An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 22 June 2015 18:29

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {9}

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {9}
Abubuwan Da Suke Wajabta Yin Ramako Tare Da Kaffara:-

 

 

{1} Idan mai azumi ya karya azuminsa ta hanyar ci ko sha da gangan a cikin watan ramalana, to ramakon azumin wannan ranar ya wajaba a kansa tare da yin kaffara.

 

{2} Idan mai azumi ya karya azuminsa ta hanyar saduwa da mace ko dabba ko kuma ta hanyar yin luwadi da gangan a cikin watan ramalana, to azuminsa ya baci, kuma wajibi ne yayi ramakon azumin wannan ranar tare da yin kaffara.

 

{3}  Idan mai azumi ya karya azuminsa ta hanyar fitar da maniyi da gangan sakamakon wasa da al'auransa ko shafan jikin mace ko aikata duk wani abin da ke tayar da sha'awa da ya kai ga fitar da maniyi a cikin watan ramalana, to azuminsa ya baci kuma wajibi ne a kansa yayi ramakon azumin wannan ranar tare da yin kaffara.

 

{4} Idan mutum ya wayi gari da janaba da gangan a cikin watan ramalana, to azuminsa ya baci kuma wajibi ne a kansa yayi ramakon azumin wannan ranar tare da yin kaffara.

 

{5} Kirkirar karya da jinginata ga Allah madaukaki ko Manzon Allah {s.a.w} ko kuma Jagororin shiriya na Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka {a.s} da gangan yana bata azumi a wajen wasu malamai, don haka a bisa fatawarsu wanda ya aikata hakan wajibi ne yayi ramakon azumin wannan ranar bayan watan ramalana.

 

Amma shin kirkirar karya da jinginata ga Allah ko Manzon Allah ko Jagororin shiriya na Iyalan gidan Manzo tsarkaka {a.s} yana wajabta yin kaffara ko baya wajabtawa? Akwai maganganun malamai kamar haka:-

 

-1- Wasu malaman sun bayyana cewa yana wajabta yin kaffara a bisa fatawarsu.

 

-2- Wasu malaman sun bayyana cewa yana wajabta yin kaffara ne a bisa ihtiyadi wajibi.

 

-3- Wasu malaman sun bayyana cewa baya wajabta yin kaffara.

 

{6} Idan mai azumi ya karya azuminsa ta hanyar yin gugutu da abu mai ruwa-ruwa ta dubura, to wajibi ne yayi ramakon azumin wannan ranar bayan watan ramalana.

 

Amma shin yana wajabta yin kaffara ko baya wajabtawa? Akwai maganganun malamai kamar haka:-

 

-1- Wasu malamai sun bayyana cewa yin gugutu da abu mai ruwa-ruwa ta dubura da gangan yana wajabta yin kaffara ne a bisa ihtiyadi wajibi.

 

-2- Wasu malaman sun bayyana cewa yin gugutu da abu mai ruwa-ruwa ta dubura da gangan baya wajabta yin kaffara.

 

{7} Nutsar da kai a cikin ruwa da gangan yana bata azumi a wajen wasu malamai, don haka a bisa fatawarsu yana wajabta yin ramako a bayan watan ramalana.

 

Amma shin yana wajabta yin kaffara ko baya wajabtawa? Akwai maganganun malamai  kamar haka:-

 

-1- Wasu malamai sun bayyana cewa yana wajabta yin kaffara a bisa ihtiyadi wajibi.

 

-2- Wasu malamai sun bayyana cewa baya wajabta yin kaffara.

 

{8} Kakaro amai da gangan yana bata azumi, don haka yana wajabta yin ramako.

 

Amma Shin yana wajabta yin kaffara ko baya wajabtawa? Akwai maganganu biyu kamar haka:- 

 

-1- Wasu malamai sun bayyana cewa yana wajabta yin kaffara a bisa ihtiyadi wajibi.

 

-2- Wasu malamai sun bayyana cewa baya wajabta yin kaffara.

 

{9} Shigar da kura mai kauri cikin makogwaro da gangan yana bata azumi a wajen wasu malamai, don haka a bisa fatawarsu yana wajabta yin ramakon azumi.

 

Shin yana wajabta yin kaffara ko baya wajabtawa? Akwai maganganun malamai kamar haka:-

 

-1- Wasu malaman sun bayyana cewa yana wajabta yin kaffara a bisa fatawarsu.

 

-2- Wasu malaman sun bayyana cewa yana wajabta yin kaffara a bisa ihtiyadi wajibi.

 

-3- Wasu malamai sun bayyana cewa baya wajabta yin kaffara.

 

Mai azumin da ya karya azuminsa da gangan a watan ramalana sai ya tsiri yin tafiya da take wajabta shan ruwa kafin gotawar rana domin gujewa yin kaffara, to kaffarar bata fadi a kansa ba, wato wajibi ne sai yayi ramakon azumin wannan ranar tare da yin kaffarar da ta hau kansa sakamakon karya azumin da yayi bisa ganganci.

