An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 22 June 2015 18:26

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {8}

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {8}
A ci gaba da bayani da muke yi kan abubuwan da ya wajaba ga mai azumi ya nisancesu, a shirin mu da ya gabata mun yi takaitaccen bayani ne dangane da yadda wayan gari da janaba da gangan yake bata azumi a watan ramalana, sai lokaci yayi mana halinsa, don haka a yau zamu dora daga yadda muka tsaya kamar haka:-

 

{8} Kirkirar karya da jinginata ga Allah Madaukaki ko Manzon Allah Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w} yana bata azumi idan bisa ganganci ne. Haka nan hukuncin yin karya ga sauran Annabawa da Imamai goma sha biyu na iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka {a.s} shi ma yana bata azumi a bisa mashhuriyar magana. Shin hukunci na karya aka jingina a garesu ko kuma hadisi ne, a kan al'amarin duniya ne ko na lahira? babu bambanci, jingina karyar tana bata azumi.

 

Amma da ace mai azumi yayi niyyar fadar gaskiya ce sai kuma maganar da ya jingina garesu ta zame ba haka take ba, to a nan azuminsa bai baci ba. Haka nan nakalto labari ko hikayar karya daga wani mutum ko littafi baya bata azumi.

 

Idan mai azumi ya nakalto ingantacciyar magana daga Allah ko Manzonsa sannan ya karyata da gangan, to azuminsa ya baci. Haka nan idan mutum ya kirkiri karya a cikin dare sannan da rana a lokacin da yake azumi ya jingina ta ga Allah ko Manzonsa, shi ma azuminsa na wannan ranar ya baci.

      

A gefe guda kuma a wajen wasu malamai kirkirar karya da jinginata ga Allah Madaukaki ko Manzon Allah ko sauran Annabawa da Imamai {a.s} yana daga cikin manyan laifuka, sai dai baya bata azumi.    

 

{9} Mai azumin da ya bar kura mai kauri ta shige cikin makogwaronsa da gangan ko bisa sakaci, azuminsa ya baci a wajen wasu malamai.

 

Shin kurar da ta shige cikin makogwaron mai azumin, kura ce ta halal misalin kurar gari ko kuma kurar abin da yake haramun ne a ci, misalin kurar kasa da makamantansu. Shin mai azumin ne  yayi sanadiyyar tada kurar da kansa ta hanyar shara ko kuma iska ce ta tada kurar, matukar dai mai azumi yana da ikon kare shigar kurar cikin makogwaronsa amma yayi sakaci ya bar kurar ta shige, to azuminsa ya baci.

 

Amma mai azumin da ya bar kura maras kauri ta shige cikin makogwaronsa da gangan ko bisa sakaci, azuminsa bai baci ba. Sai dai idan kura maras kaurin ta taru ne a bakin mai azumi sannan ya hadiye da gangan, a irin wannan yana yi azuminsa ya baci.

 

Haka nan shigar tururi ko hayaki cikin makogwaron mai azumi baya bata azumi. Sai dai idan tururin ya zame ruwa a cikin bakin mai azumi sai ya hadiye da gangan, to a irin wannan yana yi azumin mutum ya baci.

 

Amma dangane da shigar kura mai kauri cikin makogwaro bisa mantuwa ko gafala ko rashin tsammanin shigar kurar ko kuma kurar ta shiga makogwaron mai azumi ne alatilas wato babu yadda mai azumi zai hana shigarta cikin makogwaronsa, to a irin wadannan halaye azuminsa bai baci ba.

 

A gefe guda kuma wasu malamai sun bayyana cewa ihtiyadi ne mustahabi mai azumi ya dauki matakin hana shigar kura mai kauri ko maras kauri cikin makogwaronsa da gangan, haka nan shigar tururi da hayaki cikin makogwaro, amma shigarsu cikin makogwaron mai azumi ko da a bisa sakaci ne, baya bata azumi. Wato shigar kura da tururi da hayaki cikin makogwaro ba su bata azumi a wajen wasu malamai.

 

Amma dangane da hukuncin shan taba sigari ga mai azumi akwai maganganu malamai kamar haka:-

 

{1} Wasu malamai sun bayyana cewa: Shan taba sigari ga mai azumi yana bata azumi bisa ihtiyadi wajibi.

 

{2} Wasu malamai sun bayyana cewa: Shan taba sigari haramun ne a shari’a, amma shanta baya bata azumi.

 

Dukkanin abubuwan da muka ambata cewa wajibi ne ga mai azumi ya nisancesu, suna bata azumi ne idan mutum ya aikatasu a kan ganganci kuma yana da masaniyar cewa aikatasu da gangan yana bata azumi.

