An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 22 June 2015 18:43

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {14}

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {14}
I'itikafi Wato Zama A Cikin Masallaci Domin Bautan Allah.

Ma'anar I'itikafi shi ne: Zama a cikin masallaci da nufin bautan Allah Madaukaki. Kuma yana da kyau ga Mai I'itikafi ya kara da niyyar aikata ibada kamar sallah, addu'a, karatun alkur'ani da sauransu.

 

Matsayin I'itikafi a shari'a mustahabi ne amma ya kan iya zama wajibi idan mutum ya wajabta wa kansa yin I'itikafin ta hanyar yin bakance wato "Nazar" ko alkawari wato "Ahad" ko kuma rantsuwa wato "Yamin" da makamantansu.

 

Ana yin I'itikafi ne a duk lokacin da ya inganta a yi azumi wato duk lokacin da yin azumi ya halatta ga mutum, to yin I'itikafi ma ya halatta gareshi. Domin ba a yin I'itikafi sai tare da azumi ba ko da kuwa azumin na mustahabi ne wato azumin neman lada. Amma lokacin yin I'itikafi mafi daukaka shi ne watan ramalana mai alfarma kuma a kwanakin goman karshen watan.

 

Sharuddan Yin I'itikafi.

 

I'itikafi baya inganta har sai an cika wasu sharudda kamar haka:-

 

{1} Hankali:- I'itikafi baya inganta a kan mahaukaci. Haka nan mutumin dake cikin maye da makamantansu.

 

{2} Daura niyya:- I'itikafi baya inganta sai da niyya wato daura niyyar yin I'itikafi domin neman kusanci a wajen Allah Madaukaki kamar sauran ayyukan ibadu, tare da tabbata a kan niyyar wato kada mutum ya kudurta niyyar dauke hannu daga I’itikafin da yake yi.

 

Ana daura niyyar yin I'itikafi ne a daidai lokacin da za a fara gudanar da I'itikafin a farkon dare ko tsakiyansa ko kuma karshensa. I'itikafi yana farawa ne daga lokacin fitowan alfijir a ranar farko wato mutum ba zai jinkirta daura niyyar fara I'itikafi ba har zuwa bayan fitowan alfijir.

{3} Azumi:- I'itikafi baya inganta ga mutumin da baya azumi wato mutumin da yin azumi bai inganta gare shi, to yin I'itikafi ma bai inganta gareshi ba. Misali macen da ba ta azumi saboda jinin haila yin I'itikafi bai inganta ba a gareta.

 

Babu bambanci ya kasance azumin da mai i'itikafin yake yi na wajibi ne ko na mustahabi, kuma azumin da yake yi, wa kansa ne ko kuma yana azumin ne ga wani mutum na daban misalin azumin ramako ga mamaci.

 

{4} Adadin Kwanakin I'itikafi:- Wato kada kwanakin da Mai I'itikafi zai yi a cikin masallaci ya kasa wuni uku da dare biyu a tsakani, amma ya halatta Mai I'itikafi ya shige kwanaki uku a I'itikafin da yake yi. Abin da ake nufi da wuni shi ne daga fitowan alfijir zuwa faduwar rana.

 

{5} I'itikafin da mutum zai yi ya kasance a cikin babban masallacin garin da ake gudanar da sallolin jam’i misalin Masallacin juma'a:- Wato ba a yin I'itikafi a cikin kananan masallatai  da suke unguwanni. Sannan a bisa ihtiyadi mustahabi I'itikafin da mutum zai yi ya kasance a daya daga cikin masallatai hudu kamar:-

 

-1- Masallacin Ka'abah. -2- Masallacin Manzon Allah Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w} dake birnin Madinah. -3- Masallacin birnin Kufah  - 4 – Masallacin birnin Basrah.

 

{6} Rashin Fita Daga Cikin Masallaci:- Mai I'itikafi baya fita daga cikin masallacin da yake gudanar da I'itikafi a cikinsa, sai a bisa lalura na hankali ko shari'a ko kuma al'ada. Misalin fita daga masallaci domin zuwa yin wankan janaba ko kama ruwa ko kuma gaida maras lafiya. Idan kuma Mai I'itikafi ya fita daga cikin masallaci ba a kan wata lalura ba da gangan, to I'itikafinsa ya baci.

Abubuwan Da Suke Haramun Ne Ga Mai I'itikafi Ya Aikatasu.

 

Wajibi ne a kan Mai I'itikafi tun daga lokacin fara I'itikafinsa har zuwa lokacin fitansa ya nisanci aikata wasu abubuwa kamar haka:-

 

-1- Saduwa da mace ko sumbantarta ko kuma shafar jikinta domin sha'awa. Ita ma mace Mai I'itikafi dukkan wadannan ayyuka sun haramta gareta.

