An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 09 August 2013 04:49

Karamar Salla

Karamar Salla
Ranar 1 ga watan shawwal, ita ce ranar idi ko karamar salla wacce al’ummar musulmi su ke bikin zuwanta. A wannan ranar musulmi kan sabunta tufafinsu da kuma ambaton Allah domin zuwa sallar idi. Suna tafiya akan hanya suna zikirin Allah na daukaka girman Ubangiji da kadaita shi da yi masa godiya akan shiriya. Manzon Allah (s.a.w.s) ya umarci msuulmi da cewa a ranakun idi na karamar salla da babba su rika fadin cewa; “ La’ilaha illaha, wallahu Akbar, walhamdulillah, wa subhanallah.” Shi kan shi ma’aikin Allah a ranar idi yana yawaita yin wannan zikirin. Yana kuma sanya tufafi masu tsafta kamar yadda ya saba, sannan kuma ya shafa turare. Da haka ya ke isa masallaci inda ya ke jagorantar sallar idi. A tsakanin hububobin da ya ke gabatarwa yana yin kabbarori da zikirin da ya zo a sama. Imam Riza (a.s) ya bayyana zikirin da ake yi a ranakun idi da cewa ma’anarsa girmaama Ubangiji madaukakin sarki wanda kuma wani nau’i ne na godiya ga Allah bisa shiriya da kuma ni’imominsa.” Sallar idi wani nau’I ne na ibada da musulmi su ke yi a cikin jam’i. Idan mutum yana a cikin wata daga cikin kasashen musulmi zai iya ganewa idanunsu yadda farin ciki da murna su ke gama gari. Farin cikin da musulmi su ke yi a wannan rana yana kunshe da yadda su ke kuma dadadawa waninsu ta hanyoyi da dama. Ba kuma saboda sun kare azumi ne na tsawon kwanaki 30 su ke murna ba, murna ce akan cewa sun tseratar da kawukansu daga aikata sabo sannan kuma da sabunta rayuwarsu. Ramadan wani yanayi wanda ya ke bai wa musulmi dama ya yi wa kansa wanka da jaddada rayuwarsa. Abinda ya ke nesanta musulmi daga aikata abubuwan da su ka kaucewa fidirarsa. Wannan tsarki na ruhi da musulmi ya ke samu a cikin watan Ramadan ya cancanci yi wa Allah godiya akan shiriya. Sallar idin bana ta zo wa musulmi a cikin wani yanayi na daban mai cike da kalubale da matsaloli masu yawan gaske. Wannan kadai, ya isa zama wani cikas wajen yin bukukuwa da murna kamar yadda ake yi a baya. Duk da cewa da akwai matsaloli a kasa da ake fuskanta a cikin kasashen musulmi, musulmin na girmama wannan rana da gudanar da dukkan ladubban da su ke cikinta. An kunna wutar fitina a cikin kasashen Syria da Masar da Bahrain da Tunisiya da Afghanistan da sauran kasashen musulmi da dama. Wannan kadai ya isa hana musulmin da su ke cikin wadannan kasashen jin dadi da farin ciki kamar yadda ya dace dangane da idi. Kuma har yanzu Palasdinu na ci gaba da zama a karkashin mamayar ‘yan sahayoniya bayan tsawon shekaru 65. Musulmin kasashen Afghanistan da Iraki da Pakistan suna ci gaba da fuskantar hare-hare daga masu akidar kafirta musulmi. A lokaci guda kuma yammacin turai na ci gaba da cutar da su. Makiyan musulunci, ba su kaunar ganin cewa musulmi sun rayu cikin ‘yanci  kamar mabiya sauran addinai. Basu kuma son ganin cewa musulmi sun rayu cikin kauna da girmama juna. Wadannan makiya ne su ke cin moriyar sabanin da ke tsakanin musulmi saboda haka su ke ruruta wutar rikicin mazhaba. A cikin kasashen musulmi daban-daban ana gabatar da bukukuwan salla ta hanyoyi mabanbanta. A cikin kasar Syria ana kawata tituna da fitilu masu haske, mutane kuma suna sabunta tufafinsu. Haka nan kuma suna tsaftace gidajensu domin karbar baki. Suna kuma sayen kayan lashe-lashe da tande-tande masu zaki domin rabawa kananan yara. Sai dai a halin da ake ciki a yanzu wannan kasa ta Syria na fuskantar hare-hare munana daga masu akidar kafirta musulmi. Wadannan mutane sun lalata biranen kasar Syria sun rusa gidaje. Sun kashe kananan yara da mata. Wannan halin da mutanen Syria su ke ciki ya sanya yin murna a ranar kamar yadda sauran ‘yan uwansu musulmi na wasu kasashe su ke yi da wuya. Taron da ake yi na sallar idi wani taro mai girma wanda zai iya zama na nuna karfin da al’ummar musulmi su ke da shi, da kuma cusawa makiyansu razana. A tsawon lokaci kuwa wannan gagarumin taron ya fuskanci sauye-sauye masu dama. Sarakunan da su ka zo daga baya sun sauya yadda taron sallar Idi ya kasance a lokacin ma’aiki. Halifofin daulolin Banu Umayya da Abbasiyya sun rika zuwa masallacin idi akan dawakai na kawa wadanda aka yi wa kwalliya da zinariya. Suna kuma rike da takubban gwal, a bayansu kuma fadawa ne bayi biye da su kamar za su tafi filin yaki. Alhali za su je filin idi ne su yi salla raka’a biyu sannan su koma gida. Wata rana halifan Abbasiyya  Ma’amun ya bukaci Imam Rdha (a.s) ya jagoranci sallar idi, saboda ya yi amfani da wannan damar ya karawa mulkinsa matsayi. A tashin farko Imam Ridha bai karba ba, sai dai  ya ga naciyar Mamun sannan ya karba masa. Sai dai ya kafa masa sharadin cewa: “Zan amince  bisa sharadin zai yi salla ne kamar yadda kakana  manzon Allah (s.a.w.a ) da kuma ubana Ali (a.s) su ke yi. A ranar idi, Imam Ridha ya bukaci mabiyansa da su sanya tufafi ba na nuna kai ba, su kuma tafi masallacin idi a kafa ba tare da takalma a kafafunsu ba cikin nutsuwa da tsoron Allah. Shi ma Imam Ridha ya sanya tufafi da rawani kamar yadda kakansa ma’aikin Allah ya ke yi. Ya fita daga gidansa yana yin kabbarorin da ake yi a wannan rana. A wannan lokacin mutane sun dade ba su ga wannan irin yanayi ba. Lokacin da Imam Ridha ya fito yana kabbara  mutanen garim Maro suna amsawa. Lokacin da labari ya isa ga Mamun akan halin da garin Maro ya shiga, ya ji tsoron cewa idan har ya isa filin idi, to abu ne mai yiyu wa a yi wa hukumarsa bore. Ya aike wa da Imam sakon cewa ya koma gida kada ya isa masallacin idi. Sakon da ya ke cikin wannan shi ne idan har za a gudanar da sallar idi a cikin ruhinta na hakika, to za ta iya zama mai ranaza maikiya da su ke nufin musulunci da sharri.

Add comment


Security code
Refresh