An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Wednesday, 07 March 2012 07:50

Amsa Kiran Tauhidi Daga Bakin Sean Stone.

Amsa Kiran Tauhidi Daga Bakin Sean Stone.
Sean Ali Stone ya fadi cewa: " A cikin addinin musulunci da akwai alaka ta kai tsaye a tsakanin Ubangiji da Mutum wanda hakan wani abu ne mai kyawu kuma wanda ya ke karbabbe ga hankali. A karkashin koyarwar addinin musulunci kowane mutum bisa yanayinsa zai iya karbar Ubangiji. Babu bukatar wani mahaluki ya zama tsaka-tsaki kamar pada ko pasto."Masanin falsafar nan dan kasar Jamus, Emmanuel Kent yana fadin cewa: " Idan har da akwai wani abu a duniyar nan wanda ya zama wajibi ga mutum ya kalle shi ido a bude to shi ne addini." A zamanin da mu ke ciki a yanzu, addini ya shiga cikin wani zango mai muhimmanci na tarihi. Tare da cewa da akwai matsaloli da dama da aka gindaya a gaban addini, musulunci ya ci gaba da yaduwa na azo a gani, kuma rawar da ya ke takawa a cikin al'umma tana karuwa."A cikin shekarun bayan nan an sami fitattun mutane a cikin fagage al'adu da wasanni da fasaha da dama a yammacin turai da su ka musulunta. Lokaci mai yawa bai gushe ba daga musuluntar madam Lauren Booth 'yar'uwar matar Tony Blair, wacce ta ke fitacciya a fage watsa labaru. Haka nan kuma Sean Stone wanda ya ke fitacce a fagen tsara fina-finan tarihi.Sean Stone Da ne ga Oliver Stone sanannen mai shirya fina-finan tarihi dan kasar Amurka. Saurayi ne dan shekaru 27 wanda ya karanta tarihin musulunci a cikin wata fitacciyar jami'a a Amurka.Stone ya zo Iran ne a lokacin da ake bukukuwan zagayowar ranakun cin nasarar juyin musulunci na wannan shekara. Ya kuma zo ne domin ya halarci wani taron karawa juna sani da aka shirya akan "Holywood da silma" Tafiyarsa zuwa Iran ta zama dalilin samun sauyi mafi muhimmanci a rayuwarsa. Dama tun a lokaci mai tsawo ne shaukin mika kai ga Ubangiji madaukakin sarki da kuma bauta masa ya ke ratsa zuciyarsa. Ganin da ya yi wa rayuwa da yanayi mai cike da koyarwa ta addini a Iran da kuma yadda musulmi su ke rayuwa cikin 'yan'uwantaka ya ja hankalinsa da kuma ingiza shi ya mika kai ga addinin musulunci. Ya kuma fisgu zuwa ga rayuwar Imam Ali (A.s.) abinda ya sa shi ya zabarwa kansa wannan suna.A cikin al'kur'ani mai girma da akwai misalai akan samari da matasa wadanda imani ya fisge su su ka kafircewa zaluncin mahukuntan zamaninsu sannan su ka mika wuya ga addini. Manufar wadannan samarin shi ne kauracewa rayuwa cikin gurbata ta al'ummarsu da kuma shirka domin samun tsira a karkashin imani. Sun roki Allah akan ya yi musu rahama ya tseratar da su kamar yadda ya zo a cikin suratu Kahfi a karkashin labarin Ashabul-Kahfi. Ubangiji kuwa ya karba musu addu'arsu ya basu karfin guiwa ya kuma shiryar da su.Imani da shauqi da Ali Stone ya ke da shi ya sami karbuwar daga rahamar Allah. Kuma tare da cewa ya fito ne daga cikin iyali da jininsu na yahudawa ne kuma mabiya addinin kirista,amma ya kima kai ga addinin musulunci da sakonsa na gaskiya. Ya fadi cewa: " A cikin addinin musulunci da akwai alaka ta kai tsaye a tsakanin Ubangiji da Mutum wanda hakan wani abu ne mai kyawu kuma wanda ya ke karbabbe ga hankali. A karkashin koyarwar addinin musulunci kowane mutum