An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 22 June 2015 18:20

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {6}

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {6}
Abubuwan da ya wajaba ga mai azumi ya nisance su.

 {1} Ci ko Sha:- Azumi yana baci idan mai azumi ya ci ko ya sha wani abu da aka saba ci ko sha a al'ada. Misalin Waina ko ruwa. Haka nan abin da ba a saba ci ko sha ba a al'ada, shi ma yana bata azumi, misalin cin laka ko kasa ko shan kananzir, kuma komai kashin abin da mai azumi ya ci ko ya sha, ko da misalin sauran dan abinci ne da ke makalewa a hakora, matukar ci ko shan da gangan ne, azumin ya baci.

Idan mai azumi ya shigar da abinci ko abin sha zuwa cikinsa ba ta hanyar makogwaro ba, matukar za a iya gaskata cewa ya ci ko ya sha, to azuminsa ya baci. Misalin shigar da abinci ko abin sha da roba zuwa ciki ta hanyar hanci, ko karin ruwa da ake yi a asibiti da ke zama madadin abinci a jikin mutum, dukkanin irin wadannan abubuwa suna bata azumi. Amma karin ruwa da ake yi domin hanzarta shigar da magani cikin jikin mutum da ba shi da alaka da ciyar da maras lafiya baya bata azumi.

Haka nan babu laifi ga mai azumi ya yi allura a wata gabar jikinsa ko jijiya ko sanya magani a ciwonsa ko sanya kwalli ko magani a idonsa ko kunnansa ko da kuwa ya ji dandanonsa a makogwaronsa. Amma sanya magani mai ruwa-ruwa a cikin hanci da zai kai ga makogwaro yana bata azumi, saboda za a iya kiransa da ci ko sha.

Har ila yau, babu laifi mai azumi ya hadiye yawun da ya taru a bakinsa komai yawansa ko hadiye majinar da ya sauko daga kai ko ya hawo daga kirji matukar bai zo bakin mai azumi ba.    

Idan mai azumi ya fuskanci matsalar kishin ruwa mai tsanani inda ya ji tsoron halaka, to ya halatta, kai wajibi ne ya sha ruwa gwargwadon bukata, amma azuminsa na wannan ranar ya baci, kuma wajibi ne ya ci gaba da rike baki har zuwa lokacin shan ruwa sannan bayan watan ramalana yayi ramakon azumin wannan ranar.                    

Idan mutum yana azumi sai ya mance ya ci ko ya sha wani abu da ke bata azumi, to azuminsa bai baci ba.

Mai azumin da aka kamashi da karfin tsiya aka dura masa abinci ko wani abin da ke bata azumi, to azuminsa bai baci ba. Shi kuwa mai azumin da aka tilasta masa aikata wani abin da ke bata azumi, misalin wani azzalumi ya yi gargadin kashe mai azumi ko cutar da shi matukar bai ci abinci ba, sai mai azumin ya aikata abin da ke bata azumin, wato ya ci abincin, to azuminsa na wannan ranar ya baci, sai ya rike baki sannan bayan watan ramalana ya yi ramako amma babu kaffara a kansa.

{2} Jima'i:- Yin jima'i wato saduwa da mace ta gaba ko ta dubura yana bata azumi. Macen da aka sadu da ita yarinya ce ko babba ce, rayayyiya ce ko matacciya ce babu bambanci. Mace dana mijin da suka sadu da juna dukkaninsu azuminsu ya baci.

Haka nan yin luwadi yana bata azumi, wanda yayi luwadin da wanda aka yi da shi, haka nan saduwa da dabba shi ma yana bata azumi.

Jima'i yana tabbata ne idan kan al'aurar namiji da ake kira hashafa ta shige cikin kafan mace ko duburanta. Ga mai yankekken al'aura kuwa jima'i yana tabbata ne da zarar kwatankwacin hashafa ta shige cikin kafa. Idan jima'i ya tabbata azumi ya baci ko da kuwa maniyi bai fito ba, matukar bisa ganganci ne.

Amma azumi baya baci idan mutum yana wasa ne sai al’aurarsa ta shige cikin kafa bada nufi ba, ko mutum ya mance yana azumi ya sadu da mace, amma idan ya tuna sai yayi nawa wajen ficewa, to azuminsa ya baci. Haka nan macen da aka mata fyade da karfi ita ma azuminta bai baci ba. Amma mutumin da aka tilasta masa ya sadu da mace ta hanyar gargadin cutar da shi misalin yi masa gargadin kisa, shi kan azuminsa ya baci, wajibi ne bayan watan ramalana yayi ramakon azumin wannan ranar amma babu kaffara a kansa. 

{3} Fitar da maniyi da gangan. Idan mai azumi ya san ba zai iya kare kansa daga fitan maniyi ba sakamakon wasa da al'aurarsa ko shafar jikin mace ko sumbatarta ko duban mace ko kuma aikata duk wani abin da zai yi sanadiyyan fitan maniyi, kuma yana tsammanin aikata irin wadannan abubuwan zai yi sanadiyyan fitan maniyi daga gare shi, to idan ya aikata kuma maniyin ya fito, azuminsa ya baci. Amma idan haka kawai babu wani sanadi maniyi ya fito wa mai azumi, to azuminsa bai baci ba.

