An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 22 June 2015 18:38

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {12}

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {12}
Hukunce- Hukuncen Ramakon Azumin Watan Ramalana.

Wajibi ne a kan mutum ya yi ramakon azumin watan ramalana da ya shige shi bai yi ba, shin azumin ya shige shi ne da gangan sakamakon tawaye wa Allah madaukakin sarki misalin mutumin da haka kawai babu wani uzuri yaki yin azumin watan ramalana bisa ganganci, haka nan musulmin da yayi ridda ya bar addinin musulunci sannan daga baya ya tuba ya dawo musulunci ko kuma rashin yin azumin ya samo asali ne daga wani uzuri dake halatta shan ruwa a cikin watan ramalana, misalin matafiyi da yake tafiyar da take wajabta shan ruwa ko maras lafiya da ya wajaba ya sha ruwa saboda ba zai iya yin azumin ba ko azumin ya shige shi ne sakamakon maye ko barci da makamantansu.

Wajibi ne a kan musulmin da yayi ridda ya bar addinin musulunci yayi ramakon azumin watan ramalana da suka shige shi bai yi ba a lokacin da yake kafirci. Kuma babu banbanci shin asalinsa musulmi ne ya kafirta ya bar addinin musulunci ko kuma asalinsa ba musulmi ba ne, musulunta yayi sai kuma ya sake kafirta, to dukkaninsu lokacin da suka tuba suka sake dawowa addinin musulunci wajibi ne su yi ramakon azumin watan ramalana da ba su yi a lokacin da suka bar musulunci.

 

Wajibi ne a kan macen da ba ta yi azumin watan ramalana ba saboda jinin haila ko biki da ya zo mata, ta yi ramakon azumin kwanakin  da ta sha ruwa bayan watan ramalana.

 

Wajibi ne a kan macen mai ciki da tayi kusan haihuwa da ba tayi azumin watan ramalana ba saboda yin azumin zai cutar da dan dake cikinta ko yin azumin zai cutar da lafiyarta, tayi ramakon azumin ranakun da ta sha ruwa bayan watan ramalana.

Haka nan mace mai shayarwa da take da karancin nono da yin azumi zai cutar da danta da take shayarwa ko yin azumin zai cutar da lafiyarta, ita ma wajibi ne ta yi ramakon azumin ranakun da ta sha ruwa bayan watan ramalana.

 

Wajibi ne a kan mutumin da ya karya azuminsa da gangan a cikin watan ramalana ta hanyar aikata daya daga cikin abubuwan da suke bata azumi da muka ambata a shirye shiryenmu na baya, yayi ramakon azumin da ya karya a bayan watan ramalana.

 

Haka nan mutumin da ya aikata abin dake bata azumi a bisa jahilci wato bai san abin da ya aikata yana bata azumi ba, matukar yana da daman sanin hukunce-hukuncen shari'a amma yaki tashi ya nemi sanin bisa sakaci, to shima zai yi ramakon azuminsa da ya baci bayan watan ramalana.

 

Har ila yau ramakon azumin watan ramalana wajibi ne a kan jahilin da ba shi da masaniyar yin azumin wajibi ne a kansa don haka bai yi azumin ba, misalin yaro ko yarinya a farkon shekarar balagarsu da ba su da masaniyar yin azumin watan ramalana wajibi ne a kansu don haka ba suyi azumin ba, to wajibi ne daga baya lokacin da suka fahimci wajabcin yin azumi suyi ramakon azumin watan ramalana da ba su yi ba, amma babu kaffara a kansu.

 

Haka nan yara ko yarinyar a farkon shekarar balagarsu da ba zasu iya jure yin azumin cikekken watan ramalana ba, to wajibi ne su yi azumin ranakun da zasu iya jure yin azumi, sannan sauran ranakun da ba zasu iya ba, wajibi ne su yi ramakonsu a bayan watan ramalana.  

 

A gefe guda kuma ramakon azumin watan ramalana ba wajibi ba ne a kan wasu mutane da ba suyi azumin ba, wadannan mutane sune kamar haka:-

 

{1} Mutumin da asalinsa ba musulmi ba ne kuma ya balaga a kafirci, to ba zai yi ramakon azumin watan ramalana da bai yi su ba a lokacin da yake kafiri.

 

{2} Mutumin da yake fama da cutar hauka na kin karawa, idan ya warke daga cutar haukar ya dawo cikin hankalinsa, ba zai yi ramakon azumin watan ramalana da suka shigeshi a lokacin da yake hauka ba.

 

Haka nan mutumin da yake fama da cutar hauka dake tafiya ta dawo idan haukar ta bijiro masa kafin daura niyyar yin azumin washe gari kuma har alfijir ya fito bai dawo cikin hankalinsa ba, to azumin wannan ranar ya fadi a kansa wato ba zai yi ramakon azumin wannan ranar bayan watan ramalana ba.

