An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 02 November 2014 18:44

Sirrin Wanzuwar Ashura.

                   Sirrin Wanzuwar Ashura.
Wa’kiar Krabala tana daga cikin tsirarun abubuwan tarihi da su ka faru, wadanda su ke da matsayi na musamman.  Fiye da shekaru 1000 sun wuce daga faruwarsa, amma duk da haka yana kara karsashi a duk lokacin da zamani ya ke tafiya.   A farkon faruwar waki’ar Ashura; Banu Umayya sun yi duk abinda za su iya domin su karkatar da manufarta da ma gurbata ta. Sun rika yin bukukuwa idan Ashurar ta zo. Bayan Umayyawa, Daular Abbasiyawa sun dauki shekaru 700 suna kokarin rusa duk wani abu mai alaka da Ashur’a da kawar da mutane daga yunkurin Imam Husain (a.s). Kuma har yanzu azzalumai da  masu girman kai, suna ci gaba da yin kokarin da ba zai kai su ko’ina ba  domin gurbata Ashura da sakonta. Wannan ne ya sa a kodayasuhe tambaya ta ke tasowa akan ko menene sirrin wanzuwar Ashura da kuma sakon da ta ke dauke da shi? Kuma me ya sa duk da kokarin da azzalumai da  masu girman kai su ka yi a tsawon daruruwan shekaru na murkushe shi amma ya ke ci gaba sannan kuma ya ke kara karasashi? Shakka babu da akwai dalilai masu yawa da su ka taka rawa wajen ci gaba da kuma wanzuwar Ashura.. Dalili na farko dai shi ne nufin Allah, kamar yadda ya ke fada a cikin aya ta 8 suratu “Saf” “Suna son su dushe hasken Allah, amma Allah mai cika haskensa ne.” Kasantuwar yunkurin Imam Husain (a.s) na Ashura, mai nufin kare addinin musulunci ya shiga karkashin wannan fadar ta Ubangiji. Saboda haka baya ga kiyaye wannan hasken da Ubangii madaukakin sarki ya yi, kuma aduk lokacin da zamani ya ke kara ja, yana kara karasashi. Ya zo a cikin nassi na hadisi cewa; " Shahadar Imam Husai tana da karasashi a cikin zukatan mutanen wanda ba zai taba dushewa ba." Bugu da kari, wani daga cikin dalilan wanzuwar Ashura' shi ne yadda manzon Allah (s.a.wa.) ya yi maganganu akan matsayin Imam Husain (a.s). A tsawon tarihin musulunci kuwa al'ummar musulmi sun zama masu girmama da ganin matsayin maganganun manzon Allah (s.a.wa.). Adailin haka ne malaman addinin musulunci da dukkanin mazhabobinsu na sunna da shi'a su ke wajabta yin biyayya ga manzon Allah (s.a.w.a). A cikin suratu Nisa'i, aya ta 80 Allah madaukakin sarki ya bayyana wajabcin yin biyayya ga manzon Allah (s.a.w.a). Kuma a cikin ayoyin na 3 da 4 na suratu Najm, Allah madaukakin sarki ya bayyana cewa duk abinda manzon Allah (s.a.w.a) ya fada ya samo tushe ne daga wahayi. Manzon Allah (s.a.w.a)  ya yi magana akan matsayin Imam Husain (a.s)  da bayyana shi a cikin wani hadisinsa da cewa; shi jagorane. Salmanul-Parisi wanda daya ne daga cikin sahabban manzon Allah (s.a.wa) ya nakalto daga manzon Allah (s.a.wa.) cewa; "Kai jagora ne, kai dan jagora ne kuma mahaifin jagorori. Kai imami ne kuma dan imami da mahaifin imamami. Kai hujja ne kuma dan hujja kuma mahaifin hujjoji. Mahaifin jagorori tara ne kuma na taransu shi ne ma'abocin tsayuwa." Baya ga ambaton matsayar Imam Husain (a.s.) da manzon Allah ya yi, ya kuma yi hasashen yin shahadarsa. Fitaccen masanin hadisan nan na ahlusunnah Athir al-Razy, ya nakalto daga Ash'as Bin Sahaim  daga mahaifinsa  daga manzon Allah (s.a.wa) yana cewa: " Dana, Husain (a.s)  zai yi shahada a wani wuri a kusa da Iraki, duk wanda ya riske shi  wajibi ne ya taimaka masa." Wani hadisin daga A'isha matar manzon Allah (s.a.w.a) ta rawaito cewa manzon Allah ya sumbaci Husain (a.s) sannan ya ce; "Duk wanda ya ziyarci kabarinsa yana da lada na aikin haji." Wasu daga cikin dalilan wanzuwar Ashura shi ne yadda  jagororin iyalan gidan manzon Allah (s.a.w.s) suka rika raya ita kanta Ashura. A duk lokacin da dama ta samu ko kuma Ashura ta zagayo, to sukan jaddada amabton abinda ya faru a Ashura da kuma ambaton masifar da ta faru a cikinta.                                                          *****   Ita kanta manufar yunkurin na Imam Husain (a.s) wanda ya bayyana shi karara yana daga cikin abubuwan da su ka dawwamar da yunkurin.  Imam Husain (a.s) ya bayayna cewa: " Na fito ne domin in yi gyara a cikin al'ummar kakana, ina son in yi umarni da kyakkyawa, in yi hani da mummuna, domin Allah madaukaki  yana fada a cikin al'kur'ani cewa; Wajibi ne a sami wata al'umma a cikinku da su ke umarni da kyawawa, su ke kuma hani da mummuna." Daga cikin nau'oin umarni da kyawawan ayyuka,  da akwai kiran azzalumi da ya daina zaluncin da ya ke yi. Idan kuwa wata hukuma ta zama tana jefa shi kanshi koyarwar addinin musuluncin cikin hatsari, to wajibi ne a kalubalance ta. Ynukurin na Imam Husain (a.s) na Ashura ya kalubalanci hukumar zalunci ne wacce aikita shi ne rusa addinin musulunci daga tushensa, da maida al'ummar musulmi zuwa tsarin baya na jahiliyya. Kuma duk da cewa a zahiri, an kashe Imam Husain da kuma sahabbnsa a karbala, wanda kuma shakka babu ya girgiza al'umma musulmi, sai dai a lokaci guda Ashur'a ta zama falin dagar farko na kare addinin Musulunci, wanda hakan yana cikin muhimman dalilan wanzuwarta.

Add comment


Security code
Refresh