Mai azumin da yake da masaniyar idan ya kwanta bacci da rana a watan ramalana zai yi mafarki da maniyi zai fito, to ya halatta ya kwanta baccin kuma idan maniyyin ya fito azuminsa bai baci ba.

Idan kuma mai azumi ya farka daga bacci ya ji maniyyi yayi kusan fitowa, to ba wajibi ba ne ya hana fitowansa musamman idan rashin fitowansa zai cutar da shi, kuma azuminsa bai baci ba. 

Idan mai azumi yayi mafarki da rana da maniyyi ya fito, to babu laifi bayan ya farka yayi fitsari domin sauran maniyyin da yayi saura a magudanarsa ya fita.

{4} Gugutu:- Yin gugutu yana bata azumi wato shigar da abu mai ruwa-ruwa misalin magani ta dubura kuma ko da yin gugutun domin magani ne, amma yin gugutu da abu daskararre baya bata azumi misalin sanya maganin basir mai kama da cafsol ta dubura.

Yin gugutu da abu mai ruwa-ruwa yana bata azumi ne matukar ya kasance ta dubura, amma yin gugutu ta al’aurar namiji ko ta gaban mace misalin sanya magani a cikin mahaifa ko sanya na’ura ko hannu da likitoci ke yi a cikin gaban mace domin bincike ko gwaji ko kuma saboda kare lafiyar mace ko na jaririn da ke cikinta, baya bata azumi.

Idan mai azumi yana da tabbacin abin da ya sanya a cikin duburarsa domin yin gugutu abu  ne da yake daskararre, sai kuma ya bayyana masa abu ne da yake mai ruwa-ruwa, to azuminsa bai baci ba.

{5} Kakaro amai da gangan yana bata azumi ko da kuwa bisa larura ce, misali warakar da mai azumi zai samu daga wata cuta ta dogara ce a kan amai da zai yi, yin aman ya halatta amma azuminsa ya baci. Amma idan aman ya zo ne wa mai azumi bada nufi ba, to a nan azuminsa bai baci ba.

Idan mai azumi ya yi gyatsa sai abinci ya hauro zuwa makogwaronsa ko zuwa bakinsa, abincin ya kuma koma ciki ba da son ran mai azumi ba ko bisa mantuwa, to azuminsa bai baci ba.

Amma idan lokacin da mai azumi yayi gyatsa, abinci ya zo  bakinsa yana da ikon tofar da shi, to wajibi ne ya tofar, idan kuma ya sake hadiye wa da gangan, to azuminsa ya baci, wajibi ne bayan watan ramalana yayi ramakon azumin wannan ranar tare da yin kaffara.

{6} Nutsar da dukkanin kai a cikin ruwa ko da sauran jikin mai azumi yana waje da gangan, yana bata azumi a bisa ihtiyadi wajibi a wajen wasu malamai.

Abin da ake nufi da kai shi ne: Dukkanin abin da ke saman wuyan mutum, don haka nutsar da bangaren kai da ya hada da kunne a cikin ruwa baya bata azumi, amma nutsar da dukkanin kai banda gashin kai yana bata azumi.

Amma babu laifi mai azumi ya nutsar da rabin kansa a cikin ruwa, bayan ya dago kan daga cikin ruwan, sannan ya nutsar da daya bangaren rabin kan a cikin ruwa. Kamar yadda babu laifi mai azumi ya sake ruwa mai yawa a kansa, misali mai azumi ya shiga karkashin shower ko ya kwarara ruwa mai yawa a kansa saboda  hakan ba nutsar da kai ba ne a cikin ruwa.

Haka nan mai azumin da ya sanya wani abu a kansa da zai hana ruwa ya ratsa zuwa kan, sannan ya nutse a cikin kogi ko rafi da makamantansu, azuminsa bai baci ba.

Idan mai azumi ya shiga cikin ruwa yana da tabbacin ruwan ba shi da zurfin da zai kai ga nutsar da kansa, sai kuma kansa ya nutse a cikin ruwan, to a nan azuminsa bai baci ba.

Idan mai azumi ya mance ya shiga cikin ruwa ya nutsar da dukkanin jikinsa gami da kansa, to azuminsa bai baci ba, haka nan mai azumin da aka nutsar da shi a cikin ruwa da karfin tsiya ko ya fada a cikin ruwa ba da nufi ba har kansa ya nutse, shi ma azuminsa bai baci.

Idan mai azumi ya shiga cikin ruwa ya nutsar da kansa da dukkanin jikinsa da nufin yin wankan irtimasi bisa ganganci, to azuminsa na ramalana ya baci. Idan kuma bisa mantuwa ne, to wankansa da azuminsa sun inganta.

Idan mai azumi ya nutsar da kansa a cikin ruwa a kokarin da yake yi na ceto wani da ya fada a cikin ruwa zai halaka, azuminsa ya baci  duk da cewa wajibi ne gudanar da ceton.

Amma a wajen wasu malamai ihtiyadi ne wajibi mai azumi ya nisanci nutsar da dukkanin kansa a cikin ruwa, idan kuma ya nutsar, to azuminsa bai baci ba, domin nutsar da kai a cikin ruwa ba shi daga cikin abubuwan da suke bata azumi a wajensu.

 

Add comment


Security code
Refresh