 

{3} Mutumin da ya suma kafin daura niyyar yin azumin washe gari kuma har alfijir ya fito bai farfado ba, azumin wannan ranar ya fadi a kansa wato babu ramakon azumin wannan ranar a kansa bayan watan ramalana.

 

{4} Tsoho da tsohuwa da mai ciwon kishin ruwa da ba zasu iya yin azumin watan ramalana ba kwata-kwata ko kuma yin azumin zai cutar da lafiyarsu, to wajibi ne su bar yin azumin kuma babu ramakon azumin da ba suyi ba a kansu bayan watan ramalana.

 

{5} Mutumin da bai yi azumin watan ramalana ba saboda rashin lafiya da yake fama da shi, bai kuma warke ba har shekara ta zagayo, wato wani watan ramalana ya riskeshi yana cikin halin rashin lafiya, to hukuncin da ya hau kansa shi ne: Ramakon azumin shekarar data gabata da bai yi ba saboda rashin lafiya ya fadi a kansa, wato babu ramakon azumin shekarar data gabata a kansa, sai dai wajibi ne ya bai wa mabukaci mudu daya na abinci maimakon azumin kowace rana da bai yi azumi ba.

Idan mutum bai yi azumin watan ramalana ba saboda wani uzuri da ba rashin lafiya ba misalin tafiye tafiye, sai kuma uzurin ya ci gaba har zuwa wani sabon watan ramalana, ko kuma rashin lafiya ne ya sanya mutum ya sha ruwa a watan ramalana amma bayan ya warke sai wani uzuri na daban dake hana yin azumi ya bijiro masa har zuwa kamawar wani sabon watan ramalana, to anan wajibi ne yayi ramakon azumin watan ramalana da suke kansa na shekarar data gabata. Amma shin akwai ciyarwa a kansa saboda jinkirin ramakon azumin har zuwa kamawar wani sabon watan ramalana na daban ko babu? Anan akwai maaganganun malamai kamar haka:-

 

-1- Wasu malamai sun bayyana cewa babu ciyarwa a kansa, ramakon azumi kawai zai yi.

 

-2- Wasu malamai sun bayyana cewa bayan ramakon azumi da yake kansa wajibi ne sai ya kara da ciyarwa.

 

Ba wajibi ba ne mutum ya hanzarta yin ramakon azumin watan ramalana dake kansa, amma bai dace ya jinkirta yin ramakon ba har azumin watan ramalanan wata shekara ta riskeshi. Idan kuma yayi sakaci bai yi ramakon ba har azumin watan ramalanan wata shekara ta riskeshi, to wajibi ne yin ramakon tare da ciyar da mabukaci mudu daya na hatsi, misali idan mutum yana da ramakon azumin kwanaki biyar a kansa bai yi ba har azumin watan ramalanan wata shekara ya zagayo, to bayan ramakon azumin kwanaki biyar da zai yi wajibi ne kuma ya kara da bada mudu biyar na hatsi ga mabukaci saboda jinkirin da yayi har wani watan ramalana ya riskeshi.

 

Idan kuma mutum yayi sakaci bai yi ramakon azumin watan ramalana dake kansa ba har wata shekara ta zagayo, to ko shekara nawa ya kara a kai bai yi ramakon ba, ciyarwa daya ce a kansa misali idan mutum yana da ramakon azumin kwanaki uku a kansa bai yi ramakon ba har tsawon shekaru da dama, to ramakon azumin kwanaki ukun da suke kansa da ciyar da mabukata uku kawai  zai yi wato ciyarwar ba ta rubanya a kansa ba saboda karin shekaru da yayi bai yi ramakon ba.

 

Idan akwai ramakon azumin watan ramalanan shekaru biyu a kan mutum, to ya halatta gareshi ya fara ramakon duk azumin shekarar da ya ga dama, amma idan har lokaci ya kure sai ya fara yin ramakon azumin watan ramalanan da ya hau kansa a karshe domin gujewa kirin kaffarar ciyarwa.

 

Idan mutum bai yi azumin watan ramalana ba saboda rashin lafiya sai ya mutum kafin ya warke daga rashin lafiyar, to babu ramakon azumin da bai yi ba a kansa. Haka nan macen da ba ta azumi saboda jinin haila ko biki sai ta mutu kafin ta yi tsarki, itama babu ramakon azumin da ba ta yi ba a kanta.

 

Bai halatta ba ga mutumin da yake da ramakon azumin watan ramalana yayi azumin mustahabi.

 

Amma idan mutum yana da azumi na wajibi fiye da daya a kansa misalin azumin ramakon watan ramalana, azumin bakance, azumin kaffara da makamantansu, to ya halatta ya fara gabatar da duk azumin da ya ga dama.      

Add comment


Security code
Refresh