An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 22 June 2015 18:40

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {13}

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {13}
Mutanen Da Aka Musu Rangwamen Barin Yin Azumi Da Irin Hukunce-Hukuncen Da Suka Hau Kansu.

 

 

{1} Tsoho da tsohuwa da mai ciwon kishin ruwa da yin azumin watan ramalana zai zame musu wahala da tsanani, wato zasu iya yin azumin amma cikin wahala, to shari’a ta halatta musu barin yin azumin watan ramalana, amma wajibi ne a kansu su ba da mudu daya na hatsi ga mabukaci maimakon azumin kowace ranar da ba su yi ba, kuma babu ramakon azumin da ba su yi ba a kansu bayan watan ramalana.

 

Amma idan ya zame tsoho da tsohuwa da mai ciwon kishin ruwa ba zasu iya yin azumin watan ramalana ba ne kwata-kwata ko kuma yin azumin zai cutar da lafiyarsu, to wajibi ne su bar yin azumin kuma babu ciyarwa a kansu, haka nan babu ramakon azumin a kansu bayan watan ramalana.

 

{2} Mace mai ciki da ta yi kusan haihuwa da yin azumin watan ramalana zai cutar da dan dake cikinta, hukuncin da ya hau kanta shi ne ba zata yi azumin ba, amma duk ranar da ta sha ruwa zata ba wa mabukaci mudu daya na hatsi kaffarar rashin yin azumin sannan bayan watan ramalana ta yi ramakon azumin da ba ta yi ba.

 

Idan kuma yin azumin watan na ramalana zai cutar da lafiyarta ce, to anan hukuncinta ba zata yi azumin ba kuma babu kaffarar fitar da mudun hatsi a kanta, sai dai bayan watan ramalana zata yi ramakon azumin da ba ta yi ba. 

 

{3} Mace mai shayarwa da take da karancin nono wanda idan ta yi azumin watan ramalana zata cutar da danta. to hukuncin da ya hau kanta shi ne ba zata yi azumin ba, amma duk ranar da ta sha ruwa zata ba da mudu daya na hatsi ga mabukaci kaffarar rashin yin azumin, sannan bayan watan ramalana ta yi ramakon azumin da ba ta yi ba.

 

 

Idan kuma yin azumin na ramalana zai cutar da ita ce, to anan hukuncinta ba zata yi azumin ba kuma babu kaffarar fitar da mudun hatsi a kanta, amma bayan watan ramalana lokacin da laluranta ta kawu wajibi ne ta yi ramakon azumin da ba ta yi ba. 

 

Amma idan zai yiyu mace mai shayarwa ta shayar da danta da madara ko nonon da aka tatso daga dabba matukar hakan ba zai cutar da danta ba, ko kuma zata samu wata mace ta shayar mata da dan kyauta ko aka lada matukar zata iya biyan ladan, to bai halatta ta ki yin azumi ba a watan ramalana.

 

Kamar yadda ya halatta ga wadannan mutane su sha ruwa wato kada su yi azumin watan ramalana saboda rangwamen da aka yi musu, kuma ya halatta gare su su dauki matakin yin azumin matukar za su iya jure wahalarsa, amma bisa sharadin azumin ba zai cutar da lafiyarsu ba. Sai dai wannan ragwame bai hada da mace mai ciki da mai shayarwa da yin azumi zai cutar da ya’ya’yensu ba, domin wajibi ne garesu su dauki matakin kare 'ya'yan na su daga cutuwa kamar yadda yake wajibi a kansu su kare kansu daga cutuwa.        

 

Mace mai ciki da ta yi kusan haihuwa da mace mai shayarwa da take da karancin nono, idan suka sha ruwa a watan ramalana saboda yin azumin zai cutar da dansu, to matukar suka yi sakacin yin ramakon azumin watan ramalana dake kansu har shekara ta zagayo, wani sabon watan ramalana ya kama, to  wajabcin fitar da kaffarar hatsi biyu ne ya hau kansu. Daya na shan ruwan azumin watan ramalana. Na biyu saboda jinkirin yin ramakon azumin ramalana har wata ramalanar ta riskesu.

     

{4} Mutumin da bai yi azumin watan ramalana ba saboda rashin lafiya da yake fama da shi, bai kuma warke ba har shekara ta zagayo, wato wani watan ramalana ya riskeshi yana cikin halin rashin lafiya, to hukuncin da ya hau kansa shi ne: Ramakon azumin shekarar data gabata da bai yi ba saboda rashin lafiya ya fadi a kansa, wato babu ramakon azumin shekarar data gabata a kansa, sai dai wajibi ne ya bai wa mabukaci mudu daya na abinci maimakon azumin kowace rana da bai yi azumi ba.

 

Abin da ake nufi da mudu daya na abinci da za a bai wa mabukaci a kowace rana; shi ne kashi uku cikin hudu na kilo guda.

 

Hukunce-hukuncen ciyar da mabukaci:

 

-1- Niyyar bai wa mabukaci abincin ta kasance domin neman kusanci ne a wajen Allah Madaukaki, wato niyyar ta zame babu riya a cikinta.

