An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 10 February 2015 19:32

Tsokaci Akan Sakon Jagora Zuwa Ga Matasan Amurka Da Turai: ( 2)

Tsokaci Akan Sakon Jagora Zuwa Ga Matasan Amurka Da Turai:  ( 2)
To har yanzu dai muna a tare da ku ne a cikin jigon da mu ka bude na baya dangane da sakon da jagoran juyin juya halin muuslunci na Iran ya aike wa da matasa da samari na kasashen yammacin Turai da kuma Amurka ta Arewa.  A bangaren farko mun bijoro da muhiman dalilai da su ka sa jagoran ya yi magana da matasa da samarin a daidai wannan lokacin da aka dukufa ka’in da na’in wajen bakanta sunan addinin Musulunci da musulmi a cikin kasashen na turai. Kuma shakka babu ayyukan ta’addanci da ake tafakwa a duniyar Musulunci wanda masu yinsa su ke daga tutar Musulunci yana da tashi rawar da ya ke takawa wajen bai wa masu kin addinin abinda za su fake da shi. Wannan ne ya sa jagoran juyin musuluncin ya kira yi samari da matasan na turai da kada su kalli ‘yan ta’adda a mastayin masu wakilitar addinin Musulunci, maimakon hakan su koma ga alkur’ani mai girma da kuma rayuwar ma’aikin Allah da tarihinsa domin su fahimci hakikanin sakon addinin Musulunci. To da fatan za a kasance a tare da mu domin aji ci gaban shirin daga inda mu ka tsaya.                                *** Daya daga cikin abinda ya bai wa sakon na jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, muhimmanci shi ne ba wai yana kiran samarin zuwa ga fahimtarsa dangane da addinin Musulunci ba ne kamar yadda ya ke cewa: “Ba ni yin naciya akan cewa fahimtata da Musulunci ko kuma wata fahimta ta daban ce kadai za ku karba, abinda na ke cewa shi ne kada ku  bari wannan yanayin da ya zama ruwan dare a duniyar wannan lokacin wanda ya ke kunshe da gurbatacciyar manufa ya zama ya yi lamba.” Bugu da kari, sakon na jagoran bai yi bayani akan shi kanshi musuluncin ba ta fuskar hakikaninsa, abinda ya maida hanakli akansa shi ne cewa hakki ne na dabi’a ga kowane mutum ya sami sani sanann kuma ya gudanar da bincike da nazari domin kai wa ga hakikar da ya ke nema. Domin kuwa nesam sanin gaskiya wata dabi’a ce wacce ta ke tattare da kowane mutum. Kiran da jagoran ya ke yi ga matasa da samarin nahiyar turai yana nufin cewa; Duk wata zuciya mai neman gaskiya ta hanyar komawa zuwa ga alkur’ani mai girma da kuma rayuwar manzon Allah (s.a.w.a) za ta fahimci hakikanin koyarwar addinin Musulunci wacce ta ke cike da sa’adar rayuwa. A dalilin haka, matukar samari da matasan na turai za su karanta su kuma fahimci alkur’ani mai girma da kuma rayuwar manzon Allah, to shakka babu za su riski cewa kungoyin irin su alqaeda da Nusrah da Da’ish, ko Isil da Boko Haram ba su wakiltar addinin Musulunci. Da ya ke tofa albarkacin bakinsa akan sakon na jagora, wani masani dan kasar Amurka Farfesa Kevin Barrett, ya fadi cewa: “A cikin alfahari na ke alfaharin watsa sakon jagoran juyin juya halin Musulunci Na Iran, Sayydi Ali Khamnei zuwa ga matasan yammacin turai da Amurka ta Arewa, wanda ya  ke kunshe da yin kira zuwa gare su da kada su mika wuya ga yanayin da ake ciki na nuna kin jinin Musulunci, ya zamana suna yin tunani cikin ‘yanci. Watakila wasu daga cikin masu karatu su yi mamakin cewa wani jagoran ne na addinin Musulunci ya ke yin kira zuwa ‘yantaccen tunani. A cikin kasashen turai an dauka cewa ‘yantaccen tunani yana cin karo da addinai.” Farfesa Kevin ya kuma ci gaba da yin ishara da wata akida wacce ta zauna da gindinta a tsakanin turawa da ita ce; Yin tunani cikin ‘yanci da kuma addini suna  cin karo ne da juna. Kuma wannan akidar ta samu gindin zama a cikin cibiyoyin ilimi domin tana damfare da abubuwan da suka faru da Galilio da Walter da Darwing da su ka yi fito na fito da majami’u.” A hakikanin gaskiya babu wani cin karo a tsakanin ‘yancin tunani da kuma addini, saboda haka wannan wani tunani ne kuntatacce. Masanin na kasar Amurka ya yi kira da ma’abota tunani a cikin nahiyar turai da su  fito daga cikin ququmin da aka sanya su, su dubi addinin Musulunci da faffadar mahanga su san shi kamar yadda ya ke ba kamar yadda kafafen watsa labaru masu adawa da shi su ke gabatar da shi ba.  ****                                     Wani masanin wanda ya tofa albarkacin bakinsa akan sakon na Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran shi ne Yavuz Özoguz Bajamushe dan asalin Turkiya. A hirar da ya yi da kafafen watsa labarun Iran ya ce; “Muhimmin abin lura da la’akari da shi danagen da wasikar Jagoran Juyi shi ne yadda ya ke magana kai tsaye da matasan yammacin turai ba tare da wani mai shiga tsakani ba. Wannan ne ya sa bayan wani kankanen lokaci da aka watsa sakon a shafin internet na ofishin jagoran, saura shafukan internet da dama da su ka hada da jamus su ka watsa su. Ozoguz ya kuma bayyana sakon a matsayin wani kira zuwa ga farkawa, domin kuwa a halin da ake ciki a wannan lokacin da dama daga cikin matasan turai suna cikin wani yanaki ne na yanke kauna a rayuwa. Wani manazarcin dan kasar Amurka mai suna Stefan Landman ya bayyana sakon na jagora a matsayin kyakkyawan masomi da ba matasa ne kadai za su karanta sh ba domin su yi wa addinin Musulunci kyakkyawar fahimta, hadda ma sauran bangarori daban-daban na al’umma. Farfesa Charles Taliaferro wanda memba ne a cikin kungiyar Malaman Jami’a masana falsafa a Amurka  cewa ya yi; Sakon na jagora ya jefa masu son bakanta addinin Musulunci cikin damuwa domin kuwa ya bayyana cewa;  laifukan da ake tafkawa  ta hanayar fakewa da sunan Musulunci, abin yin Allah wadai da shi ne kuma suna cin karo da koyarwar alkur’ani.” Farfesa Teliaferro ya ci gaba da cewa: A halin da ake ciki a yanzu da akwai mutane masu yawan gaske a nahiyar turai da su ke sha’awar fahimtar addinin Musulunci,  domin musulmin da su ke rayuwa acikin turai din suna rubanya ayyukan da su ke yi. Kuma suna shiga cikin bangarori da dama na rayuwa da su ka hada majalisu da cibiyoyi na shari’a. A dalilin haka, ba ana nuna damuwa ne da Musulunci da musulmi ba, da kuwa hakan ne ai da musulmin ba su sami kutsawa su ka shiga cikin wadannan cibiyoyin ba, abinda damuwa shi ne masu wuce gona da iri da sunan Musulunci, su ke kuma dasa bama-bamai da kai hare-hare da makamai. Sun zabi amfani da karfi maimakon zmaan lafiya.” A tsakanin ‘yan siyasar nahiyar turai ma, sakon na jagoran juyi ya sami tofa albakracin baki. Ga misali, wani dan majalisar dokokin kasar Birtaniya Day Haward ya ce; “Sakon yana nufin kalubalantar wuce gona da iri da kuma kungiyar Da’ish.” Haward ya ci gaba da cewa: “Babban abinda ya ke da muhimmanci a wurina shi ne yadda jagoran na Iran ya yi ishara da abubuwan da mu ka yi tarayya akansu. Ya kirayi samari da matasan yammacin turai da su san Musulunci kai tsaye daga tushensa. Wannan tunani ne mai kyau, domin maimakon ace sun rungumi Musulunci a hannu wasu mutane da ba amintattu ba, su tafi kai tsaye zuwa ga tushen musuluncin su fahimce shi daga can.” Shi kuwa shugaban mabiya mazhabar kiristacni ta Manonite, Rev. David Paula a Amurka da Canada cewa ya yi; Abinda na fahimta daga sakon jagoran Iran shi ne cewa; Yana son matasa da samarin turai su fahimci banbancin da ke tsakanin mafi rinjayen musulmi da kuma tsirarun da su ka zabi hanyar wuce gona da iri. Kuma yana so ne matasan da samarin musulmin su fahimci Musulunci daga hanyar da ta dace.”

Add comment


Security code
Refresh