An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Friday, 15 June 2012 19:21

Ranar 'Yanto Da Garin Kurramshahr

Ranar 'Yanto Da Garin Kurramshahr
Ranar uku da watan Khurdad na shekarar hijira shamshiyya ta 1361 wacce ta yi daidai da watan mayu na 1982 miladiyya, tana daga cikin muhimman ranakun tarihin juyin musulunci a Iran. Rana ce wacce al'ummar Iran su ka yi imani da cewa tana daga cikin fiattun taimakon da su ka samu daga Ubangiji a fadansu da masu wuce gona da iri. A wannan ranar ce garin Khurramshahr da ke kudu maso yammacin Iran dakarun musulunci su ka yi nasarar sake kwace shi daga hannun sojojin wuce gona da iri na Iraki bayan tsawon watanni 20 da mamaye shi. A cikin gaggawa labarin sake kwato wannan garin ya watsu a cikin Iran wanda ya haddasa farin ciki da murna. Al'ummar Iran a cikin birane daban-daban sun shiga masallatai domin yin salla ta nuna godiya ga ubangiji sun kuma rika bada kabbarori a cikin gari.Farmakin da aka kai na kwato garin Kurramshahr mai suna: Baitulmuqaddas yana kunshe da matakai guda hudu wanda ya kare da shiga cikinsa da kuma yi wa sojojin ba'asiyya asara mai yawan gaske.Saddam wanda ya ke da goyon baya da kariya daga yammacin turai da kuma kasashen larabwa ya za ci cewa zai iya kawo karshen juyin musulunci wanda a wancan lokacin ya ke jariri. Yakin wanda Saddam ya fara shi da zummar cewa ba zai wuce kwanaki uku ne, ya dauki tsawon shekaru takwas ana yinsa. Al'ummar Iran manya da kanana sun zage damtse wajen kare kasarsu da hana masu wuce gona da iri cimma manufarsu. Yakin ya shiga cikin tarihi da cewa shi ne mafi tsawo a tsakanin yake-yaken da aka yi a karni na 20. Wannan yakin ya kebanta da wasu abubuwa wadanda sauran yake-yaken da aka yi a duniya ba su da shi.Tsayin dakar da al'ummar Iran su ka yi a tsawon lokacin kallafaffen yaki, wani abu ne wanda ya fi karfin siffauwa. Sojojin Ba'asiyya na Iraki sun mamayi garin Khurramshahr ne a lokacin da mazaunansa ba su cikin shirin domin kuwa ya zo musu ne bisa ba za to. Imanin da su ke da shi ne ya zamar musu makami da kuma kishi da son da su ke yi wa kasarsu. Sun fito kwansu da kwarkwatarsu domin kare kasa da al'ummarsu. Masana dabarun yaki da siyasa sun yi imani da cewa kuskure mafi girma da Saddam ya yi shi ne kallon karfin makami da goyon baya daga al'ummun duniya da ya ke da su, ya dauka cewa sun isa ba shi nasara. Ya jahilci rawar da imani ya ke takawa wajen murkushe duk wani mai takama da karfi."Yantar da garin Kurramshahr shi ne nasara mafi girma wacce tsarin musulunci ya samu tun bayan cin nasarar juyi a Iran. Kuma shi ne nasara mafi girma ta fuskar soja wacce iran din ta gani a cikin shekaru 150 da su ka gabata. Baya ga baiwa al'ummar Iran jin daukaka da girma ya kuma bada mamaki ga sauran kasashe. Sojojin Saddam wadanda suna da yawa na azo a gani da kuma samun goyon baya daga manyan kasashe ta fuskar soja da siyasa, sai dai duk da haka sun sha kashi a hannun dakarun musulunci na Iran. A ranar da aka 'yanto da Khurramshahr Jagoran juyin musulunci Imam Khumain (r.a) ya fitar da bayani wanda a cikin ya taya al'ummar Iran murna da kuma yi musu godiya akan kwazon da su ka nuna. Ya kuma bayyana cewa:" Murna ga al'ummar Iran wadanda su ka sadaukar da kawukansu, murna mai girma ga musulunci wanda ya yi nasara akan makiya na fake da sarari.""Yanto da garin Khurramshahr ya fuskanci maida martani daga kasashe da kungiyoyin duniya, domin kuwa ya fito da fifikon da sojojin Iran su ke da shi akan na Iraki a filin daga da kuma a fagen siyasa. Yaki ne wanda masominsa shi ne kifar da juyin muuslunci da kuma yanke wani sashe na