An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 10 February 2015 19:29

Tsokaci Akan Sakon Jagora Zuwa Ga Matasan Amurka Da Turai: ( 1)

Tsokaci Akan Sakon Jagora Zuwa Ga Matasan Amurka Da Turai:  ( 1)
Adaidai lokacin da kafafen watsa labarun turai su ka cika duniya da yin magangnu da su ke nuni da batunci ga addinin Musulunci da musulmi, jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya fitar d sako zuwa ga matasan turai da su ke a cikin nahiyar turai da kuma Amurka ta Arewa. Sako ne wanda ya kunshi yin kira da dogon nazari mai zurfi akan abubuwan da ake fada akan Musulunci na batunci a cikin kafafen watsa labarun turai. Sakon na Jagoran Juya Halin Musulunci Na Iran, ya zo ne a daidai lokacin da batuncin da ake yi wa Musulunci da musulmi ya kai koli a cikin kwanakin bayannan  a kasar Faransa. Jagoran, ya kira yi matasa da samarin na turai   da kuma Amurka ta Arewa akan su nutsu ku karanta alkur’ani mai girma da  tarihin ma’aikin Allah (s.a.w.a.) domin su fahimci hakikanin sakon Musulunci. Wannan kiran na Jagoran Juyin Musuluncin, ya zo ne a matsayin aiki da fadar Imam Sadiq (a.s) da ya ke cewa; “Ko Je wurin Samari, domin su ne masu karbar gaskiya da sauri, su kuma yunkura akan tafarkin alheri.” Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bude sakon nashi da cewa: “Sakona zuwa gare ku ne matasa, ba kuma saboda na kasakntar da mahaifanku ba ne, sai dai saboda kasantuwar makomar al’ummarku da kasarsu ta dogara ne da ku, kuma da ina ganin yadda neman gaskiya na hakika  ya ke a cikin zukatanku.” A cikin yanayin da ya biyo bayan harin da aka kai a kasar Faransa wanda kuma ya sa wasu kafafen ke kokarin bata sunan Musulunci da bakanta shi a idon duniya, jagoran juyin ya kirayi samari da matasan na turai da Amurka da su gudanar da bincike da nazari mai zurfi akan tushe da dalilan da su ka sa ake nunawa addinin Musulunci kyama. Ya kuma kiraye su, da su yi bincike dangane da addinin Musulunci daga tushensa  da su ne alkur’ani mai girma da kuma tahinin ma’aikin Allah (s.a.w.a). Abu ne da babu shakku a cikinsa cewa matukar samari da matasan na turai za su yi aiki da wannan kiran su gudanar da bincike da nazari daga tushen Musulunci, abubuwa da dama da su ka shige musu duhu za su bayyana a fili. Wani sashen na sakon ya kira yi samari da matasan turai din da cewa kada su bari mutane masu fuska biyu da kuma ‘yan ta’adda su zama abinda su ke kallo a matsayin masu wakiltar addinin Musulunci. Maimakon haka su koma zuwa ga koyarsa Musulunci ta asali da su ne alkur’ani mai girma da kuma rayuwar manzon Allah domin su fahimci abinda addinin Musulunci  ya kunsa. Jagoran ya yi wasu tambayoyi ga matasa da samarin musulmin da su ka kunshi ko sun taba jin  wani bayani akan addinin Musulunci daga wata kafa ta Musulunci kai tsaye ba daga kafafen watsa labaru ba? kuma ko sun taba karanta alqur’ani da kansu wanda shi ne littafi mai tsarki a wurin musulmi? Kuma sun taba yi wa kawukansu tambaya akan ginshikai na tunani  da kyawawan halaye wadanda addinin Musulunci ya doraga da su wajen gina ci gaba mai girma na bil’adama sannan kuma ya samar da ma’abota tunani  da masana masu yawan gaske a tsawon tarihi?  *****                                           Alkur’ani mai girma wanda zancen Allah ne, yana cike da ayoyin da duk wanda ya karanta shi zai fisgu zuwa gare shi, musamman matasa da samari masu neman gaskiya da son riskarta. A cikin aya ta 8 suratu An’am, Allah madaukakin sarki yana fadin cewa: “Kada kiyayya da mutane ta kai ku ga yin sabon watsi da adalci. Ku yi adalci, shi ne mafi kusanci zuwa ga tsoron Allah. Ku ji tsoron Allah, domin shi masani ne akan abinda ku ke aikatawa.” Duk wani mai neman gaskiya tsakani da Allah, zai rusuna a gaban wannan irin kira zuwa ga aiki da adalci koda kuwa akan wanda ake kiyayya da shi. Har ila yau, zuciyar samarin da su ke neman gaskiya bilhakki za ta girgiza saboda jin kiran alkur’ani mai girma zuwa ga ma’abota littafi kamar yadda ya zo a cikin aya ta 64 Suratu al-Imrana: “ Ka ce ya ku ma’abota littafi ku zo izuwa Kalmar da ta ke daidai ce a tsakaninmu da ku; Kada mu bautawa wani sai Allah, kada mu hada wani abokin tarayya da shi, kuma kada wani sashenmu ya dauki sashe a matsayin iyayengiji; Idan kuwa su ka juya baya, to ku ce; Ku zama shaida mu kam musulmi ne.” Wanda duk ya fahimci wannan ayar babu yadda zai damfarawa addinin Musulunci tashe-tashen hankula da zubar da jini.  Ko kuma aya ta 108 da tazo a cikin suratu An’am da Allah madaukakin sarki ya ke cewa: “Kada ku zagi wadanda su ke bautar wani abu ba Allah ba, sai su zagi Allah bisa kiyayya da rashin sani. “ Matukar matasa da samarin nahiyar turai za su karanta alkur’ani mai girma za su fahimci cewa addini ne wanda ya ke bada ‘yancin tofa albakracin baki kamar yadda ya zo a cikin aya ta 6 da ke cewa: “Idan wani daga cikin mushrikai ya nemi mafaka a wurinka ka ba shi, saboda ya ji zancen Allah, sannan kuma ka mai da shi zuwa wurinsa na aminci. Domin kuwa su mutane ne da basu da masaniya.” Babu yadda za a yi wani matashi da saurayi wanda ya ke amsa kiran lamirinsa, kuma ya ke aiki da hankalinsa da zai yi wa addinin Musulunci fassarar da ta sabawa  hankali da mandiqi matukar dai ya karanta wadannan ayoyin da su ka gabata da kuma wasu masu yawa. Ta fuskar kyawawna halaye da rayuwar zamantakewa mai nagarta, da akwai ayoyi masu yawa a cikin alkur’ani da duk wanda ya karanta su, matukar yana da rayayyen lamiri zai fahimci matsayin alkur’ani mai girma da sakon da ya ke dauke da shi zuwa ga bil’adama.Aya ta  8 acikin suratu Ankabut tana kira zuwa ga kyautatawa iyaye, ko kuma aya ta 19 Suratu Nisa’i da ta ke kira ga kyautatawa iyali.    

Add comment


Security code
Refresh