An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Thursday, 09 August 2012 08:22

Rayuwar Roger Graudi

Rayuwar Roger Graudi
Mun fara bada tarihin rayuwa Roger Garaudi daga haihuwa da fadi tashin da ya yi a fagen siyasar kasar. Haka nan kuma mun ji yadda neman gaskiya ya zamar masa mizanin da ya ke tafiya akansa wanda shi ne ya kai shi ga shiga jam'iyyar gurguzun kasar har ya kai ga samun mukamai da su ka hada da shugabancin cibiyar nazari da bincike. Hatta a lokacin da ya ke dan majalisar dokoki da kuma majalisar dattijai bai yi watsi da bincike na ilimi ba saboda neman gaskiya. Tare da cewa ya rungumi akidar gurguzu sai dai ya ci gaba da neman gaskiya ta addini. Wannan ne ya kai shi ga kokarin kusanto da akidar gurguzu da kuma addini a wani littafi da ya rubuta. Sai dai shigar da sojojin tarayyar Soviet su ka yi a cikin kasar Chekoslovakia ya dagula masa lissafi ya sa shi dawowa daga rakiyar wannan akidar ta siyasa. A zatonsa gurguzu yana son 'yanto da mutane ne ba bautar da su ba. Ya sake rungumar addinin kiristanci amma kuma duk da haka ya ci gaba da bincike, a karshi ya yi watsi da shi saboda yadda ta bankado tarihi ya gano cewa da sunan gicciye, aka yi wa mutanen birnin Qudus kiyashi  haka nan kuma mutane Qustantine.  An kuma yi wa 'yan asalin amurka kisan kiyashi da sunan kiristanci. Roger Garaudi ya kai ga cimma sakamakon cewa mabiya addinin kiristanci da aka gurbata ne su ka yi wa duniya mulkin mallaka sun kuma fake da sunan shimfida adalci da yanci wajen kafa ikonsu a kan al'ummu. Wannan ne ya sa shi juya wa kiristanci baya, ya kuma rubuta littafi mai suna: "Gargadi Ga Rayayyun Mutane." To masu sauraro za mu dasa daga inda mu ka tsaya, da fatan za a kasance a tare da mu domin a ji shirin kamar yadda zai gudana. Bayan dawowa daga rakiyar addinin kiristanci da Roger Garaudi ya yi saboda sakamakon da ya cimmawa ta hanyar nazari da bincikensa, ya maida hankali wajen yin nazari akan sauran addinai da su ka hada musulunci da Hindu da Buddha da yahudanci da Zartusht. A karshe kuwa ya gano wannan gaskiyar a tare da musulunci. A shekarar 1982 ya yi kalmar shahada. Garaudi wanda ya taba kawo ziyara Iran ya bayyana cewa: " Na zabi musulunci ne saboda shi ne addini cikakke wanda kuma ya ke fada da zalunci." Bayan musuluntarsa ya fara gudanar da nazari akan hakikanin abinda ya faru da yahudawa na kisan da Htler ya yi musu da kuma hakikanin sahayoniya. Bayan da ya tattara bayanai masu kima ya fitar da wani littafi wanda ya kira da sunan: Almarar wadanda su ka kafa Isra'ila" a 1995. Littafin ya fuskanci suka daga 'yan sahayoniya da masu yi musu rakiya. A 1997 wata cibiyar buga littatafai ta larabawa ta dauki

Add comment


Security code
Refresh