An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Sunday, 20 May 2012 02:24

Rawar Da Imani Na Addini Ya ke Takawa.

  Watakila zai yi kyau mu bude wannan shirin da wata shahararriyar maganar marubucin kirkirarrun labarum nan dan kasar Rasha, wato Fyodor Destoevsky da ya ke cewa:" Idan mu ka cire imani da Ubangiji a cikin al'umma, to babu abinda ba za a aikata ba."Tarihin bil'adama a doron kasa yana nuni da cewa aikata laifi wani sashe ne na rayuwar zamantakewa. Wannan ne ya sa a kodayaushe mutane su ke neman sanin dalilin da ya sa ake aikata laifi da kuma gano yadda za a hana afkuwarsa. Addinai ma suna bada muhimmanci wajen shimfida hanyoyin hana afkuwar lafukan. Kasantuwar musulunci addini na karshe da ya zo daga ubangiji, yana da bakin fada a cikin kowane bangare na rayuwar mutum. Ya kuma shimfida hanyoyin da idan aka bi su, za a magance afkuwar da dama daga cikin laifuka.Sanannen abu ne cewa dukkanin addinai da mazhabobi suna kiran mutane zuwa ga ayyukan kwarai aduniya. A bisa mahanga ta falfasa, aiko da annabawa da manzanni da kuma saukar wahayi, manufarsu ita ce, tseratar da mutum daga fadawa cikin ayyukan kaskanci ta fuskar kyawawan halaye da kuma karfafa su da yin ayyukan kwarai. Ma'anar addini shi ne gungu na umarni da dokoki da Allah ya aiko annabawa da manzanni da su domin su dora mutane akansu. Dokokin addinin suna da bangarori guda uku: Na farko shi ne bangaren yin imani da wasu abubuwa sai na biyu kyawawan halaye sai na uku hukunce-hukunce da daidaikun mutane da kuma al'umma za su tafiyar da rayuwarsu akansu.Dangane da yadda wannan gungun koyarwar su ke taka rawa wajen hana afkuwar laifuka, za a iya kafa dalili da cewa idan har hankali da kuma lamiri na mutum sun iya taka rawa wajen hana shi aikata laifi, to shakka babu yin imani na gaskiya da addini da dukkanin abinda ya kunsa na bangarori uku da mu ka yi Magana akansu, su ne garkuwa mafi tasiri wajen hana afkuwar laifuka da karkacewa. Gwargwadon yadda dokoki da tsare-tsare su ka ginu bisa adalci, to za su taka rawa wajen hana afkuwar laifukan. Ta hanyar kyawawan halaye za a iya shaga tsakanin mutum da aikata laifi fiye da wani abu waninsa. Masana ilimin zamantakewa da masu kula da harkokin tarbiyya suna bada kima ga rawar da addini ya ke takawa wajen yin afkuwar laifuka. Koyarwar addini tana kiran mutum ne zuwa ga kyawawan halaye da nesantar gurbatattun ayyuka. Edwid Sutherland wanda kwararre ne a fagen sani manyan laifuka dan kasar Amurka ya yi imani da cewa addini ya zo ne domin ya cusawa mutane kyawawan halaye da kuma nesanta su daga aikata laifuka.Sayydi Mustafa Muhsal Hamdani wanda masanin dokoki ne dan kasar Iran, yana fadin cewa: " A bisa mahanga ta mafi rinjayen masana laifuka- criminology- riko da addini yana taka rawa mai girma wajen hana afkuwar laifi. Kyakkyawan sanin addini da kuma imani mai karfi da kuma aiki da dokokin ubangiji da sun zo ne domin samar da daidaito a cikin hankali da tunanin mutum. Za su hana shi fadawa cikin aikata laifuka.Da dama daga cikin manazarta sun maida hankali wajen yin nazari da bincike da yadda ake samun karancin aikata laifuka a tsakanin daidaikun mutane da kuma jama'a da su ke riko da addini.Haka nan kuma nazarin masana a cibiyoyin bincike yana nuni da cewa tarukan addini da ake gudanarwa suna da tasiri akan ruhin daidaikun mutane. A cikin watan azumin Ramadana ga misali halayen mutane suna sauyawa wanda kuma tasirnsa ya ke kasancewa a tare da su har zuwa bayan azumin. Kuma nazari ya tabbatar da cewa gwargwadon yadda mutane su ke riko da addini ne su ke samun kariya da kuma iya jurewa aikata laifuka.Ilimin zamantakewa na addini yana daga cikin hanyoyi mafi dacewa wajen tafiyar da rayuwar al'umma da kawar da munanan abubuwan da ba su dace ba a cikinta. Domin riko da addini yana zamarwa mutum kandakarko akan karkacewa sannan kuma ya maida mutum ya zama mai sanya idanu akan ayyukansa da kansa, mai makon jami'an tsaro da masu kayan sarki.Malam Talibani yana daga cikin masu yin nazari akan alakar da ke tsakanin riko da addini da kuma halayya ta matasa. Ya kuma fito da wani sakamako da ke nuni da cewa hakan yana matasan aikata laifuka. Tasirin addini akan matasa yana nesanta su daga fadawa cikin munanan halaye.Har ila yau nazari da bincike yana nuni da cewa mafi yawancin masu aikata manyan laifuka mutane ne wadanda sun nesanta daga addini da aiki da shi. Rashin daidaito a cikin ruhi da kuma tunani su ne ummul haba'isin da su ke ingiza mutane aikata manyan laifuka kamar yadda ilimin laifuka ya ke nunawa. Masu aikata laifuka su ne mutanen da sun kasa samun mafita daga matsalolin rayu ta hanyoyin da su ka dace da hankali da kyakkyawan tunani. Ta hanyar nazari mai zurfi akan tushen laifukan da daidaiku ko kuma kungiyoyi su ke aikatawa za a iya fahimtar cewa da akwai rashin daidaito a cikin tunani da ruhi na masu karya dokoki da kuma aikata laifuka.Yin nazari akan koyarwar musulunci zai sa a fahimci cewa duk wani abu da ya yi umarni da a aikata shi, ko kuma ya yi hani da shi, suna taka rawa wajen baiwa mutum lafiya ta ruhi da tunani da kuma gangar jiki. Mai riko da addini yana da karancin fadawa cikin fushi wanda zai raba shi da hankali da tunaninsa ko ya ingiza shi ya aikata abinda bai dace ba. Kuma matsala ko mai girmanta ba ta sa shi ya rude yana ci gaba da zama cikin nutsuwa. Wannan irin halayyar kuwa ita ce mafi tasiri wajen hana aikata laifi. Da yardar Allah za mu ci gaba da bayani akan tasirin akidojin addini wajen hana aikata laifuka.  

Add comment


Security code
Refresh