An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 16 March 2013 17:48

Dalilan Daukaka Ko Faduwar Mutum

Dalilan Daukaka  Ko Faduwar Mutum
  Mutum, halittar Ubangiji ne mai cike da baiwa, kuma bisa radin kansa zai iya kai kansa zuwa ga abubuwa masu kyau ko kuma munana. Wannan 'yancin da ya ke shi ya bashi damar samun daukaka sama da mala'ika ko kuma ya fadi ya ci kasa fiye da dabba. Al'kur'ani mai girma ya yi cikakken bayani akan dalilan daukakar mutum da samun kusacin da ubangiji, haka nan kuma. Ginshikin da ke sa mutum ya sami daukaka kai wa koli shi ne imani da ubangiji. Mutum zai iya kai wa ga samun matsayi na koli ta hanyar amfani da baiwar da ta ke tattare da shi wacce ubangiji ya halicce shi da ita. A cikin suratul Bakara aya ta 186 Allah madaukakin sarki yana fadin cewa: " Su, amsa kirana su kuma yi imani da ni ko sa samu shiriya." A cikin suratul mujadalah aya 11 ubangiji madaukakin sarki yana fadin cewa: " Allah zai daga darajojin wadanda su ka bada gaskiya daga cikinku da wadadna aka baiwa ilimi. Allah kuwa masani ne da abinda ku ke aikatawa." Wani masani mai suna Khaje Nasruddin Tusi ya fassara imani da cewa; shi ne karba da yarda da wani abu, kamar imani da ubangijin talikai da rayuwa bayan mutuwa da annabci da kuma sauran abubuwa masu tsarki. A fili ya ke cewa yin imani da abubuwa masu tsarki musamman imani da Allah yana da tasiri mai girman gaske ga ruhin mutum. Imani yana baiwa mutum karfi dauriyar wahala da kuma cusa masa fata da sadaukar da kai. Haka nan kuma yama sanya rayuwa ta zama mai cike da nishadi. Ya kuma nesanta mutum da damuwa da zullumi. Ya kuma baiwa mutum damar nesantar ayyukan sabo. Yana kuma baiwa mutum jarunta  da gwarzantaka. A karshe kuma ya baiwa mutum nutsuwa. Hakan ya zo a cikin kur'ani cewa; Da ambaton ubangiji ne zukata su ke samun nutsuwa. Yin dubi a cikin rayuwar annabawa irin su Ibrahim da Musa da Isa da annabi Muhammadu (s.a.wa.) zai yi nuni da cewa sun yi fada da gurbacewar al'ummunsu sun kuma sami nasara. A fili ya ke cewa imanin da su ke da shi  mai karfi ne dalilin samun nasararsu akan kafirci, shi ne abinda ya sa mutane su ka rika fusguwa zuwa gare su. Wani kyakkyawan misali na matsayin imani a cikin wannan zamanin shi ne juyin juya halin Musulunci na Iran bisa jagorancin Imam Kumaini (r.a).. Imani mai karfi da al'ummar Iran su ke da shi ya sa su yin nasara akan sarauta da kuma yan mulkin mallaka. Hatta a cikin shekaru 8 na kallafaffen yaki imanin al'ummar Iran ya fito a fili. Kamar kuma yadda Imani ya ke baiwa mutum karfin guiwa haka nan rashin imani da ubangiji yana raunana mutum. Ubangiji madaukakin sarki a cikin suratu Nahl yana fadin cewa: "Shakka babu  mafi munin dabbobi a wurin Allah su ne kafirai wadanda ba su yi imani ba." Imani yana a matsayin manufa ne wanda ya ke sa mutum ya kai ga kamala. Saboda haka wanda ba shi da imani ba zai iya samun manufar da ta ke tattare da kamala ba wacce zai iya kai wa gare ta. A bisa mahanga ta alkur'ani mai girma, imani bai takaita a cikin yin furuci da kadaicin Allah madaukakin sarki ba. Ya kuma kunshi mika wuya a gare shi. Wadanda imaninsu bai fita daga cikin zuciya zuwa fagen aiki ba yana a matsayin kafiri ne. A cikin suratu Namli aya ta 14 ubangiji madaukakin sarki yana bayyanin Fir'auna da  mutanen a matsayin munafikai. Domin kuwa har a cikin zuciyarsa Fir'auna ya yi imani da mu'ujizojin da ya gani a tare da ananbi Musa amma bai mika kai a gare su ba. A Musulunci, mutumin da zuciyarsa da harshensa ba su da tsarki ana kiransa munafiki. Shi kuwa mutum munafiki yana da ciwo a cikin ruhinsa da kuma tunaninsa. Bala'i mafi girma da  zai iya fadawa al'umma shi ne raba ta da nutsuwa da kuma zama mai fuska biyu. Ya zamana mutane suna fadin wani abu  suna kuma aikata wani abu daban. Rashin imani  na hakika wanda zai tashi daga fagen yarda ta zuci zuwa cikin fagen aiki shi ne ummul-haba'isin jefa al'umma cikin wannan yanayi. Haka nan kuma yana jefa al'umma zama cikin razana da tsoro da fargaba. Daidaikun mutane da ba su da cikakken imani suna aikata kowane irin laifi da fasadi da barna. A cikin kwanakin bayan nan kafafen watsa labarun Amerika su ka dauki labarin wani matashi dan shekaru 22 wanda bude wuta a wata makaranta tare da kashe mutane 28 mafi yawancinsu kananan yara. Kuma shakka babu yaran da su ka ga abinda ya faru za su kasance a cikin yanayin firgita da ban tsoro na tsawon lokaci. Hanyar daukaka tunanin al'umma,  da kuma bunkasa shi,  shi ne imani,  da kuma ilimi da aiki da shi. Saboda haka wajibi ne a watsa ilimin da ake da bukatuwa da shi domin ganin cewa al'umma ta kai ga ci gaba akan tafarkinta na kai wa ga kamala.

Add comment


Security code
Refresh