An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Monday, 22 June 2015 18:03

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {1}

Shiri Na Musamman Kan Ramadana {1}
Azumi daya ne daga cikin wajibai masu muhimmanci da Allah Madaukakin Sarki ya wajabtasu a kan bayinsa sakamakon irin madaukakin tasiri da fa’ida mai girma da suke da shi a kan mutum da ma al’umma baki daya. Kuma saboda girman matsayin azumin ne Allah Madaukakin Sarki ya wajabta shi a kan sauran al’ummomin da suka gabata kafin zuwan Musulunci kamar yadda ya wajabta shi a kan al’ummar musulmi. Allah Madaukakin Sarki da buwaya yana bayyana cewa: { Ya ku wadanda kuka yi imani! An wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suka gabace ku, ko zaku ji tsoron Allah}. Suratul Baqara Ayah ta 183.

 

 

Rabe-raben azumi na wajibi  a shari’a suna da yawa, amma mafi muhimmanci daga cikinsu akwai azumin watan ramalana mai alfarma, domin yin azumi a cikin watan ramalana yana daga cikin  muhimman wajibai a shari’ar Musulunci, kuma daya ne daga cikin shika-shikan musulunci biyar da aka gina addinin musulunci a kansu.    

 

Har ila yau shari’ar musulunci ta kwadaitar da mutane yin azumi kamar yadda ya zo cikin ingantattun hadisan Manzon Allah {s.a.w} cewa: Hakika azumi garkuwa ne daga wuta. Kuma azumi zakka ne na jiki. Haka nan fadin Manzon Allah da ke cewa: "Barcin mai azumi ibada ne, nunfashinsa da shirunsa tasbihi ne, ayyukansa karbabbu ne, addu’arsa amsassu ne kuma kamshin bakinsa yafi kamshin almiski a wajen Allah".

 

Azumi a lugga yana nufin kamewa daga wani abu, yayin da a shari’a yake nufin kamewa daga wasu abubuwa kebantattun a wani kayyadadden lokaci.

 

Don haka azumi a shari’a yana nufin kamewa daga wasu abubuwa kebantattun da ake kira da “Mufadira’t” a larabce, misalin ci da sha, tarawa da mace, fitar da maniyi, kakaro amai da makamantansu, daga fitowan alfijir zuwa faduwar rana wato daga shigar lokacin sallar asubahi zuwa shigar lokacin sallar magariba da nufin neman kusanci a wajen Allah, inda wajabcin azumi da rana a cikin watan ramalana mai alfarma yake farawa daga farkon ranar watan har zuwa karshenta, wato zuwa lokacin kamawan sabon watan Shawwal.

 

Don haka zamu dan yi takaitaccen bayani kan yadda watan kamariyya yake kamawa da yadda yake mutuwa kamar haka:-

 

Watan sama na kamariyya bayan haihuwansa yana kwanaki ashirin da tara ne ko talatin kafin ya mutu, kamar yadda dalili na shari’a ya tabbatar kuma bincike na ilimi ya karfafa hakan. Domin bincike na ilimi ya tabbatar cewa: Wata yana kewaya duniya ce da take kamar kwallo daga kusurwar yammaci zuwa gabashi, wanda watan kamar duniya ce, rabinsa yana fuskantar rana sai bangaren da yake fuskantar ranar ya yi haske, saboda haka yankunan duniya da suke bangaren hasken watan su kasance a lokacin rana, yayin da sauran yankunan duniya da suke bangaren wata da baya fuskantar rana suke lokacin dare, kuma lokacin da watan ya ci gaba da juyawa sai yankunan da suke rana su koma cikin duhun dare, su kuma yankunan da suke cikin dare su koma cikin hasken rana.

 

Haka watan zai ci gaba da kewaya wa har ya kai ga lokacin da duniya ta shiga tsakanin wata da rana, sannan watan ya ci gaba da tafiya har ya tunkari tsakanin rana da duniya, wadda haskensa zai fara dushewa har ya shiga tsakanin ranar da duniya, sai ya zame hasken watan ya bace, ba a ganinsa, wannan tsakanin rana da duniya ana kiransa da “Almaha’q” kuma buyan hasken watan shi ake kira da mutuwan wata.

 

A lokacin da watan ya fara fitowa daga tsakanin rana da duniya  wato wajen da ake kira “Almaha’q” bangaren watan da yake fuskantar rana haskensa ya fara bayyana ga bangaren duniya dake kusurwan yammaci, wannan bangaren watan da ya bayyana shi ake kira da haihuwan sabon wata wato Hilal a larabce, inda watan zai ci gaba da fitowa daga “Almaha’q” har rabinsa ya bayyana inda ake kiran wata a wannan lokacin da “Badaru” a larabce.

 

Saboda haka a nan zamu fahimci abubuwa kamar haka:- A lokacin da wata ya shiga tsakanin rana da duniya, wajen da ake kira  “Almaha’q” a larabce haskensa ya bace, mutanen da suke duniya  suka bar ganinsa,  shi ake kiran wannan lokacin da cewa Wata ya mutu.

