An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 20 May 2012 02:27

Rawar Da Imani Na Addini Ya ke Takawa. (2)

Normal 0 false false false EN-US X-NONE FA MicrosoftInternetExplorer4 /* Style Definitions */ table.MsoNormalTable {mso-style-name:"Table Normal"; mso-tstyle-rowband-size:0; mso-tstyle-colband-size:0; mso-style-noshow:yes; mso-style-priority:99; mso-style-qformat:yes; mso-style-parent:""; mso-padding-alt:0cm 5.4pt 0cm 5.4pt; mso-para-margin:0cm; mso-para-margin-bottom:.0001pt; mso-pagination:widow-orphan; font-size:11.0pt; font-family:"Calibri","sans-serif"; mso-ascii-font-family:Calibri; mso-ascii-theme-font:minor-latin; mso-fareast-font-family:"Times New Roman"; mso-fareast-theme-font:minor-fareast; mso-hansi-font-family:Calibri; mso-hansi-theme-font:minor-latin; mso-bidi-font-family:Arial; mso-bidi-theme-font:minor-bidi;} Imani mai karfi da riko da addini suna baiwa mutum karfin tsayin daka wajen jurewa fadawa cikin laifuka. Ma'abocin tunani kuma malamin addini shahid Murtadha Mutahhari yana fadin cewa: " Gwargwadon yadda Imanin mutum ya ke da karfi, zai zama mai rika tuna Allah, kuma gwargwadon yadda mutum ya ke tuna Allah, ya ke rage aikata sabo. Ana yin ibada ne domin a tuna Allah domin ya zama mai riko da kyawawan halaye." Imani da Ubangiji da ranar kiyama suna daga cikin abubuwan da musulunci ya gindaya a matsayin abubuwan da su ke hana mutum aikata laifi. Ma'anar imani anan shi ne jin cewa Allah shi ne mamallakin mutum da duniya kuma makadaicin abin bauta kuma mai ji ne mai gani. Mutum ma'abocin imani a kodayaushe yana sanya Allah a idanunsa. Duniya a idon mutum ma'abocin imani ba a sandare ta ke ba kuma ba haka kara zube ta ke tafiya ba, wani tsari ne wanda da ma'ana da manufa. Mutumin da ya ke sanya Allah a zuciya da idanunsa, ba zai rika jin cewa yana rayuwa haka nan ba tare da manufa ba. Yin imani da Allah yana sanya zama mai kyakkyawan fata a kodayaushe a rayuwarsa, ya ke kuma ingiza shi ya yi aikin kwarai ya kuma nesanci munanan ayyuka. Yin imani da Allah ya yi kama da bishiya wacce ta ke tsirowa a cikin ruhin masu shi. Tana kuma fitar da tsiro mai kyawu wanda shi ne kyawawan ayyuka. Sakamakon yin imani da Allah kuwa shi ne yin gaskiya da adalci da tsarkin zuciya da sadaukar da kai. Wadannan kuma siffofi ne da su ke nuni da cewa ruhin mai su yana cikin koshin lafiya da kuma daidaito. Tuna Allah, wata bukata ce da mutum ya ke da shi bisa fidira. Idan kuwa mutum ya kau da kai daga wannan kiran na fidirar, to zai fada cikin rayuwa mai cin karo da juna. Kuma zai zama mai share fagen aikata laifuka da sabo. Saboda haka imani na hakika yana a matsayin wata wadatuwa ce ga mutum da ke gamsar da mutum da hana shi aikata laifi. Imani da ranar kiyama wacce ita ce ta sakamako wata ce daga cikin hanyoyin samun kariya. Ma'anar yin imani da ranar kiyama kuwa shi ne yarda da cewa mutane bayan mutumwa za su sake rayuwa bisa umarnin ubangiji za kuma a yi musu hukunci akan abubuwan da su ka aikata a duniya. A ranar kiyama mutane za su ga sakamakon ayyukansu masu kyau da munana. Marigayi Allamah Taba'-Tabei wanda malamin tafsiri ne kuma masanin falsafa yana fadin cewa: " Mutumin da ya yi imani da ranar kiyama yana sane da cewa ubangiji yana da masaniya akan dukkanin ayyukan da ya ke yi. Yana kuma sace da cewa wata rana za ta zo wacce za a baje kolin dukkanin abinda ya aikata daya bayan daya a yi masa hisabi akansu. Wannan abinda mutum ya ke ji a cikin zuciyarsa ya fi tasiri akan dubban jami'an tsaro da 'yan sanda. Domin kuwa dukkaninsu suna aiki ne daga waje, alhali imani yana a matsayin mai sanya idanu ne daga cikin zuciyar mutum." Idan mutum ya yi imani da ranar lahira kuma ya ke jin cewa ubangiji yana ganinsa to zai zama mai sanya idanu akan ayyukan da su ke bijirowa daga gare shi, saboda haka ba zai zama yana da bukatuwa da 'yan sanda da jami'an tsaron da za su rika sanya idanu akansa ba. Kuma a kodayaushe ayyukansa na zahiri da boye za su zama suna tafiya daidai wa daida. A musulunci, ayyukan ibadar da mutum ya ke yi suna amatsayin abubuwan da su ke hana shi aikata laifi. Ayyukan farilla irin su salla da azumi da zakka da haji da kumusi da zakka da umarni da kyawawan halaye da hani da munanan ayyuka suna takawa mutum birki ya nesanci munanan ayyuka. A cikin suratu Ankabuti aya ta 45 muna karanta cewa: " Ka karanta abinda kae yo maka wahayinsa na kur'ani, ka tsaida salla, domin salla tana hana yin hani daga alfahasha da mummuna, sai dai ambaton Allah shi ne mafi girma, kuma Allah yana sane da abinda ku ke aikatawa." A cikin kur'ani da kuma hadisan annabi da Ahlul-Baiti (a.s) an mabaci matsayi kwatankwacin wannan dangane da azumi da haji. Kumusi da zakka suna daga cikin ayyukan ibada da kowanensu yana da tasiri na musamman ga mutum a cikin rayuwarsa ta duniya da kuma tsarkake ruhinsa da daukaka shi. Umarni da kyawawan ayyuka da kuma hani da munana da su ka zo a cikin musulunci, yana kira ne ga mutanen kwarai da su zama mai sanya idanu akan al'umma ta ke tafiya da hana masu laifi yin ta'asa a cikin al'umma. Baya ga tasirin da wani sashe na ayyukan ibada ya ke yi a ruhin mutum da tunaninsa, yana kuma da tasiri a cikin al'umma baki daya. Ga misali bada zakka da kudin kumusi da kuma ciyarwa ta mustahabbi da wakafi za su iya magance wasu bukatu a cikin al'umma,idan har an raba su ta hanyar da ta dace. Biyawa mutane bukatunsu kuwa yana taka gagarumar rawa wajen yin maganin aikata laifuka. Sai dai duk da haka bai kamata a kau da kai daga rawar da hukuma za ta taka ba a wannan fagen. Domin kuwa nauyi ne da ya ratya a wuyan hukuma ta dauki matakan warware matsalolin al'umma, da kuma biya musu bukatun da za su hana su aikata laifi. A jumlace za a iya cewa, addini da riko da shi shi ne hanya mafi karfi wajen samar da daidaito ga daidaikun mutane da kuma al'umma. Kuma kandagarko mai karfi na hana afkuwar laifuka.

Add comment


Security code
Refresh