Iran, ya kara hade kan al'ummar Iran wuri guda da maida su tsintsiya madaurinki daya. A lokacin da mayakan Iran din su ka sake kwato garin na Khurramshahr kafafen watsa labarun duniya sun yi shiru na tsawon sa'oi 24, babu wani labari da kafafen watsa labarun yammacin turai su ka dauka dangane da shi. Sai dai a karshe ya zama babu makawa sai sun dauki labarun ba domin sun so ba. Kwanaki biyu bayan 'yanto da garin ne, radoyon gwamnatin Ingila ya watsa labarin cikin mamaki da cewa:" A lokacin da kafafen watsa labarun yammacin turai su ka ziyarci garin Khurramshahr sun sami sojojin Iraki cikin karfin guiwa, sai dai kwanaki uku zuwa hudu da su ka shude sojojin Irakin sun fice daga birnin."Yakin kare kai wani wajabci ne na addini da kuma kasa wanda ya hau wuyan dukkanin al'umma. Ubangiji madaukakin sarki a cikin aya ta 39 zuwa 40 a Suratul Haj yana fadin cewa:" An yi izini ga wadanda ake yaka da cewa an zalunce su kuma Allah mai iko ne akan taimakonsu. Wadanda aka fitar da su daga gidajensu ba tare da hakki ba sai saboda sun ce Allah ne ubangijinmu."Wannan alkawalin na Allah ya fito fili a cikin yakin Iran da Iraki na tsawon shekaru takwas. An zalunci al'ummar Iran saboda kare hakkokinsu da kuma tsayin daka kan manufofinsu, amma Allah ya taimaka musu su ka yi galaba akan makiyansu.Tsarin dakar da al'ummar Iran su ka yi a tsawon lokaci yaki da ya hada da kokarin kwato da 'yanto birnin Khurramshahr, yana daga cikin shafuka mafi haske wajen cin nasara. Al'ummar Iran sun yi tsayin daka a tsawon wannan lokacin da matsaloli su ka yi musu yawa. A wannan lokacin ma al'ummar Iran na ci gaba da kare juyinsu da manufofinsa cikin ruhi irin wancan abinda ya sa su ci gaba ta fuskokin ilimi da kere-kere. Dukkanin duniya ta yi furuci da cewa Iran da ta ke fuskantar takunkumi daga yammacin turai ta zage damtse wajen gina kanta kuma tana ganin haske. A yau an wayi gari cewa iran din tana cikin jerin kasashe goma wadanda su ke samun ci gaba a wasu fagage na ilimi a duniya.Muhimmancin 'yanto da garin Khurramshahr bai takaita a cikin kwato wani yanki na kasa ba, ya kuma kunshi yin riko da manufofin juyi da kuma kafa kyakkyawan misali, kamar yadda jagoran juyin musulunci ya bayyana. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei da ya ke magana akan zagayowar 'yanto da wannan birnin ya ce:" Fasaha mafi girma wacce al'ummar Iran su ka nuna a wajen fuskantar harin masu wuce gona da iri a garin Khurramshahr shi ne tsayin daka mara tamka da al'ummar Iran din su ka nuna. Domin kuma mutanen wannan birnin maza da mata da manya da kanana sun fito cikin kumaji wanda ya maida Khurramshahr a matsayin abin koyi na kowane lokaci. Makiyanmu sun ganewa idanunsu nasarar da mu ka samu a cikin Khurramshahr da kuma sauran garuruwa sun kuma fahimci cewa wannan al'umma wacce ta yi nasara a cikin fagen yaki tana mai dauke da tutar musulunci, to za ta iya yin nasara a cikin sauran fagage. Wannan ne ya sa su ka yi kokarin sauke wannan tutar da su ke rike da ita a kasa. A wannan lokacin dukkanin kokarin Amurka da masu girman kai na duniya shi ne su raba raba mu da karfin gwagwarmaya da tsayin daka. Wato suna son raba mu da dogaro da kai da gaskata kanmu da mu ka yi da kuma imaninmu."Shekaru masu yawa sun shude daga sake kwato garin Khurramshahr amma har yanzu al'ummar Iran suna tuna shi da jin alfahari. An kuma baiwa wannan rana sunan, ranar gwagwarmaya da samun nasara. Domin kuwa a wannan ranar ce su ka tabbatar wa da duniya cewa babu wani ma'abocin karfi wanda zai iya wuce gona da iri akan kasarsu su kyale shi.

Add comment


Security code
Refresh