 

Haka nan idan mai azumi ya karya azumin watan ramalana da gangan sai kuma tafiya da take wajabta shan ruwa ta bijiro masa ba da nufi ba kafin gotawar rana, shi ma wajabcin yin kaffarar da ta hau kansa sakamakon karya azumin da yayi da gangan bata fadi a kansa ba.

 

Mai azumin da ya karya azuminsa bisa ganganci sai wani uzuri da yake hana yin azumi ya bijiro masa misalin rashin lafiya dake wajabta shan ruwa ko jinin haila ko biki ya zo wa macen data karya azuminta da gangan, to anan malamai sun bayyana cewa kaffarar da ta hau kansu sakamakon karya azumi da gangan ta fadi.

 

Haka nan babu kaffara a kan mai azumin da ya karya azuminsa da gangan a ranar da ake kokwanto shin ranar talatin ne ga watan ramalana ko kuma ranar daya ce ga watan shawwal, sai kuma ya bayyana cewa ranar daya ce ga watan shawwal domin an tabbatar da ganin wata cikin dare.

 

Idan kaffara ta hau kan mutum sakamakon karya azuminsa da yayi da gangan a cikin watan ramalana, sai kuma ya sake aikata wannan nau'in abin dake bata azumin ko kuma wani nau'in dake bata azumi na daban, misali mutum ya karya azuminsa ta hanyar cin abinci da safe a watan ramalana, sai kuma ya kara cin abincin da rana, ko kuma bayan ya karya azuminsa ta hanyar cin abinci sannan yayi gugutu da abu mai ruwa-ruwa a wannan ranar, to malamai sun bayyana cewa kaffara daya ce ta hau kansa, amma idan ya karya azumin ne ta hanyar saduwa da mace sai kuma ya sake maimaita saduwa da macen a wannan ranar, to a bisa ihtiyadi mustahabi  yayi kaffara biyu.

 

Idan mai azumi ya sadu da matarsa da take azumi a cikin watan ramalana da karfin tsiya, to yin kaffara biyu ya kamashi, kaffara daya na karya azuminsa da yayi da gangan, kaffara ta biyu kuma na saduwar da yayi da matarsa da take azumi.

 

Har ila yau wasu malamai sun bayyana cewa za a masa bulala hamsin na ladabtarwa, ashirin da biyar na shi, sauran ashirin da biyar kuma na laifin tilastawa matarsa da yayi. Kuma babu bambanci matarsa ta auren da’imi ce  ko kuma ta auren mutu’a ce. Amma ita matar da aka sadu da ita da karfi babu komai a kanta kuma azuminta bai baci ba.

 

Amma idan da yardar mace mijinta ya sadu da ita alhalin dukkaninsu suna azumin watan ramalana, to azuminsu ya baci kuma wajibi ne su yi ramakon azumin wannan ranar tare da yin kaffara bayan watan ramalana, kuma kowane daga cikinsu za a yi masa bulala ashirin da biyar na ladabtarwa.

 

Idan kuma matar da mai azumi ya sadu da ita da karfi a cikin watan ramalana ba matarsa ba ce, to kaffara daya ce a kansa na karya azuminsa da yayi da gangan, ita kuma matar da aka mata fyade azuminta bai baci ba.

 

Idan kuma mace ce ta sadu da mijinta da karfin tsiya a cikin watan ramalana, a nan hukuncin yin kaffara daya ne a kanta wato kaffarar karya azuminta da ta yi bisa gangan.

 

Idan mutum baya azumi sakamakon rashin lafiya ko kuma matafiyi ne da ya dawo daga tafiya baya azumi a watan ramalana, to bai halatta ya sadu da matarsa da take azumi ba, idan kuma har ya sadu da ita da karfi, to a nan akwai maganganu biyu:- Wasu malamai sun bayyana cewa babu yin kaffara a kansa saboda saduwar da yayi da matarsa da take azumi duk da cewa ya aikata zunubi. Yayin da wasu malaman suka bayyana cewa wajibi ne yayi kaffara saboda saduwar da yayi da matarsa da take azumi a bisa ihtiyadi wajibi.

 

Idan mai azumi ya karya azuminsa a watan ramalana da hanyar aikata abin da yake haramun, misalin shan giya ko zina, to  kaffara daya ce ta hau kansa, wato yin azumin watanni biyu a jere ko ciyar da mabukata guda sittin.

 

Idan mutum ya bata azuminsa amma yana kokwanto shin abin da ya aikata yana wajabta ramako ne kawai ko kuma har da kaffara? to a nan hukuncin ramako ne kawai ya hau kansa banda kaffara.

Add comment


Security code
Refresh