An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 18 June 2011 14:04

Wakafi {8}

Wakafi {8}
A ci gaba da bayanin da muke yi kan hukunce-hukuncen wakafi a shirinmu na yau ma zamu gabatar muku da wasu hukunce-hukunce ne kan sharuddan wakili a kan wakafi karkashin fatawowin jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatull... Sayyid Ali Khamene'i {hafizahull...}, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa. Tambaya:- Shin ya halatta ga wanda ba wakili ba ne na shari'a a kan wakafi ya dauki matakin tsoma baki a al'amarin gudanar da wakafi da canja sharuddan da aka gindaya a lokacin gabatar da wakafin? Kuma shin ya halatta a gare shi ya bukaci wakilin wakafi na shari'a kan ya mika filin da aka bada wakafinsa ga wani mutum na daban domin ya gudanar da al'amarin wakafin, duk kuwa da cewa wakilin wakafin na shari'a baya ganin mutumin da aka gabatar masa shi ya dace da gudanar da al'amarin wannan wakafin? Amsa:- Gudanar da al'amarin wakafi daidai da tsarin da mai wakafin na asali ya gindaya a lokacin gabatar da wakafin, hakki ne kawai na mutumin da aka wakilta shi domin gudanar da al'amarin wannan wakafin, idan kuma mai wakafin na asali bai wakilta wanda zai gudanar da al'amarin wakafin ba, to hakkin gudanar da al'amarin wannan wakafin yana hannun shugaban musulmi ne, don haka babu wanda ke da hakkin tsoma baki a harkar gudanar da al'amarin wakafin, kamar yadda babu wanda ke da hakkin canja tsarin gudanar da al'amarin wakafin ko juyar da akalar sharuddan da aka gindaya a lokacin gabatar da wakafin koda kuwa mutumin da aka wakilta shi ne domin gudanar da wakafin. Tambaya:- Idan mai wakafi na asali ya gabatar da wani mutum a matsayin wanda zai sanya ido da kula da wakafin da ya bayar, kuma ya gindaya sharadin cewa babu wanda ke da hakkin tsige shi daga kan wannan matsayin na mai sanya ido da kula da wannan wakafin sai shugaban musulmi; shin a nan ya halatta ga mutumin da aka bashi wakilcin sanya idon ya dauki matakin yin murabus daga kan wannan matsayin ko kuma bai halatta ba?. Amsa:- Baya halatta ga mutumin da aka nada shi a matsayin mai sanya ido kan wakafi ya yi murabus daga kan wannan matsayin bayan ya amince ya karbi matsayin tun da fari, kamar yadda baya halatta ga mutumin da aka wakilta shi a kan kula da al'amarin wakafi ya dauki matakin yin murabus daga kan wannan matsayin.  
More in this category: Wakafi {7} »

Add comment


Security code
Refresh