An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 22 June 2015 18:32

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {10}

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {10}
Bayani Kan Yadda Ake Yin Kaffarar Karya Azumin Watan Ramalana.

 

Yin kaffara yana wajaba ne a kan duk mai azumin da yake da masaniyar aikata abubuwan da aka ambata suna bata azumi amma ya aikata da gangan bisa zabinsa da son ransa. Wato ba tilasta shi aka yi ba da karfin tsiya ko ta hanyar gargadin cutar da shi matukar bai aikata ba. Saboda mai azumin da aka tilasta shi da karfin tsiya ya aikata abin dake bata azumi, misali mai azumin da aka dura masa abinci da karfi, azuminsa bai baci ba. Amma mai azumin da aka tilasta shi ta hanyar tsorata shi kan ya aikata abin dake bata azumi, misalin wani azzalumi yayi gargadin cutar da shi idan bai ci abinci ba, to idan ya ci abincin azuminsa ya baci sai ya rike baki zuwa faduwar rana sannan bayan watan ramalana yayi ramakon azumin wannan ranar amma babu kaffara a kansa.

 

Idan mai azumi ya aikata abin dake bata azumi a bisa jahilci wato bai san abin da ya aikata yana bata azumi ba, to idan yana da daman sanin hukunce-hukuncen shari'a amma yaki tashi ya nemi sanin, to hukuncinsa zai yi ramakon azuminsa da ya baci, amma dangane da hukuncin kaffara akwai maganganun malamai kamar haka:-

 

{1} Wasu malaman sun bayyana cewa zai yi kaffara ne a bisa ihtiyadi wajibi.

 

{2} Wasu malaman sun bayyana cewa babu kaffara a kansa.

 

Amma idan mai azumi ya aikata abin dake bata azumi ne a bisa jahilci, to idan jahilcinsa ya samo asali ne daga rashin yiyuwan sanin hukunce- hukuncen shari'a kuma bai ma hankalta a kan rashin sanin nashi ba, wato bai san ma shi jahili ba ne ballantana yayi tambaya ko kuma yana da tabbacin abin da ya aikata baya bata azumi, to a irin wannan yana yi ba zai yi kaffara ba.

Yadda ake kaffarar azumin watan ramalana shi ne:- Mutum zai zabi daya ne daga cikin wadannan abubuwa guda uku ya aikata:-

 

-1- Yanta bawa ko baiwa wato kuyanga.

 

-2- Azumin watanni biyu a jere.

 

-3- Ciyar da mabukata sittin.

 

Kasancewar a wannan zamani babu maganar bauta ballantana a samu bayin da za a yantar, to ya rage abu biyu ke nan, wato azumin watanni biyu a jere ko bada mudu daya na hatsi ga mabukata guda sittin ko kuma ciyar da su abinci har su koshi.

 

Yadda ake ciyar da mabukata guda sittin shi ne: Ciyar da su abinci har su koshi ko kuma bawa kowani mabukaci daga cikinsu mudu daya na hatsi, misalin alkama ko shinkafa ko dawa ko gero da makamantansu wato abincin da aka fi amfani da shi a wajen da mutum yake rayuwa.

 

Abin da ake nufi da mudu daya na hatsi shi ne: Kashi uku cikin hudu na kilo guda, misali idan aka auna kilo guda na shinkafa sai a rabashi gida hudu, to kashi uku shi ne ake nufi da mudu daya da za a bai wa kowane mabukaci.

 

Ba a bai wa mabukaci fiye da mudu daya na hatsin kaffarar watan azumin ramalana ko ciyar da shi sau biyu, matukar za a samu adadin mabukata guda sittin da ake bukata a ciyar da su kamar yadda shari’a ta wajabta. Amma ya halatta a bai wa mabukaci magidanci abincin kaffara daidai da yawan iyalan gidansa, ko da iyalan sun hada da manya da kananan yara ne. Misali idan yawan iyalansa sun kai bakwai tare da shi, to sai a ba shi mudu bakwai.

Mutanen da ake ciyar da su a kaffarar azumin watan ramalana sune Fakiri da Miskini. Abin da ake nufi da fakiri shi ne mutumin da yake mabukaci da bai mallaki abincin shekara ba, wato ba shi da abincin shekara a ajiye ko kuma abin da yake samu ta hanyar sana’arsa ko albashin da yake karba baya isarsa a shekara. Miskini kuma shi ne wanda yafi fakiri bukata wato gwamma fikiri da shi.

