An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Tuesday, 11 February 2014 16:21

Bunkasar Ilimin Mata A karkashin Juyin Musulunci

Bunkasar Ilimin Mata A karkashin Juyin Musulunci
  Shakka babu daya daga cikin ma’aunin da ake dora ci gaban kowace kasa akansa shi ne yadda ta ke samun bunkasa ta fuskar ilimi da ci gabansa. Bayan nasarar juyin musulunci, Iran ta samu ci gaba ta fuskoki da dama na ilimi da al’adu da tattalin arziki da fuskoki masu yawa a tsarin zamantakewa. Daya daga cikin taken da tsarin juyin musulunci ya rika bayarwa shi ne ci gaban mata ta kowace fuska ta ilimi. A yanzu an wayi gari cewa mata a Iran sun sami ci gaba ta fuskar ilimomi masusarkakiya na zamani da su ka hada ilimin tsarin halitta da Nano,      (Nanotechnology) da ilimin sararin samaniya da ilimin Nukiliya da bangarori daban-daban na ilimin likitanci. Cibiyar kasa da kasa mai gwada ci gaban ilimi na kasashen duniya, mai suna ( Scimago ) ta bayyana cewa;   “ Ci gaban da Iran ta ke samu ta fuskoki daban-daban na ilimi zai maida ita zama ta hudu a duniya daga nan zuwa shekara ta 2018.” A halin da ake ciki a yanzu, cibiyoyin ilimi na duniya masu yawa sun yi furuci da cewa ci gaban da  mata su ke samu a Iran yana da jan hankali matuka. Abdulkadir Tomy wanda malamin jami’a ne a kasar Aljeriya ya  yi ishara da parpagandar da kasashen yammacin turai su ke yi akan mata a Iran sannan ya ce: “ Kasantuwar mata akan mukaman da su ka hada minista da mai Magana da yawun ma’aikatu daban-daban da kuma malaman jami’oi da aikin likita da matuka jirgin sama, yana nuni da cewa sun samu gaggarumin ci gaba fiye da kasashen turai da dama.” Shekaru 35 sun shude daga cin nasarar juyin juya halin musulunci a Iran, kuma a wannan tsakanin an yi dokoki masu yawa wadanda su ka saukakawa mata samun dama a cikin bangarori daban-daban na rayuwa domin su taka rawa. Daga cikin wadannan irin dokokin da aka yi da akwai fagen ilimi da basu damar shiga kowane irin fage na ilimi. Kididdiga tana nuni da cewa a cikin gomiya uku ta rayuwar juyin juya halin musulunci an sami karuwar mata masu yawan gaske da su ka sami ilimi na koli. “Yan matan da su ke dauke da takardun shaidar karatu ta koli ya dara na matasa maza a cikin shekaru biyu zuwa uku da suka gabata da kaso 44%.  Jumillar mutanen da su ked a ilimi a cikin fadin Iran baki daya kamar yadda hukumar kididdiga ta kasa ta sanar a shekarar 2011, shi ne kaso 93.2.%. Kuma kusan rabin wannan adadin mata ne. Bayan juyin musulunci babu shinge da aka sanya a tsakanin mata da maza ta fuskar ilimi da nemansa. Wannan kuma ya taimaka wajen sauya yadda a baya ake daukar mace da daukar yadda ya kamata ace ta kasance a tsakanin al’umma. A cikin jami’oi da manyan cibiyoyin ilimi, mata ne su ke da damar da ta kai kaso 65 % na yin karatu. Wannan ya zama wani ma’auni mai girma na ci gaban da Iran ta ke samu ta fuskar ilimin mata. Ya kuma sa matan sun zama masu taka gagarumar rawa a cikin fagagen masu yawa na rayuwa, wanda kuma sa al’umma ta yarda da hakan. Aikin likitanci yana daga cikin fagagen da mata a Iran su ka sami gagarumin ci gaba a cikinsa bayan cin nasarar juyi. Idan kuwa za a kwatantasu da takwarorinsu na yammacin turai, to a ga cewa ci gaban da su ka yi na azo a gani ne. Wasu malaman jami’ar ilimin likitanci a garin Shizar da ke Tehran sun gudanar da nazari a tsakanin mata da su ke a tsangayar ilikitanci na wannan jami’ar da kuma takwarorinsu na Jami’ar Amurka. Daga cikin sakamakon da su ka samu da akwai cewa da akwai fifiko akan yadda mata su ke cikin majalisar tafiyar da tsangayar ilimin likitanci a jami’ar Shiraz fiye da yadda su ke a cikin jami’oin Amurka. A cikin tsangayar ilimin aikin likitanci ta jami’ar Shiraz da akwai fifiko na kaso 35% na matan da su ke koyarwa a matsayin malamai da kuma a cikin tsangayoyi 106 na ilimin likitanci a jami’oin Amurka. Wannan nazarin yana  yaye kallabi ne akan girman parpagandar da ake yi akan mata a Iran bayan cin nasarar juyin musulunci, inda ake bayyana su a mastayin wadanda ake takewa hakkoki. A fuskar aikin likitanci a asibitoci da dakunan bada magani, mata sun sami ci gaba a karkashin juyin musulunci fiye da baya. A Iran kaso 49 % na likitoci, sannan  kuma kaso 40% na kwararru a fagage na musamman na bangarorin likitanci, mata ne. A fagen ilimin fasahar Nukiliya ma ba a bar mata a baya ba a Iran ba. Dr Freshteh Isma’il Biky tana daya daga cikin irin wadannan matan, domin memba ce a cikin kwamitin koli na masana ilimin fasahar Nukliya a Iran. A fagen ilimin kimiyyar sanadarori ma mata a Iran suna taka rawa daidai da maza. Malama Afasaneh Safawiyyah tana daga cikin matan da su ka yi fice a wannan fage wadanda kuma su ka sami kyautuka na kasa da kasa a fagen ilimin kimiyyar sanadarori. Ta hanyar dogaro da addinin musulunci da koyarwarsa wacce ta bai wa ilimi muhimmanci juyin musulunci na Iran baya yin kasa a guiwa a wannan fagen.Jagoran juyin musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamnei yana fadin cewa: “ Girmama mata yana nufin a basu dama domin su bayyana baiwar da Allah ya yi wa kowane mutum.”

Add comment


Security code
Refresh