An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 22 June 2015 18:10

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {2}

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {2}
Hanyoyin Tabbatar Da Ganin Wata.

 

 

Hakika ana samun sabani wajen ganin watan kamariyya a kasashe da dama na duniya, inda ake ganin Wata a wannan kasa ba tare da an ganshi a wancan kasar ba, to ko mene ne hukuncin shari’a dangane da wannan matsala ta sabanin ganin wata?

 

Da farko wadansu kasashe suna da kusanci da juna, inda fitowar rana da faduwarta a kasashen biyu ba su da bambanci, ko kuma kasashe ne da dama da suke da daidaiton Ufuki wato kasashen suna nesa da juna amma suna kan layi guda ne na yana yi, inda fitowar rana da faduwarta a tsakanin kasashen suke kusanci da juna.

 

A irin wadannan kasashe idan aka ga wata a daya daga cikinsu zai yiyu a ganshi a sauran kasashen, sai dai idan akwai wata matsala a sararin samaniya da zata hana ganin Watan, misalin kasancewan hadari ko hazo da makamantansu.

 

A gefe guda kuma wadansu kasashen suna da sabanin Ufuki a tsakaninsu saboda ba su kan layi guda na yanayi, wato akwai sabanin lokaci mai tsayi a tsakaninsu wajen fitowar rana da faduwarta. Misali rana ta kan fadi a wata kasa sannan bayan tsawon lokaci ranar ta fadi a wata kasar ta daban saboda sabanin Ufuki dake tsakaninsu.

 

A nan kasancewan bayyanan watan kamariyya bayan haihuwansa yana da alaka da faduwar rana, wato sai rana ta fadi za a ga sabon wata, kuma ana samun sabani wajen faduwar ranar tsakanin wasu kasashe, wanda hakan zai hana yiyuwan ganin Wata bayan haihuwansa a wasu kasashe da suke da sabanin fitowar rana da faduwarta. To a nan mene ne hukuncin ganin wata tsakanin kasashen da suke da sabanin faduwar rana ? Shin kowace kasa zata yi hukunci da ganin watan ta ne? ko kuma idan an ga wata a daya daga cikin kasashe na duniya ya isar a yi hukunci da tabbatansa a sauran kasashe duk kuwa da cewa suna da sabani wajen faduwar rana? Wato shin ganin wata na kamariyya na shari’a lamari ne da ya danganci kowace kasa, wato sai rana ta fadi an ga wata a kasa za a yi hukunci da ganin wata a cikin wannan kasar, ko kuma ganin wata a kowace kasa ta duniya ya isar wajen yin hukunci da ganin wata a sauran kasashe? Wato babu banbanci tsakanin wannan kasa da wancan, da zarar dai an ga wata a wata kasa, ganin watan ya isar wajen tabbatan ganin wata a sauran kasashe?

 

Da farko dangane da hukuncin kasashen da suke da kusanci da juna, inda fitowar ranar da faduwarta a kasashen biyu ba su da banbanci, dukkanin malamai sun yi tarayya akan cewa idan an ga wata a daya daga cikin kasashen, ya isar wajen yi hukunci da tabbatan ganinsa a daya kasar da ba a ga Watan ba.

 

Haka nan hukuncin yake dangane da kasashe da dama da suke da daidaiton Ufuki wato kasashen da suke nesa da juna amma suna kan layi guda na yanayi, inda fitowar rana da faduwarta a tsakanin kasashen suke kusanci da juna. Wato idan an tabbatar da ganin wata a daya daga cikin kasashen da suke da daidaiton Ufuki, ya isar wajen yin hukunci da tabbatan ganin watan a sauran kasashen da suke daidaito da ita a Ufuki, saboda fitowar rana da faduwarta a tsakanin kasashen suna da kusanci.

 

Amma dangane da kasashen da ba su da kusanci da juna kuma ba su da daidaiton Ufuki wato kasashe ne da suke nesa da juna ga kuma sabani wajen fitowar rana da faduwarta a tsakaninsu, anan akwai sabanin malamai dangane da hukuncin ganin wata a tsakanin kasashen kamar haka:-

 

{1} Wasu malamai sun bayyana cewa: Kowace kasa zata yi hukunci da ganin watan ta ne ita kadai. Wato idan aka tabbatar da ganin wata a daya daga cikin kasashen da suke da sabanin fitowar rana da faduwarta, to ba zai yiyu a yi hukunci da tabbatar ganin watan a sauran kasashen ba, saboda sabanin Ufuki da suke da shi.

 

{2} Wasu malaman da suke da ra’ayin cewa idan aka tabbatar da ganin wata a daya daga cikin kasashen da suke da sabanin fitowar rana da faduwarta wato suke da sabanin Ufuki, to kowace kasa daga cikinsu zata yi hukunci da ganin watan ta ce, sun bayyana cewa matukar aka tabbatar da ganin wata a kasar da take gabashi, to za a yi hukunci da ganin watan a sauran kasashen da suke yammacin kasar da aka ga watan, duk kuwa da cewa suna da sabanin Ufuki a tsakaninsu wato sabanin fitowar rana da faduwarta. Amma idan kasar da aka ga watan tana yammaci ne, to ba za a yi hukunci da ganin watan a kasashen da suke gabashinta ba, saboda sabanin ufuki da suke da shi a tsakaninsu.  