 

-2- Ba wa mabukaci hatsi, ba kimar hatsin ba, wato ba a bai wa mabukaci kudi a maimakon hatsin da za a ba shi.

 

-3- Ya halatta a bai wa mabukaci fiye da mudu guda na hatsin da za a fitar. Wato idan mutum yana da ciyarwa na kwanaki da dama a kansa misalin ciyarwar kwanani goma, to ya hallata ya bada mudu goman ga mabukaci daya, sabanin kaffarar ciyarwa na baci azumin watan ramalana, inda muka bayyana cewa matukar za a samu mabukata guda sittin, to bai halatta a bai wa mabukaci daya mudu fiye da guda ba.

 

-4- Ba a ciyar da mabukaci har ya koshi, maimakon ba shi mudun hatsi, sabanin kaffarar bacin azumin watan ramalana inda muka bayyana cewa kodai mutum ya bai wa mabukaci mudun hatsi ko kuma ya shirya liyafa ya ciyar da shi dafaffen abinci har ya koshi.       

 

Rabe-Raben Azumi.

 

Hukuncin yin azumi ya kasu gida hudu kamar haka:-

 

-1- Azumi na Wajibi. -2- Azumi na Mustahabi. -3- Azumin na Makruhi. -4- Azumi na Haramun.

 

-1- Azumin wajibi sune kamar haka: Azumin watan ramalana, Azumin Kaffara, Azumin Bakance wato Nazar, Azumin Rantsuwa wato Yamin, Azumin Alkawari wato Ahad, Azumin da yake maimakon hadaya a lokacin aikin hajji da Azumin ramakon watan ramalana.

 

A azumin watan ramalana wajibi ne mutum ya kame daga aikata duk wani abin dake bata azumi daga fitowar rana zuwa faduwarta. Bai kuma halatta mutum ya karya azuminsa ba matukar babu wani uzuri da zai tilasta masa shan ruwa.  

 

A azumin ramakon watan ramalana ya halatta mutum ya karya azumin kafin gotawar rana wato kafin shigan lokacin sallar azahar, amma bayan shigan lokacin sallar azahar, bai halatta mutum ya karya azumin ramakon ba.

 

A azumin kaffara bai halatta mutum ya karya azumin ba a lokacin da yake jera azumin watan daya da kwana daya kafin gotawar rana ko bayanta, amma bayan yin azumin wata daya da kwana daya, a sauran ranakun azumin kaffarar da ya halatta a rarrabasu, mutum zai iya karya azumin kafin lokacin gotawar rana, amma bayan gotawar rana bai halatta ba.

 

A azumin da mutum ya wajabta wa kansa ta hanyar bakance, rantsuwa, alkawari da makamantansu, idan mutum bai sanya takamammen lokacin yin azumin ba, to ya halatta ya karya azumin a duk lokacin da ya ga dama kafin gotawar rana ko bayan gotawarta, amma idan har ya sanya tsayayyen lokacin yin azumin, to bai halatta ya karya ba kafin gotawar rana ko bayan gotawarta.

 

-2- Azumin Mustahabi suna da yawa amma shahararru daga cikinsu sune azumin watannin Rajab da Sha’aban, azumin kwanaki uku a kowane wata, azumin ranar Ghadir, azumin ranar haihuwar Manzon Allah {s.a.w} da makamantansu. Dukkanin wadannan azumi ya halatta mutum ya karyasu a duk lokacin da ya ga dama, sai dai ban da azumin I’itikafi shi kam bai inganta mutum ya karya shi ba matukar yana son cika sharadin I’itikafi, domin ba a yin I’itikafi sai da azumi.

 

-3- Azumin Makaruhi wato azumin da yake abin ki ne mutum ya aikata; sune kamar haka:- Azumin da yaron da bai balaga ba zai yi ba tare da izinin mahaifinsa ba, da azumin da bako zai yi ba tare da izinin mai masaukinsa ba, haka nan azumi ranar da ake kokwanto shin ranar Arfah ce ko ranar sallar idi, da azumin ranar Arfah ga wanda yin azumin zai raunana shi da zai kai ga barin yin addu’a.

 

-4- Azumin Haramun sune; yin azumin ranar sallar Idi babba da karami wato sallar Idul-Fitir da na Adhha, azumin ranakun sha daya, sha biyu da sha uku ga watan Zul-Hajj ga mutumin da ya ke Minah, shin yana aikin hajji ne ko baya yi, azumin ranar kokwanto shin ranar talatin ga watan Sha’aban ne ko ranar farko ne ga watan ramalana a matsayin azumin watan ramalana, azumin bakance domin godiya ga Allah saboda aikata wani abu na sabon Allah, azumin dare da rana a hade wato mutum yayi niyyar azumi har da dare, azumin mace na mustahabi da zai tauyaye hakkin mijinta, mutumin da yin azumi zai cutar da lafiyarsa amma ya yi azumin.             

 

Add comment


Security code
Refresh