An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 22 February 2013 19:45

Turkiya: Mafarkin Shiga Tarayyar Turai

Turkiya: Mafarkin Shiga Tarayyar Turai
Turkiya Da Kungiyar Turai: (1) Turkiya, kasa ce wacce ta fuskar siyasa da tattalin arziki da kuma tsaro ta ke da kamanni da kasashe da dama na turai, ta dade tana fatan shiga cikin tarayyar. Pira ministan kasar ta Turkiya Rajab Tayyin Urdugan wanda ya shirya wa jakadu 27 na kasashen kungiyar tarayyar turai liyafar cin abincin dare, a birnin Ankara ya fada musu cewa: " Shekaru 34 kenan Turkiya ta ke tsumayen ranar da za a shigar da ita cikin tarayyar turai, amma a fili ya ke cewa tattaunawar da ake yi dangane da hakan ta dau salo na siyasa, wanda kuma a cikin shekaru biyu na bayan nan ya dau wani salo na siyasa." Kuma a yayin tafiye-tafiyen da ya yi zuwa kasashe uku na tarayyar turai, pira ministan na kasar Turkiya ya yi suka da kakkausar murya akan tarayyar turai din. A birnin Prag ya fadi cewa; "Shekaru 54 sun shude daga lokacin da Turkiya ta fara kokarin shiga cikin tarayyar turai, sai dai maimakon ace an gabatar da dalilin da zai hana a shigar da ita, sai yawo ake yi da hankalinta." Pira ministan na Turkiya ya bayyana cewa shigar Turkiya cikin tarayyar turai din zai amfani tarayyar ne, sannan kuma ya kara da cewa; " Har yanzu Turkiya tana son shiga cikin tarayyar turai, sai dai jinkirin da ake yi wajen karbar ta, ba abu ne wanda za a kau da kai daga gare shi ba." Hawa kan karagar mulki da masu ra'ayin gurguzu a tarayyar turai su ka yi, ya sa kasar Turkiyan samun Karin fata na cewa za ta shiga trayyar. Domin kuwa shugaban kasar Faransa da ya sauka, Nicholay Sarkozy, ya dauki tsauraran matakan da su ka kawo cikas wajen shigar Turkiya cikin tarayyar ta turai. A daya daga cikin maganganunsa, Sarkozy ya ce; tunaninsa ba zai taba kama cewa wata rana za ta zo ba tarayyar turai za ta yi iyaka da kasashen Iran da Iraki da Syria. Wasu daga cikin shugabannin kasashen tarayyar turai masu ra'ayin mazan jiya kamar Angela Markel ta Jamus, sun goyi bayan matsayin Sarkozy akan Turkiya. Gwamnatin Turkiya ta yanzu, musaman ma dai ministanta na harkokin waje, Ahmad Daud Uglu,  wanda kuma shi ne injiniyan siyasar wajen kasar, sun yi imani da cewa masu ra'ayin kawo sauyi 'yan gurguzu a kasar Faransa daa su ka hau mulki, za su taimaka wajen sake dawowar tattaunawa da Turkiya akan shigarta tarayyar turai. A yayin tafiyarsa ta bayan nan zuwa kasar Faransa, Ahmad Uglu, bayan ganawarsa da takwaransa na Faransa Lauran Pavios, ya gudanar da taron manema labaru da a ciki ya bayyana cewa; " Ina zaton cewa sannu a hankali kasar Faransa za ta sauya matsayinta na nuna adawa." Shi ma ministan harkokin wajen Faransa Lauran Favious ya fadi cewa; " Baya ga tattauna alaka ta tsakanin kasashenmu biyu, mun kuma yi magana dangane da tarayyar turai tare da Turkiya. Na kuma jaddada cewa wajibi ne a fara tattaunawa akan shigar Turkiyar cikin tarayyar turai din, wacce  ta ke kunshe da kaso 22. Kuma za ta fara ne daga kan siyasar yanki" ***** Gwamnatin Turkiya ta dauki sani salon siyasa wanda zai kufula tarayyar Turai saboda muhimmancinsa a siyasance, ya kuma sanya tarayyar yin tunanin jawo Turkiyan a cikinta. Wannan siyasar kuwa ita ce yadda Pira ministan kasar Rajab Urdugan ya yi magana akan sha'awar kasarsa na zama memba a cikin kungiyar nan ta Shanghai. Ita kuwa wannan kungiyar an kafa ne domin ta kalubalanci kungiyar yarjejeniyar tsaro ta  Nato da kuma tasirin Amerika da tarayyar turai. A taron karshe da aka yi na wannan kungiyar a Beijin na kasar Sin, Turkiya ta halarta, kuma  an karbe ta a matsayin abokiyar tattaunawa. Kodayake dai abokiyar tattaunawar da aka karbi Turkiya a cikin wannan kungiya shi ne matsayi na bayan baya a cikin kungiyar, kuma ba zai ba ta damar halartar tarukan sirri ba. Sai dai duk da haka Turkiyan tana hankoron samun mukamin 'yar kallo a cikin wannan kungiya. Yin dubi ga manufar wannan kungiya ta Shanghai, zai sai Turkiya ta shiga tsaka mai wuya ta fuskokin siyasa da tsaro domin kuwa har yanzu memba ce a cikin kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato. Domin kuwa kasashen Rasha da Sin, da su ne ginshikin kafuwar kungiyar Shanghai, suna da sabani da kasar Turkiya akan girke na'urori masu kakkabo makamai mai linzami na kungiyar Nato a cikin kasar Turkiyan. Sun kuma raba hannun riga da ita akan siyasarta a cikin kasashen Syria da Iraki. Adalilin haka, a cikin sani Turkiya ta kusaci kungiyar shanghai, domin ta sa Amerika ta yi wa turai matsayin lamba a karbe ta a matsayin memba. Yana da ci gaba....

Add comment


Security code
Refresh