 

-2- Fitar da maniyi ta hanyar wasa da al'aura ko kallon mace ko kuma aikata duk wani abin da zai yi sanadiyyan fitar maniyi daga Mai I'itikafi da gangan.

 

-3- Shekar turare mai kamshi.

 

-4- Shekar duk wata itace mai kamshi ko fulawa domin jin dadi.

 

-5- Saye da sayarwa da duk wani nau'in kasuwanci.

 

-6- Musu da jayayya a kan al'amarin duniya ko addini, idan sun kasance domin gwada isa da neman daukaka ne, amma babu laifi idan sun kasance domin fayyace gaskiya ce da nuna hanya madaidaiciya.

 

Hukunce-hukuncen I’itikafi.

 

Idan mutum ya fara gudanar da I’itikafi ya halatta yayi watsi da I’itikafin wato ya fasa ci gaba da gudanar da I’itikafin, ya fice daga cikin masallacin, sai dai a wajaje kamar haka:-

 

-1- Idan mutum yayi bakancen gudanar da I’itikafi a kwanaki kebantattu, to matukar ya fara gudanar da I’itikafin a cikin wadannan kwanakin da ya kebance, wajibi ne ya ci gaba da I’itikafin, ba zai fasa ba saboda bakancen da yayi.

 

-2- Idan mutum ya fara gudanar da I’itikafi koda na mustahabi ne matukar ya riga yayi kwanaki biyu a cikin I’itikafin, to dole ne ya ci gaba da gudanar da I’itikafin ya cika kwana ta uku. Sai dai idan tun da fari ya gindaya sharadi a cikin niyyarsa cewa zai fasa ci gaba da gudanar da I’itikafin duk lokacin da yaga dama ko idan wani abu ya faru, to anan ya halatta ya fice daga I’itikafin a kan sharadin da ya gindaya koda kuwa a rana ta uku ce.

 

Idan mutum ya shiga I’itikafi na mustahabi, bayan kwanaki biyu sai I’itikafinsa ya baci saboda aukuwar wani abin dake bata I’itikafi, to wajibi ne ya sake gudanar da I’itikafin, amma ba dole ba ne sai ya hanzarta sake gudanar da I’itikafin. Sai dai idan I’itikafin ya baci ne sakamakon kasancewar cikan rana ta uku, ranar sallar idi ce, ko ya bayyana masa cewa wajen da yake gudanar da I’itikafin ba masallaci ba ne, to anan babu maganar sake gudanar da I’itikafinsa a kansa.           

 

Dukkanin abubuwan da suka haramta ga Mai I'itikafi ya aikatasu  da rana sun haramta gareshi ya aikatasu a cikin dare, amma ban da cin abinci.

 

Dukkanin abubuwan da suke bata azumi suna bata I'itikafi. Kari kan haka jima'i cikin dare ga Mai I'itikafi yana bata I'itikafin da yake yi, haka nan jima'i yana bata I'itikafi koda bisa mantuwa ne Mai I'itikafi ya aikata.

 

Idan mai I'itikafi ya bata I'itikafinsa na wajibi ta hanyar jima'i da gangan yin kaffara ta hau kansa, kuma babu bambanci jima’in da rana ce koda dare ne. Amma babu kaffara a kan Mai I’itikafin da ya bata I’itikafinsa da hanyar aikata sauran abubuwan da suka haramta ga Mai I’itikafi ya aikatasu.   

 

Kaffarar I'itikafi daidai take da kaffarar karya azumin watan ramalana da gangan wato yanta kuyanga ko ciyar da mabukata guda sittin ko kuma yin azumin watanni biyu a jere. Kuma ihtiyadi ne kaffarar ta kasance tamkar kaffarar Zihari wato ya jeranta kaffarar, farko ya dauki matakin yanta kuyanga, idan ba zai iya ba sannan yayi azumin watanni biyu a jere, idan ba zai iya ba sannan ya dauki matakin ciyar da mabukata guda sittin.    

 

Idan mutum ya bata I'itikafinsa na wajibi da rana a watan ramalana ta hanyar saduwa da mace, kaffara guda biyu sun hau kansa, kaffara daya ta azumin watan ramalana, kaffara ta biyu ta I'itikafi.

 

Mai I'itikafin da ya bata I'itikafinsa na wajibi a watan ramalana ta hanyar saduwa da matarsa da take azumi da rana da karfin tsiya, kaffara uku sun hau kansa, kaffara ta farko na azuminsa, kaffara ta biyu na I'itikafinsa, kaffara ta uku na saduwa da yayi da matarsa da take azumi.              

 

Add comment


Security code
Refresh