 

A lokacin da watan ya fara fitowa daga tsakanin rana da duniya  wato daga “Almaha’q” haskensa ya fara bayyana ga mutanen da suke duniya, ana kiran wata a wannan lokacin da cewa an haifi sabon wata wato Hilal.

 

A gefe guda kuma malamai sun kasa haihuwan wata zuwa gida biyu kamar haka:-

 

{1} A lokacin da wata ya fara fitowa daga tsakanin rana da duniya  wato wata ya fara fitowa daga wajen da ake kira “Almaha’q” a larabce, hasken watan zai fara bayyana ne a lokacin da rana zata fadi a sararin samaniyar yammaci, wanda baya daukan lokaci mai tsayi yakan bace kuma yana da wahala a ga watan a wannan ranar da kwayar idon dan Adam, a nan hasken watan da ya bayyana wanda ba zai yiyu a ganshi da kwayar idon dan Adam ba, ana kiransa da haihuwan wata na dabi’a.

 

{2} A lokacin da wata ya fara fitowa daga tsakanin rana da duniya  wato haskensa ya ci gaba da bayyana a sararin samaniyar yammaci wanda zai yiyu kwayar idon dan Adam ta iya ganinsa,  sai dai idan akwai wata matsala a sararin samaniya misalin hadari ko hazo da makamantansu, to a nan ana kiran hasken watan da ya bayyana wanda zai yiyu kwayar idon dan Adam ta ganshi da haihuwan wata na shari’a.

 

Sakamakon wannan rabe-rabe zamu fahimci cewa haihuwan wata na dabi’a yana riga haihuwan wata na shari’a, inda a misali watan dabi’a zai fara a daren asabar, shi kuma watan shari’a ya fara a daren lahadi. 

 

Amma abin lura anan shi ne: Haihuwan wata abu guda ne, iyaka dai a lokacin da ba zai yiyu a ga watan ba a ranar farko da kwayar idon dan Adam saboda raunin haskensa shi ne ake kiransa da haihuwan wata na dabi’a, yayin da kuma watan ya ci gaba da fitowa daga tsakanin rana da duniya, haskensa ya ci gaba da bayyana inda zai kai ga matakin da kwayar idon dan Adam zai yiyu ta ganshi idan babu wata matsala a sararin samaniya, ake kiransa da haihuwan wata na shari’a.

 

Bayan takaitaccen bayanin da muka yi dangane da yadda haihuwan sabon wata yake, to abin tambaya anan: Shin ya halatta a shari’a a yi amfani da na’urar zamani kamar madubin hangen-nesa wajen ganin wata?

 

Mashhuriyar magana a tsakanin malamai itace ganin wata dole ne ya kasance da kwayar idon dan Adam. Amma wasu malamai sun bayyana cewa za a iya yin amfani da na’urar zamani misalin madubin hangen-nesa wajen tabbatar da ganin wata. Ga kuma yadda fatawowin malaman suke kamar haka:-

     

Wasu malamai sun bayyana cewa: Matukar wata ya riga ya fito daga “Almaha’q” wato daga tsakanin rana da duniya kuma zai yiyu a iya ganinsa da kwayar idon dan Adam, amma wani dalili ya hana ganin watan misalin hadari ko hazo ko kuma mutane ba su dauki matakin duban watan ba da makamantan haka, to a irin wannan hali za a iya yin amfani da na’urar zamani misalin madubin hangen-nesa wajen tabbatar da ganin watan ko dogaro da fadin amintattun malaman ilimin taurari da suka tabbatar da haihuwan wata ta hanyar fitansa daga “almaha’q” wato daga tsakanin rana da duniya, kuma watan ya kai matsayin da zai yiyu kwayar idon dan Adam ta iya ganinsa, da ba don matsala da aka samu a sararin samaniya ba.

 

Wasu malaman kuma sun bayyana cewa: Koda wata ya riga ya fito daga “Almaha’q” wato tsakanin rana da duniya, kuma zai iya yiyuwa kwayan idon dan Adam ta ganshi, amma wani dalili ya hana ganin watan, to matukar dai kwayan idon dan Adam bai ga watan ba, to ba za a  dogara da fadin malaman ilimin taurari ko yin amfani da na’urar zamani misalin madubin hangen-nesa wajen tabbatar da ganin watan ba, har sai lokacin da aka ga watan da kwayar ido ko kuma wata da ya zo karshe ya cika kwanaki talatin, to anan sai washe gari ya zame farkon sabon wata, domin mun bayyana cewa watan kamariyya baya wuce kwanaki talatin kamar yadda baya kasa kwanaki ashirin da tara bisa dalili na shari’a da ingantaccen binciken ilimin zamani.

 

Fa’ida: Wasu malamai sun bayyana cewa za a iya yin amfani da na’urar zamani misalin madubin hangen-nesa wajen duban wata a sararin samaniya a ranar ashirin da tara da ake fara duban wata, idan aka tantance wajen da yake sai kuma a koma ga dubansa da kwayan ido, inda hakan zai saukaka wa mutane wahalar duban wata.        

Add comment


Security code
Refresh