidansa domin gudanar da bukukuwan sallah kuma sun kasance a karkashinsa kafin shigan dare, to wajibi ne dukkansu ya fitar musu da zakkan fidda-kai.

 

Amma idan an yi haihuwa wa mutum ne bayan faduwar ranar karshen watan ramalana ko bako ya shiga karkashinsa bayan faduwar rana wato bayan shigan daren sallar idi, to fitar musu da zakkan fidda- kai ba wajibi ba ne, sai dai fitarwar mustahabi ne.

 

-2- Idan mawadaci ya shiga karkashin wani mutum ta hanyar bakonta kafin faduwar ranar karshen watan ramalana ko kuma duk da wadatar mutum wani ne yake daukar nauyinsa da dawainiyarsa, to fitar da zakkan fidda-kai ya fadi a kan mawadacin wato mutumin dake daukar dawainiyarsa ne zai fitar masa da zakkan-fidda kai.

 

-3- Mutumin da fitar da zakkan fidda-kansa ya rataya a wuyar wani mutum na daban, to fitar da zakkan ya fadi a kansa, amma idan wanda hakkin fitar da zakkan ya rataya a wuyarsa yaki fitar masa da zakkan da gangan, ko kuma bai fitar masa da zakkan ba bisa mantuwa, duk da haka dai fitar da zakkan ba wajibi ba ne a kansa, amma ihtiyadi ne mustahabi ya fitar wa kansa da zakkan.

 

-4- Mutumin da fitar da zakkan fidda kansa ya rataya a wuyar wani mutum na daban misalin mahaifinsa, sai ya zame mahaifinsa mabukaci ne wato bai mallaki abincin shekara guda ba, to idan shi yana da wadata ya fitar da zakkan wa kansa.

 

Jinsin Abincin Da Ake Fitarwa Da Yawansa Da Kuma Wadanda Ake Ba Su Zakkan na Fidda-Kai.

 

-1- Wajibi ne zakkan fidda-kai ya kasance abinci misalin shinkafa, alkama, dabino, sha'ir, dawa, masara, gero ko kuma duk wani abin da mutane kasa ko gari suke amfani da shi a matsayin abinci.

 

-2- Abincin da mutum zai fitar da shi a matsayin zakkan fidda kai ya kasance mai kyau ne ba gurbatacce ba.

 

-3- Ya halatta idan mutum zai fitar da zakkan fidda-kai ya fitar da kimarsa na irin kudin kasarsu ko kudin da ake amfani da shi a duniya a halin yanzu.

 

-4- Yawan abin da ake fitar wa kowace rai, shi ne sa'i guda wato kilo uku. Kilo uku shi ne zakkan fidda-kan kowace rai.

 

-5- Lokacin fitar da zakkan fidda-kai ya kan fara ne daga shigan daren sallar idi zuwa gotawar ranar sallah wato lokacin shigan sallar azahar.

 

Amma ana so mutum ya jinkirta fitar da zakkan na fidda-kai zuwa fitowan alfijir na ranar sallah kuma ihtiyadi ga wanda zai yi sallar idi ya fitar da zakkan fidda- kan kafin yayi sallah.

 

-6- Idan mutum ya fitar da zakkan fidda kai zai iya ajiyewa har lokacin da za a samu wanda ya cancanci a bashi zakkan, haka nan idan mutum ya cire zakkan fidda-kai, to ya hanzarta mikawa ga mabukatan da suka cancanci karban zakkan.

 

-7- Ana bada zakkan fidda-kai ne ga fakirai da miskinai, fakiri shi ne mabukaci da bai mallaki abincin shekara ba, shi kuwa  miskini shi ne mabukacin da yafi fakiri bukata.

 

Mabukacin da za a bashi zakkan fidda-kai ya kasance mumini kuma ya halatta a bai wa mutum daya sa'i da dama har zuwa abin da zai ishe shi na shekara shi da iyalansa.

 

Mustahabi ne mutum ya bada zakkan fidda-kai ga mabukata da suke makusantansa da makobtansa.

 

Haka nan ihtiyadi ne wajibi mutum ya nisanci bada zakkan fidda-kai ga mashayin giya ko mai bayyana manyan laifuka da yake aikatawa. Kamar yadda yake haramun ne mutum ya bada zakkan fidda-kai ga mubukacin da zai yi amfani da zakkan wajen aikata ayyukan sabon Allah.

Add comment


Security code
Refresh