 

Jahili da yake da daman neman ilimi amma ya ki tashi ya nemi sanin hukunce-hukuncen shari’a saboda sakaci, idan ya aikata abin da yake bata azumi misali yayi sanadiyyan fitan maniyyi da rana a watan ramalana da gangan bisa rashin sanin hakan yana bata azumi, to azuminsa ya baci.

 

Amma Jahilin da ba shi da daman neman ilimi kuma bai yi sakaci wajen neman sanin hukunce-hukuncen shari’a ba, idan ya aikata abin da yake bata azumi misali yayi gugutu da abu mai ruwa-ruwa da rana saboda bai san yana bata azumi ba, ko kuma yayi gugutun ne bisa tabbacin baya bata azumi, to wasu malamai sun bayyana cewa azuminsa bai baci ba, yayin da wasu malaman suka bayyana cewa azuminsa ya baci amma bisa ihtiyadi wajibi.

 

Idan mutum ya aikata abin da ke bata azumi bisa mantuwa ko rafkanuwa ko gafala, to azuminsa bai baci ba.

 

Amma mai azumin da ya aikata abin da yake bata azumi bisa mantuwa sai ya tsammaci cewa azuminsa ya baci, don haka ya ci gaba da aikata abin da yake bata azumin da gangan, to a nan hukuncinsa daya yake da wanda ya bata azuminsa da gangan wato azuminsa na wannan ranar ya baci.

 

Jahilin da kasance ba shi da masaniya dangane da wajabcin yin azumi a kansa, don haka bai yi azumi ba, to wajibi ne yayi ramakon azumin watan ramalana da suka shige shi, kuma babu bambanci shin jahilcinsa ya samo asali daga sakacin rashin neman ilimi ne ko kuma jahili ne da ba shi da daman sanin hukuncin da ya hau kansa na yin azumin watan ramalana misalin  ‘yan mata da suke saurin balaga.

 

{Fadakarwa a dukkanin wajajen da muka bayyana sabanin fatawowin malamai, wajibi ne a kan mutum ya koma zuwa ga mujtahidin da yake masa takalidi domin yin aiki da fatawarsa, domin a wannan shirin namu, muna kokarin bijiro da fatawowin da suka shafi hukunce-hukuncen azumin watan ramalana ne musamman muhimmai daga cikinsu da aka samu daidaito baki a tsakanin malamai, amma a wasu bigiren babu makawa sai mun bayyana hukuncin da suke da sabani a kai saboda muhimmancin hukunce -hukuncen}. 

       

Babu laifi mai azumi ya tauna abinci ga karamin yaro ko sanya abinci a baki domin tsuntsu ya dinga ci daga bakinsa ko dandana miya sannan ya tofar ko yin asuwaki da bushasshen itace ko         zama a cikin ruwa ga namiji amma ban da nutsar da kai.

 

Abubuwan da suke abin ki ne ga mai azumi ya aikatasu wato makaruhi.

 

Abin ki ne mai azumi ya aikata abubuwa kamar haka:-

 

-Wasa da mace ko shafarta ko sumbatarta ko aikata duk wani abin da zai ta da sha’awa, idan mai azumi yana da amincin hakan ba zai yi sanadiyyan fitar maniyi daga gareshi ba.

 

-Daukan jinin mai azumi da zai yi sanadiyyan raunana shi, amma babu matsala matukar daukan jinin ba zai raunanashi ba.

 

-Shakar duk wani itace mai kamshin. Amma ba a ki mai azumi ya sanya turare mai kamshi ba.

 

-Jika tufar da mai azumi ke sanye da ita.

 

-Mace mai azumi ta zauna a cikin ruwa.

 

-Yin gugutu da magani daskararre, wato sanya daskararren abu ta dubura misalin magani ga mai azumi.

 

-Yin kaho da zai janyo raunanan mai azumi.

 

-Mai azumi ya cire hakori da yake matauni ne a tsakanin hakwaransa ko janyo baki yayi jini, sai dai idan bisa lalura ne.

 

-Yin asuwaki da danyen itace ga mai azumi.

 

-Kurkuran baki domin wasa ga mai azumi.

 

-Sanya kwallin da yake dauke da itacen “sabar” mai tsananin daci ko miski da yake da kamshi wanda zai ji dandanonsa ko kamshinsa a magogwaronsa. 

 

-Rera waka ga mai azumi, sai dai a wajen bukukuwan Jagororin shiriya na iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka {a.s}.

  

 

Add comment


Security code
Refresh