bisa yanayinsa zai iya karbar Ubangiji. Babu bukatar wani mahaluki ya zama tsaka-tsaki kamar pada ko pasto. .. Musulunci ci gaba ne na zancen Ubangiji. Ubangiji wanda ya aiko da annabi Ibrahim da annabi Musa" 9999Shakka babu salon rayuwa wacce ta wofinta daga addini da koyarwarsa a cikin nahiyar turai yana daga cikin abinda ya ke ingiza matasa da samari suna rungumar addinin musulunci. Fredrich Nitche, masanin falsafar nan dan kasar Jamus yana fada acikin littafins amai suna: "Lagaya Science" cewa: "Ci gaban turai ya wofinta daga ruhin addini. Kuma a cikin littafin ya ambato wani mahaukaci wanda ya ke yawo da fitila a hannu da tsakar rana yana cewa: "Ina neman Ubangiji." Wani mutum wanda ya ke maida martani ga wannan mahaukacin mutumin cikin isgili ya ce: "Shin Ubangiji ya bace ne ko kuma ya yi tafiya? "Wanann salon rubutun zube na Nitche yana magana ne akan yadda bil'adam ya kaucewa kiran Ubangiji da kin bin umarninsa. Sai dai Nitshce yana kore hakikar da ta ke cewa mutum yana da bukatuwa da ya farfado da ruhin addini domin ya kai ga cimma manufofinsa. Domin kuwa a karkashin imani da addini ne mutum zai iya yin rayuwa cikin daidaito.Ali Stone ya yi wa musulunci kyakkyawar fahimta da ya ke fadin cewa: " A cikin kasashen musulmi da akwai wani yanayi na musamman da ruhi na addini mai kyawu. Wata irin rayuwa ce wacce ta ke fisgar mutum zuwa gare ta." Haka nan ya yi hasashen cewa: " Ina fatan cewa musuluntar da na i zai taimakawa al'ummar Amurka su fahimci hakikanin musulunci, kuma kyawun da ya ke tattare da shi ya watsu a cikin al'umma. Manufata ita ce karafafa alaka a tsakanin yahudawa da kiristoci da kuma musulmi."Wannan mai shirya fim din dan kasar Amurka ya yi imani da cewa silma za ta iya taimakawa wjaen samar da yanayin da ya dace na hadin kai a tsakanin al'ummu da masu al'adu mabanbanta da harsuna mabanbanta. Ya kuma fadi cewa: "Ina fatan cewa za mu iya gina wata gada ta al'adu saboda mu iya hango da tsinkayo banbance-banbancen da ke cikinta. Wajibi ne a gare mu mu rika yin tunani akan yadda dan'adam zai rayu a cikin sa'ada, kuma mu yi kokarin sake gina rayuwar mutum ta hanya mafi dacewa. Ba mu da bukatar samar da kiyayyar wani addini a cikin al'umma. Mu fahimci cewa mahlicci guda daya ne tilo wanda shi ne mahaliccin komai da komai."Ali Stone ya bayyana halin da ya shiga alokacin da ya shiga musulunci. Ya fadi cewa: " A yayin da na shiga musulunci na ji cewa wani sabon ruhi ya shige ni. A hakikanin gaskiya na ji wani sabon karfi a tare da ni. Na ji kuma ji cewa na sami wata alaka ta musamman da Ubangiji."Har ila yau, Stone ya ce: "Fadi tashin da annabi Muhammadu ya yi wajen shiryar da mutane da kuma ilmantar da su shi ne dalilin musulunta ta."Ya kuma fadi cewa: Annabi Muhammad (a.s) ya hada kan mutane a lokacin da duniya ta ke cike da kafirci. Ina iya fahimtar jaruntar da ya nuna."Shakka babu Ali Stone ba shi ne mutum na karshe da ya karbi musulunci. Da akwai kididdigar da ta ke nuni da cewa, ana samun masu karbar musulunci da dama a cikin yammacin turai. Domin kuwa musulunci addini ne na rayuwa wanda ya ke da karfin taka rawa a cikin rayuwa ta daidaikun mutane da kuma al'umma."

Add comment


Security code
Refresh