An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 22 June 2015 18:23

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {7}

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {7}
A shirin mu da ya gabata mun fara bayani ne kan abubuwan da ya wajaba ga mai azumi ya nisancesu, inda muka ambaci wasu daga cikinsu sai lokaci yayi mana halinsa, don haka a yau zamu dora ne daga inda muka tsaya kamar haka:-

 

{7} Wayan-Gari da janaba da gangan a watan ramalana:- Idan mutum ya sadu da mace ko yayi mafarki da ya kai ga fitar maniyi a cikin dare, amma ya wayi gari da janaba bisa ganganci ko sakaci, azuminsa na wannan ranar ya baci.

 

Idan mutum ya yi janaba a fadake ta hanyar saduwa da mace ko fitar da maniyi a cikin dare, to ba zai kwanta domin yayi bacci ba kafin yayi wanka, sai dai idan ya kasance a dabi’arsa yana tashi kafin fitowan alfijir ko ya sanya na’urar dake tashin mutum daga bacci saboda ya tashi yayi wanka kafin fitowan alfijir.

 

Amma idan mutum yayi janaba cikin dare sannan ya kwanta bacci da niyyar ba zai tashi yayi wanka ba, kuma bai tashi ba har sai da alfijir ya fito, to yana daidai da wanda ya wayi gari da janaba da gangan, wato azuminsa na wannan ranar ya baci.

 

Idan mutum yayi janaba cikin dare, sannan ya kwanta bacci da niyyar zai tashi yayi wanka kafin fitowan alfijir, amma a dabi’arsa baya tashi daga bacci kafin fitowan alfijir kuma sai baccin ya zarce har bayan fitowan alfijir, to hukuncinsa a nan zai ci gaba da azuminsa bisa tsammanin ingancinsa sannan ihtiyadi wajibi yayi ramakon azumin wannan ranar.

 

Idan mutum yayi janaba cikin dare sannan ya kwanta bacci da niyyar zai tashi yayi wanka kafin fitowan alfijir kuma ya kasance a dabi’arsa ya kan tashi kafin fitowan alfijir ko ya sanya na’urar dake tashin mutum daga bacci domin ya tasheshi, amma sai baccin ya zarce har bayan fitowan alfijir, to anan azuminsa na wannan ranar ya inganta babu komai a kansa.

 

Idan mutum yayi janaba cikin dare sannan ya kwanta bacci saboda a dabi’arsa ya kasance yana tashi kafin fitowan alfijir, to idan ya farka daga wannan baccin wanda yake shi ne karo na farko bayan yayi janaba, to ihtiyadi kada ya sake komawa wani baccin na daban, sai dai idan yana da nutsuwar zai sake farkawa kafin alfijir, idan kuma ya koma baccin karo na biyu sai kuma barcin ya zarce har zuwa bayan fitowan alfijir, hukuncinsa anan sai ya rike baki har zuwa faduwar rana, sannan bayan watan ramalana yayi ramakon azumin wannan ranar, amma babu kaffara a kansa. Amma wasu malaman sun bayyana cewa hukuncin ramakon azumin wannan ranar zai hau kansa ne a lokacin da ya koma bacci karo na uku da nufin zai tashi yayi wanka sai kuma baccin ya zarce har zuwa bayan fitowan alfijir. 

 

Haka nan hukuncin yake ga wanda ya farka daga bacci karo na biyu ya koma karo na uku ko na hudu ko fiye da haka, matukar dai duk lokacin da ya farka yana da nutsuwar idan ya koma baccin zai tashi yayi wanka kafin fitowan alfijir.

 

Wannan hukunce hukuncen sun danganci mutumin da yayi janaba ne cikin dare a fadake ta hanyar saduwa da mace ko fitar maniyyi. Amma mutumin da yayi janaba ta hanyar yin mafarki ga yadda hukunce hukuncen da suka hau kansa suke kamar haka:-

 

Idan mutum yayi janaba ta hanyar mafarki a cikin barci, bai kuma farka ba sai bayan fitowan alfijir, azuminsa na wannan ranar ya inganta wato babu komai a kansa.

 

Amma idan mutum yayi janaba ta hanyar mafarki a cikin barci da dare sai ya farka daga barcin, to bisa ihtiyadi ba zai koma ya sake wani barci na daban ba kafin yayi wanka, sai dai idan yana da amincin zai sake tashi domin yayi wanka kafin fitowan alfijir, a kan haka idan ya koma barci karo na farko bayan  janabarsa sai kuma aka yi rashin dace baccin ya zarce har zuwa bayan fitowan alfijir, to hukuncinsa zai ci gaba da rike baki har zuwa faduwar rana sannan bayan watan ramalana yayi ramako.

Amma wasu malaman sun bayyana cewa azuminsa na wannan ranar ya inganta wato babu ramako a kansa. Sai dai idan ya sake komawa wani baccin na daban wato karo na biyu bayan janabarsa kuma baccin ya zarce har zuwa bayan fitowan alfijir, to wajibi ne yayi ramakon azumin wannan ranar bayan watan ramalana.

 

Idan kuma lokacin da mutum ya farka daga barcin da yayi janaba a ciki sai kuma ya koma ya sake kwanciya, kuma a bisa al’adarsa baya tashi kafin fitowan alfijir, sai kuma baccin ya zarce har zuwa bayan fitowan alfijir, to hukuncinsa zai ci gaba da rike baki har zuwa faduwar rana sannan bayan watan ramalana yayi ramakon azumin wannan ranar tare da kaffara.       

