An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 10 March 2013 19:28

Turkiya: Mafarkin Shiga Tarayyar Turai (2)

Turkiya: Mafarkin Shiga Tarayyar Turai (2)
(2) Turkiya, ta fara kallon yammacin turai a matsayin alkibla ne tun a farkon kafuwarta a yadda ta ke a yanzu a 1923. Ta kuma fara kokarin shiga cikin wannan kungiya ne a aikace a 1953. A wannan shekarar ce aka kulla yarjejeniya ta farko da Turkiyan, akan hade ayyukan jami'an shiga da ficenta da na tarayyar turai, bisa alakawalin cewa a karshe za a shigar da ita cikin kungiyar. Tun daga wancan lokacin ne kuwa shugabannin kasar Turkiya su ke ci gaba da bin diddigin ganin hakan ta faru. Jam'iyyar da ke mulki a Turkiya a yanzu karkashin su Urdugan, ba ta sauya ra'ayinta ba na shigar kasar cikin wannan tarayya. Ta kuma zage wajen ganin cewa an samar da sauye-sauye na siyasa da tattalin arziki da dokoki wadanda za su daidai da na tarayyar turai. Kuma akan haka ne aka  yi tataunawa  a 2005 tsakanin bangarorin biyu. Tsaida ranar bude tattaunawa da kasar Turkiya da Tarayyar Turai ta yi, ya cusa fata mai yawan gaske a tsakanin 'yan siyasar Turkiya da kuma kafafen watsa labarum wannan kasa, bayan tsawon lokacin da haura rabin karni. Jami'iyyar da ta ke mulki a kasar Turkiya tana daukar bude tattaunawar a matsayin wata nasara a siyasarta ta waje. Sai dai a lokaci guda yadda ake samun nawa wajen yin wannan tattaunawa, yana nuni da cewa tarayyar turai din ba ta da nufin shigar da Turkiya a cikinta nan da wasu shekaru kadan masu zuwa. Shakka babu, bude tattaunawar da Turkiya wani ci gaba ne, sai dai kuma a lokaci guda kofofin shigar da ita cikin turai din a rufe su ke. Kuma kasar Turkiya ce kadai aka rufewa wadannan kofofin domin sauran kasashen Balkan da kuma gabacin turai da  su ke son shiga tarayyar an bude musu kofa ba a rufe ba. Kasar Crotia ta fara tattaunawar  neman shiga tarayyar turai ne a lokaci daya da kasar Turkiya. An kuwa kawo karshen tattaunawar tsakanin Crotia da tarayyar ta turai a 2012, za kuma ta zama cikakkiyar memba a  ranar farko ta July na 2013. A cikin shekaru bakwai da su ka gabata, tattaunawa 35 da tarayyar turai ke yi da kasashen da su ke son shigarta, sau daya kadai aka yi da kasar Turkiya. A wasu lokutan tattaunawar tana samun tsaiko ne saboda rashin amincewar wasu kasashe kamar Faransa. Kuma tare da cewa gwamnatin da ta ke mulki yanzu a kasar Turkiya ta gudanar da sauye-sauye ta fuskar tattalin arziki da siyasa da kuma soja da su ka yi daidai da ma'aunin kasashen tarayyar turai, sai dai duk da haka ana nunawa Turkiyan banbanci da wariya, idan aka kwatanta da yadda kungiyar ta ke mu'amala da sauran kasashen da su ke son shigarta. Ga misali kasar Sabia wacce ta ke da matsaloli, amma tuni tarayyar turai ta rattaba hannu da ita akan yarjejeniyar dauke visa ta shiga da fice tsakaninta da kasashen turai. A lokaci guda kuma tarayyar turai din ta ki amincewa da bukatar Turkiya na bude kan iyakoki da shiga da fice ba tare da visa ba. Ta fuskar al'adu da zamantakewa, tarayyar turai na daukar kansa a matsayin wani Kulub na kiristoci.  Idan Turkiya mai mutane miliyan 75 musulmi ta shiga cikinsu za ta kawo cikas ga kasashen Faransa da Jamus wajen zartar da kudurori. Kuma shigar Turkiyan cikin tarayyar zai jefa manufofin Greek cikin hatsari musamman saboda sabani mai zurfi wanda su ke da shi agabar tekun midetraniya da kuma akan Cyprus da Turkiyan da dara gida biyu. Ita kanta Turkiya, duk da  ci gaba na azo a gani da ta ke da shi,  sai dai tana cike da matsaloli na zamantakewa da  na kabilu da kuma tattalin arziki. Matsalar Kurdawa da talaucin da ya ke cikin biranensu masu yawa zai zamarwa tarayyar turai wani nauyi mai girma. Kuma tarayyar turan tana da damuwa akan cewa idan har Turkiya ta zama memba to miliyoyin  turkawa za su yi hijira zuwa cikin kasashen da su ka fi arziki domin yin aiki. Wannan ne ya sa duk da sauye-sauyen da jam'iyya mai mulki ta Su Urdugan ta yi, musamman ma dai kawar da tasirin sojojin a cikin harkokin siyasayar kasar, amma duk da haka tarayyar turai ba su gamsu ba. Turkiya tana da muhimmanci a wurin tarayyar turai, amma duk da haka, tarayyar turai din tana kallon Turkiyan ne da cewa ba ta wuce abokiyar hulda ba wacce ba za a bude mata kofar shiga ciki ba. Za kuma a ci gaba da daukarta a matsayin makwabciya amma ba 'yar gida ba. Shi ne ya sa fiye da rabin karni su ke wasan kura da ita. Kuma shekaru bakwai da  su ka gabata ne aka bude tattaunawar da ita, wacce aka yi sau guda. Idan kuwa har aka ci gaba da tafiya a haka cikin nawa, to shakka babu za dauki wani karnin anan gaba  ba tare da an shigar da ita ba.

Add comment


Security code
Refresh