An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 16 February 2013 19:20

Yadda Kasashen Yammacin Turawa Su ke Sauya Ma'anoni Masu kima

Yadda Kasashen Yammacin Turawa Su ke Sauya Ma'anoni Masu kima
Babu wani lokaci a tsawon tarihin bil'adama da aka rika amfani da ma'anoni na jin kai da kare hakkin bil'adama kamar a wannan zamanin da mu ke ciki. Sai dai a lokaci guda wadannan ma'anonin sun zama makami da manyan kasashe masu takama da karfi ke amfani da su domin su yi wa siyasarsu da kuma manufofinsu saiti. Daya daga cikin ma'aunin ci gaba kasashe shi ne girmama hakkin bil'adama a cikin dukkanin fuskokinsa. Su kuwa kafafen watsa labaru masu karfi suna amfani da su domin sauyawa mutane tunani da yi musu cushen abinda ba shi ne gaskiya ba. Tare da cewa tarihinsu a cike ya ke da take hakkin bil'adama da cin zarafinsa, sun maida kansu masu kare wannan hakkin a wannan lokacin a duniya. Su ke kuma baiwa kawukansu hakki da iko akan tsoma baki a cikin kasashen da su ka ga dama da sunan kare hakkin bil'adama. Tsarin jahmuriyar Musulunci a tsawon shekaru 34 na rayuwarsa ya zama wanda kasashen yamma su ke kai wa bara ta hanyar fakewa da batun kare hakkin bil'adama. Bai kuma zama abin mamaki ba domin kuwa wadannan kasashen su ne su ka rika bada kariya ga tsarin sarautar dan kama-karya na Muhammad Riza Pahlawi. Al'ummar Iran bisa jagorancin marigayi Imam Khumaini (r.a) sun yunkura domin yin juyin juya hali wanda ya kai ga kifar da gwamnatin Sha. Wannan juyin ya zama masomin ani gagarumin yunkuri na al'umma a duniya. Sai dai duk da haka, kasashen yammacin turai din suna bugun kirji da cewa su ne masu kare hakkin bil'adama a duniya, alhali su da Amerika babu wata kutunguila wacce ba su kitsawa juyin Musulunci na al'ummar Iran ba ta fuskar siyasa da tattalin arziki da al'adu da zummar kifar da shi. Ba kuma su yi la'akari da ra'ayin al'umma ba na cewa su ne su ka yi juyi kuma su ka kada kuri'ar zabarsa. Yawan bijiro da sunan jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen turai bisa jagorancin Amerikan su ke yi a cikin cibiyoyin kasa da kasa, manufarsa guda daya tilo ita ce samun damar da za su shimfida ikonsu a cikin wannan yankin. Yunkuri na karshe da wadannan irin kasashen suna yi shi ne gabatar da daftarin kuduri da kasar Canada ta yi a gaban  majalisar dinkin duniya a ranar 27 ga wtan nuwamba. Kwamitin da Canada din ta gabatar da batun a gabansa wanda ak kira da kwamiti na uku yana daya daga cikin kwamitoci shidda da su ke tattauna batutuwa daban-daban na musamman kamar kare hakkin bil'adama da fada da wariya a ko'ina su ke a duniya. Sai dai abin takaici ne cewa kwamitin na ukuu da ke karkashin babban zauren majalisar dinkin duniya ya zama wani fage wanda kasashen yammacin turai su ka yi tasiri a cikinsa. Suna amfani da shi domin ganin cewa sun aiwatar da siyasarsu a cikin duniya. Saboda haka daftarin kudurin da aka gabatarwa da kwamitin akan Jamhuriyar Musulunci ta Iran yana da alaka ne da tasirin kasashen yammacin turai da Amerika. Wannan shi ne abinda ya ke raunana matsayin majalisar dinkin duniya da ayyukan da ta ke gudanarwa. Muhammad Kahza'i wanda shi ne jakadan Iran a majalisar dinkin duniya ya gabatar da jawabi da a ciki ya yi bayani akan rawar da Canada ta ke takawa wajen ta ke hakkin bil'adama. Ya kuma bayyana matakin na kasar Canada da sauran kasashen turai wajen shigar da siyasa a cikin duk wani batu da za su gabatar da ya shafi batun take hakkin bil'adama. Malam Khaza'i ya kuma zargi kasashe da rufe idanunsu akan abubuwan da su ke faruwa a cikin wannan yankin na gabas ta tsakiya musamman a cikin kasashen Bahrain da Jordan da Saudiyya da take hakkin bil'adama ya zama ruwan dare. A cikin kasashen Saudiyya da Bahrain gwamnatoci ne na bangaranci su ke mulki ta hanya mafi mufi da ba su daidai da duk wani mizani na mulki a wannan zamanin ba. Sai dai alokaci guda wadannan kasashen basu da masu basu kariya da su ka kai kasashen turai da Amerika. ***** Shekaru biyu sun shude fara yunkurin al'umma a arewacin Afrika zuwa kasashen larabawan yankin tekun pasha. Wannan guguwar ta kifar da gwamnatocin 'yan kama-karya na Masar da Tunisiya da Libya wadanda a baya kasashen na yammacin turai da Amerika ne su ke basu kariya. Kuma kasashen na turai ba su taba furta kalmar tir da yadda kawayen nasu su ke take hakkin bil'adama ba a tsawon lokacin da su ke kan karagar mulki. Sai da su ka tabbatar da cewa za su fadi ne sannan su ka fara nuna goyon bayansu ga yunkurin al'umma. Jakadan jamhuriyar Musulunci ta Iran a majalisar dinkin duniya, ya yi cikakken bayani akan yadda kasashen na turai da Canada da Amerika su ke take hakkin bil'adama akan 'yan gudun hijira da kuma musulmin da su ke rayuwa a cikinsu. Karuwar kin jinin Musulunci da kai wa masu zanga-zanga da gangami na lumana da sulki hari acikin kasashensu suna a matsayin karamin misali ne na take hakkin bil'adama. Har ila yau, Muhammad khaza'i ya yi ishara da yadda a cikin kasar Amerika ake takurawa bakaken fata da hana su hakkokinsu. Ko kuma yadda Amerikan da kawayenta su ke kashe mutane a cikin kasashen Afghanistan da Yamen da Pakistan. Da sunan shimfida tsarin demokradiyya ne Amerika ta kashe dubban mutanen kasar Iraki. Haka nan kuma cikakken goyon bayan da ta ke baiwa h.k. Isra'ila da ta ke yi wa palasdinawa kisan gilla. A takaice a wannan lokacin kasashen yammacin turai suna kokarin nunawa duniya cewa sun kai koli wajen kare hakkin bil'adama saboda haka su ke baiwa kansu hakkin tsoma baki a cikin duk wata kasa da su ka ga dama da wannan suna. Sai dai a hakikanin gaskiya ba kare hakkin bil'adama ne ya dame su ba, abinda ya ke gabansu shi ne yadda za su yi amfani da wannan batu mai dadin suna domin shimfida ikonsu a cikin kasashen duniya.

Add comment


Security code
Refresh