        

Idan mutum yayi janaba cikin dare kuma ya mance bai yi wanka ba har alfijir ya fito, to wajibi ne ya rike bakinsa har zuwa faduwar rana sannan bayan watan ramalana yayi ramako, amma babu kaffara a kansa. Wannan hukunce hukunce ne da suka shafi azumin watan ramalana kawai, ban da sauran nau’o’in azumi domin hukuncinsu ya sha banban.

 

Idan babu ishasshen lokacin yin wanka kafin alfijir ya fito a watan ramalana, to bai halatta mutum ya sadu da matarsa yayi janaba ba, idan kuma ya aikata hakan bisa mantuwa ko ganganci, to wajibi ne ya hanzarta yin taimama kafin fitowan alfijir kuma azuminsa na wannan ranar ya inganta. Sannan idan yayi taimamar, ba wajibi ba ne ya zauna har lokacin fitowan alfijir ba tare da yayi barci ba, domin ka da taimamar da yayi ta baci. Wato ya halatta bayan yayi taimamar maimakon wanka ya kwanta yayi barci har zuwa bayan fitowan alfijir.

 

Idan kuma mutum yayi janaba da gangan duk da cewa ya san babu ishasshen lokacin yin wanka kuma yayi sakaci bai yi taimama ba har alfijir ya fito, to azuminsa na wannan ranar ya baci, don haka wajibi ne ya rike baki har zuwa faduwar rana sannan bayan watan ramalana yayi ramakon azumin wannan ranar tare da kaffara.

Dangane da hukuncin jinin haila ko jinin biki kuwa:- Idan jinin hailan mace ko bikinta ya dauke a cikin dare a watan ramalana, amma taki yin wanka bisa ganganci ko sakaci har ta wayi gari, to anan akwai fatawowin malamai kamar haka:-

 

{1} Mafi yawan malamai sun bayyana cewa azuminta na wannan ranar ya baci kuma wajibi ne bayan watan ramalana ta yi ramakon azumin tare da yin kaffara.

 

{2} Wasu malaman sun bayyana cewa ne macen da jinin hailanta ko bikinta ya dauke cikin dare a watan ramalana, ba wajibi ba ne sai ta hanzarta yin wanka kafin fitowan alfijir, amma yin wankan abu ne mai kyau kuma ihtiyadi mustahabi, wato dai azuminta bai baci ba saboda ta wayi gari ba tayi wanka ba.

 

Don haka a irin wannan hali na sabanin malamai dole ne mutum ya tabbatar da ya kiyaye hukuncin da ya hau kansa daidai da fatawan mujtahidin da yake masa takalidi.

 

Sakamakon haka a bisa fatawan malaman da suke ganin wajibi ne macen da jinin hailanta ko bikinta ya dauke cikin dare a watan ramalana ta yi wanka kafin fitowan alfijir: Sun bayyana hukunce hukunce kamar haka:-

 

Idan mace jinin hailanta ko bikinta ya dauke cikin dare a watan ramalana amma ba ta san jinin ya dauke ba sai bayan da alfijir ya fito, to hukuncinta kawai sai ta daura niyyar azumin wannan ranar tayi azumi, kuma azuminta ya inganta. Haka nan idan mace tana da masaniyar jinin hailanta ko bikinta ya dauke a cikin dare amma ta mance ba ta yi wanka ba har alfijir ya fito, itama zata daura niyyar yin azumi ne kuma azumin ya inganta.

 

Dangane da jinin istihada kuwa:- Hukuncin mace mai jinin istihada kadan, daidai yake da hukuncin macen da take cikin halin tsarki, wato jininta bai shafi azuminta ba.

Amma macen da take jinin istihada matsakaici ko mai yawa, mashuriyar magana a wajen wasu malamai itace: Sharadi ne na ingancin azuminta ta yi wankan rana da ake yi domin sallah, wato idan jinin istihada da yake wajabta yin wanka ya zo mata kafin ta yi sallar asubahi ko azahar da la’asar sai kuma ta ki yin wankan, to azuminta na wannan ranar ya baci.

 

Amma da jinin istihadan ya zo mata ne bayan ta riga ta yi sallar azahar da la’asar sai ta ki yin wankan har rana ta fadi, to ingancin azuminta na wannan ranar ya dogara ne da yin wankan dare kafin fitowan alfijir.

 

A gefe guda kuma wasu malaman sun bayyana cewa ingancin azumin mace mai jinin istihada matsakaici da mai yawa ba shi da alaka da yin wankanta na rana ko na dare, sai dai ihtiyadi ne mustahabi yin wankan. Don haka a irin wannan yana yi sai mutum yayi aiki da fatawan mujtahidin da yake masa takalidi.

 

Idan wajabcin yin wanka ya hau kan mutum cikin dare sakamakon shafan jikin mamaci bayan jikinsa yayi sanyi kafin a yi masa wanka, to ba dole ba ne sai mutum yayi wankan kafin fitowan alfijir kuma babu abin da ya hada azuminsa da wankan da zai yi sakamakon shafan jikin mamaci.

 

A duk lokacin da wanka ya zame wajibi a kan mutum kafin fitowan alfijir, idan ba zai yiyu yayi wankan ba saboda wani uzuri misalin rashin ruwa ko maras lafiya da yake tsoron yin amfani da ruwa ko saboda kurewan lokaci da makamantan haka, to sai mutum ya gudanar da taimama maimakon wankan kafin fitowan alfijir domin azuminsa ya inganta.

 

Idan kuma wanka ya wajaba a kan mutum kafin fitowan alfijir sakamakon yin janaba ko macen da jinin hailanta ko bikinta ya dauke kuma babu ruwan yin wanka, haka nan babu kasar yin taimama, to anan wayan gari a watan ramalana ba tare da yin wankan ba, baya bata azumin wannan ranar.

Add comment


Security code
Refresh