 

{3} Wasu malaman kuma sun bayyana cewa ne idan har aka tabbatar da ganin wata a daya daga cikin kasashe ta duniya, to za a yi hukunci da ganin watan a sauran kasashen da suke da sabanin Ufuki a tsakaninsu matukar sun yi tarayya a wani yanki na dare. Dangane da kasar da ba suyi tarayya a dare ba kuwa, misali idan an ga wata a wata kasa a farkon dare, yayin da rana ta riga ta fito a wata kasar ta daban saboda sabanin Ufuki da suke da shi, wato suna da sabanin fitowar rana da faduwarta, to anan kasar da rana ta riga ta fito kafin tabbatar ganin wata, wannan ranar ba ta daga cikin ranakun sabon wata da ya kama, tana daga cikin cikon ranakun karshen watan da ya gabata ne.

 

Hanyoyin Tabbatar da Ganin Watan Ramalana ko Watan Shawwal:-

 

Ana tabbatar da ganin watannin ne ta hanyoyi kamar haka:-

 

{1} Mutum shi kadai ya ga wata da kwayar idonsa. Idan mutum ya ga watan ramalana shi kadai, ganinsa hujja ne a kansa, wato wajibi ne a kansa ya dauki azumin watan ramalana ko da dukkan mutane ba su azumi, idan kuma ya ki yin azumin da gangan ko kuma ya karya azumin bisa ganganci, to wajibi ne yayi ramakon wannan azumin bayan watan ramalana tare da kaffara.

Sannan kuma ganin watan mutum shi kadai ba hujja ba ne a kan sauran mutane har iyalan gidansa, wato ganin watansa ba zai sanya a dauki azumi ba komai gaskiyarsa.

 

Haka nan idan mutum ya ga watan shawwal shi kadai, to dole ne ya sha ruwa, domin haramun ne a kansa yayi azumi ko da dukkanin mutane suna azumi.

 

{2} Shaidar adalai biyu:- Idan mutane biyu adalai suka bada shaidar cewa sun ga watan ramalana, to shaidarsu hujja ce wajen daukan azumi washe gari, kamar yadda take hujja wajen sauke azumi idan watan shawwal suka gani. Hujjar daukan azumi ko sauke wa bisa dogaro da shaidar adalai biyu ta game duk wanda ta riskeshi ko da kuwa ba a gaban shugaba adali suka bada shaidar ba, ko kuma shugaban ya ki amincewa da shaidarsu saboda wani dalili, matukar dai mutanen biyu da suka bada shaidar ganin wata adalai ne a wajen mutum, to shaidar ganin watansu ta zame masa hujja wajen daukan azumi ko sauke wa.

 

Dangane da batun shaidar adalai biyu wajen ganin wata, ba a karban shaidar mutum guda adali ko shaidar mutum guda da mata biyu ko shaidar mutum guda gami da rantsuwa ko kuma shaidar mata hudu.

 

{3} Ganin watan ya kasance daga mutane masu tarin yawa, inda labarin ganin watan zai zame ya game tsakanin al’ummah ko labarin ya zame ya watsu a tsakanin mutane da zai kai ga haifar da tabbaci ko nutsuwa a zuciya, saboda labari ne mai tushe sakamakon yawan mutanen da suka ga watan, wanda zai yi tsananin wuya su yi tarayya a kan karya ko kuskure.

 

{4} Cikan kwanaki talatin a watan da ya gabata:- Idan aka cika kwanaki talatin a watan sha’aban, to washe gari ranar farko ce ga watan ramalana, domin watan kamariyya ba ya haura kwanaki talati.

Haka nan idan aka cika kwanaki talatin a watan ramalana, to washe gari ranar farko ce ga watan shawwal wato ranar salla karama ce.

 

{5} Hukuncin malami da ya cika sharuddan bada hukunci da fatawa a tsakanin mutane da ake kira da “Ha’kimush-Shara’i” .

 

Idan malami da ake kira Ha’kimush-shara’i ya fitar da fatawar ganin wata, to wajibi ne yin aiki da fatawarsa wajen daukan azumin ramalana ko sauke azumi, kuma wajabcin bin umurninsa bai takaita ga masu masa takalidi ba kawai, wajabci ne da ya hada dukkanin mutane har da sauran Mujtahidai da ake musu takalidi.

 

Amma idan mutum yana da masaniyar dalilin da Ha’kimush-Shara’i ya dogara da shi wajen fitar da hukuncin ganin wata kuskure ne, to anan ba zai yi aiki da fatawar ganin watan ba.

 

Idan sabon wata ya fito da haske ko girmansa ya kai ga ya tankwara kamar da’ira ko ya jima bai bace ba har ya kai ga bayan bacewan shafaki, dukkanin wadannan halaye na wata ba dalili ba ne da zai sanya a yi hukunci da bayyanan watan a daren da ya gabata.                           

 

Add comment


Security code
Refresh