An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 16 May 2013 17:47

Yakin Da Kasashen Duniya su ka shelanta Akan Kasar Syria.

 Yakin Da Kasashen Duniya su ka shelanta Akan Kasar Syria.
  A wata hira da kafafen watsa abarun kasar Turkiya da su ka hada telbijin din  Olosal da jaridar  Edin Link su ka yi da shugaban kasar Syria Bassharu Assad, ya fadi cewa:   “Yakin da ake yi a kasarsa ba yakin cikin gida ba ne, yaki ne wanda kasashen waje su ka shelanta akan kasar.”  Har ila yau shugaban na kasar Syria ya ce; yakin da ake yi ba yaki ne a tsakanin mazhabobi ba, yaki ne a tsakanin  kasar Syria da kasashen yammacin turai da larabawa.” Wannan bayanin na shugaban kasar ta Syria ya zo ne a matsayin maida martani ga abinda kafafen watsa labarun turai su ke watsawa na cewa, Syria ta fada yakin basasa a tsakanin ‘yan kasarta. Sai dai tsayin daka na shekaru biyu da gwamnatin Basshar Asad ta yi wajen fada da masu dauke da makamai da kasashen yammacin turai su ke goya wa baya, ya tabbatar da cewa abinda ya ke faruwa a cikin wannan kasa ba yakin basasa ba ne, yaki ne wakilci. Manufar wannan yakin kuwa shi ne fitar da kasar syria daga cikin sahun masu yin gwagwarmaya da kuma fada da h.k. Isra’ila. Sojojin kasar Syria kuwa sun yi nasarar kame masu dauke da makamai da dama da su ka fito daga cikin kasashen duniya daban-daban. Kuma rahotanni daban-daban na cibiyoyin leken asiri sun tabbatar da cewa sojojin syria sun fara fada ne da masu dauke da makamai da su ka fito daga kasashen wajen kafin wasu yan kasar Syria shiga ciki. Orien Y jealing na cibiyar tattara bayanai da ke a birnin London na kasar Birtaniy  ya bayyana cewa; Da akwai fiye da ‘yan ta’adda dari shida da su ka fito daga kasashe daban-daban na turai wadanda su ka tafi kasar Syria domin yin fada da gwamnati. Jealing ya yi imani da cewa a halin da ake ciki a yanzu, kasar Syria ta zama wani gagarumin sansani na masu taya kayar baya. Muhammad Bn Sa’ad a’li Mufrah shugaban jam’iyyar “Hizbul-Ummah’ da ke kasar Saudiyya wanda kuma yana daya daga cikin masu bada goyon baya ga kuniyar ‘yan ta’adda ta “Jabhatun-Nasarah’ ya rubuta a cikin wani shafinsa na hanyar sadarwa ta internet cewa; da akwai mayaka dubu 12 da su ka fito daga kasashen larabawa daban-daban da su ke yin yaki a cikin kasar Syria. Shi kuwa kakakin ma’aikar harkokin wajen Rasha Alexader Lokaswitch ya bayyana cewa; A halin yanzu kasar Syria ta zama sansanin da ke jawo ‘yan ta’adda wanda hakan lamari ne mai ban tsoro.” Bayan da al’ummu daban-daban na kasashen larabwa su ka fara yankurawa domin samar da sauyi a cikin kasashensu a arewacin Afrika da kuma gabas ta tsakiya, kasashen yammacin turai, sun yi kokarin yi wa wannan yunkurin na al’umma hawan kawara domin karkatar da manufofinsa. Kasar Syria kuwa tana da matsayi na musamman a karkashin siyasar Amuerika da kuma kawayenta. Turkiya da kasashen kama-karyar larabawa irin su Saudiyya da Qatar sune ‘yan koren  Kasashen Amerika da yammacin turai wajen aiwatar da wannan siyasar a cikin wannan yankin na gabas ta tsakiya. Syria kasa ce mai muhimmacin a cikin siyasar gabas ta tsakiya. Dukkanin kokarin da kasashen turai su ka yin a sauya akalar wannan kasa ta zama mai biyayya a gare su ya ci tura. A cikin wannan kasa ne kungiyoyin gwagwarmayar palasdinawa su ked a matsuguni kuma tana kan gaba wajen tallafawa da taimakawa gwagwarmayar kasar Lebanon. Kasashen yammacin turai sun yi amfani da farkawar al’ummar larabawa da yunkurin sauyin da ya ke ci gaba, da daukarsa a matsayin wata dama mai tsoka a gare su wacce za su yi amfani da ita domin tilastawa kasar Syria ta zama mai yi musu biyayya.  “Yan hamayyar siyasa na cikin gidan Syria, ba wadanda su ke a waje ba, tun a tashin farko sun bayyana cewa manufarsu ita ce samar da sauyi ta hanyar tattaunawa ba ta hanyar rikici da fadace-fadace da zubar da jini ba. Saboda wannan matsayin na ‘yan hamayyar siyasa na cikin gidan Syria yana cin karo da manufofin yammacin turai, kafafen watsa labarunsu ba su ko ambatonsu balle ba su dammar bayyana matsayin nasu, kamar yadda su ke yi wa sauran kungiyoyin da su ke damfare da su masu dauke da makamai. Kasashe irin su Turkiya da Qatar da Saudiyya sune masu bada makamai da kudi da hanyoyin sadarwa da kuma bude kafafen watsa labarunsu ga kungiyoyin da su ke dauke da makamai. Kungiyoyi ne na mutanen da shekaru biyu da su ka gabata babu wanda ya san da su a fagen siyasar kasar Syria. An samar da mafi yawancinsu ne bayan rikicin kasar Syria. Saboda haka matsayinsu bai wuce na suna akan takardu ba. Kuma kasahen  Saudiyya da Qatar da Turkiya sun fara tattaro duk wani dan ta’adda da ‘yan daba da ‘yan kalare daga cikin kasashen du niya, sannan su ka basu horo na soja domin su yi yaki a kasar Syria. A cikin wasu kasashen na larabawa kamar Saudiyya an yi wa fursunoni masu aikata laifi afuwa da zummar tura su Syria su yi yaki acan wajen kifar da gwamnatin Basshar Asad. A gefe daya wasu kungiyoyin ‘yan salafiyya masu daskararren tunani irin na mazauna kogo, sun rika aikewa da mambobinsu zuwa kasar ta Syria da zummar yin ayyukan ta’addancin da su ke kira jihadi. Kungiyar al’ka’ida ce a gaba-gaba wajen tura mayaka cikin kasar Syria. Kungiya ce wacce a zahiri Amerika ta ke dauka a matsayin abokiyar gabarta, amma a yanzu ta zama cikin sahun farko na masu yi mata hidima. Kuma wadannan kungiyoyin na masu wuce gona da irin da sunan addini sun masu taimako ne kai tsaye na makamai da kudi daga Amerika da kasashen yammaccin turai. Kuma duk yadda wadannan kungiyoyin a zahiri su ke daga tutar musulunci wajen yin yaki da sojojin Syria, sai dai a fili ya ke cewa tsakaninsu da sanin hakikanin musulunci nisansa ya kai tazarar da ta ke tsakanin sama da kasa. Babu wani ta’addanci da barna wacce ba su aikatawa da sunan musulunci. Duk wani yanki da su ka shiga su ka shimfida ikonsu a cikinsa to za su aikata barna da ta’addancin da ko kare ba zai ci ba. Kasashen yammacin turai suna cin moriyar barnar da kungiyoyi irin wadannan su ke yi ta hanyoyi da dama. Daga cikinsu akwai barin wadannan mutanen su bata sunan musulunci a idon duniya da bayyana shi a matsayin na ta’addanci da rashin hankali da kuma rashin kimanta rayuwar bil’adama. A lokaci guda kuma suna yi musu aiki ta hanyar fada da abokin gabarsu ba tare da su sun shiga ciki ba. Wanda ya ke nufin cewa musulmi ne su ke kasha junansu da kansu ba wai makiya ne na waje su ke kashe su ba.

Add comment


Security code
Refresh