 

Mabukacin da za a ba shi kaffarar azumin watan ramalana ya kasance mumini, kuma kada ya zame daga cikin mutanen da wajibi ne ciyar da su a kan mutumin da kaffarar ciyarwar ta hau kansa, misalin mahaifinsa ko mahaifiyarsa ko kuma da ne gare shi.   

 

Yadda ake yin azumin watanni biyu a jere shi ne:- Kodai mutum yayi azumin watanni biyu a jere ko kuma yayi azumin wata daya da azumin kwana daya a wata na biyu a jere, misali azumi kwanaki talatin da daya ke nan ko kuma talatin idan watan farko kwanaki ashirin da tara yayi, sannan sauran azumin kwanakin wata na biyun, ya halatta mutum ya rarrabasu wato yayi azumi ya huta sannan ya ci gaba da yin azumin sannan ya huta, da haka har ya kare azumin.

 

Amma idan mutum bai jera azumin wata daya da kwana daya ba da gangan, to wajibi ne ya sake azumin tun daga farko, wato azumin da yayi dukkaninsu sun baci, misali idan yayi azumin kwanaki ashirin a jere sai yaki yin azumin rana ta shirin da daya da gangan, to dukkan azumin da yayi a baya na kwanaki ashirin sun rushe, sun zame kamar bai yi ba, sai ya sake wani azumin daga farko.

 

Amma idan rashin jero azumin ya samo asali ne daga wata larura misalin rashin lafiya ko jinin haila ko kuma tafiya ta bijiro masa da ake mata kasaru wadda ya zame dole ya sha ruwa, to a nan duk lokacin da uzurinsa ya kawu zai ci gaba da gudanar da azuminsa ne daga yadda ya tsaya a baya kafin uzuri ya bijiro masa.

Misali idan mutum yayi azumin kwanaki goma a jere, sai rashin lafiya ya kamashi dake wajabta shan ruwa, don haka ya dakatar da azumin kaffarar da yake yi, to bayan mutum ya warke daga rashin lafiyar, sai ya ci gaba da azumin kaffarar daga yadda ya tsaya kafin bijirowar rashin lafiya wato sai yayi azumin rana ta goma sha daya.

 

Idan kuma mutum yana da masaniyar akwai kaffara a kansa amma yana kokwanton shin yayi kaffarar ko bai yi ba? to a nan hukuncinsa wajibi ne yayi kaffarar.

 

Idan mutum bai san yawan ranakun da ya sha azumi ba da gangan, to hukuncinsa zai yi kaffara na adadin ranakun da yake da yakinin ya sha ruwa a cikinsu ne, amma dangane da ranakun da yake kokwanto, ba wajibi ba ne sai yayi musu kaffara. Misali idan mutum yana da masaniyar ya sha azumi na kwanaki amma yana kokwanto shin na kwanaki goma ne ko kuma na kwanaki goma sha biyar ne? a nan yana da tabbaci da yakinin kwanaki goma, kari a kan haka kuma yana kokwanto, to kaffarar kwanaki goma ne suke wajibi a kansa.

 

Ba wajibi ba ne mutum ya hanzarta yin kaffarar da ta hau kansa wato mutum zai iya jinkirta yin kaffarar zuwa shekaru amma kada jinkirin ya zame ya wuce iyaka da za a iya cewa ya zame sakaci.

 

Ya halatta mutum ya sauke wa mamaci hakkin kaffarar dake kansa ta hanyar biya masa azumi ko ciyarwa. Amma ga rayayye sai dai ciyarwa banda azumi, wato mutum ba zai yi azumin kaffara dake kan rayayye ba.

 

Mutumin da kaffarar azumin watan ramalana ta hau kansa amma baya da halin yanta bawa ko kuyanga kuma ba zai iya yin azumin watanni biyu ba kuma baya da halin ciyar da mabukata guda sittin, to sai yayi zabi tsakanin yin azumin kwanaki goma sha takwas da yin sadaka da abin da zai iya, amma an fi son yayi sadaka.

Idan kuma ba shi da abin da zai yi sadakar kuma ba zai iya yin azumin kwanaki goma sha takwas ba, to sai ya yayi istigfari wato ya nemi gafaran Allah Madaukaki ko da sau daya ne ya isar, a maimakon kaffarar, idan kuma daga baya ya samu daman yin kaffarar, to ba dole ba ne a kansa amma bisa ihtiyadi mustahabi mutum ya sake yin kaffarar.

 

   

Add comment


Security code
Refresh