An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 18 June 2011 14:03

Wakafi {7}

A shirinmu na wannan mako zamu ci gaba da bijiro muku da hukunce-hukunce ne kan sharuddan wakili a kan wakafi karkashin fatawowin jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatull... Sayyid Ali Khamene'i {hafizahull...}, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa.Tambaya:- Idan mutum ya bada wani abu da ya mallaka a matsayin wakafi domin amfani da abin da ake samu daga wannan abin da ya bayar wakafin a wasu hanyoyin alheri kebantattu misalin taimakawa zuriyar ahlul-baiti wato sharifai da gudanar da tarukan juyayin mutuwa, to a halin yanzu farashin kudin haya ya tashi kuma abin da ya bayar wakafi ana bada hayarsa ne, don haka wasu cibiyoyi ko mutane suka nemi a ba su hayar wannan abin da aka bada wakafinsa a farashi kasa da yadda ake bada shi haya saboda a yanzu bashi da cikekken daraja ko kuma saboda wasu dalilai na daban misalin al'ada ko siyasa ko zamantakewa ko kuma addini, shin ya halatta ga masu kula da wannan wakafin su bada hayarsa a kan farashi kasa da yadda ake bada haya a yanzu?. Amsa:- Wajibi ne a kan wakili na shari'a da ke kula da al'amarin gudanar da wakafi ya kiyaye masalaha da amfanin wannan wakafin a bangaren bada hayarsa da tsaida farashinsa ga duk mai neman karbar hayar wakafin, idan kuma ya kasance rage farashin hayar wakafin saboda wani dalili ko yana yi ko kuma aikin da za a gudanar da wannan wakafin a matsayin haya yana da muhimmanci ga wakafin da haka zai zame masalaha da amfani ga wannan wakafin, to babu matsala a rage farashin bada hayar wakafin, amma idan babu wata masalaha ko amfani, to baya halatta a rage farashin bada hayar wannan wakafin. Tambaya:- Kamar yadda a bisa fatawar marigayi Imam Khomeini {r.a} masallaci bashi da wakili da zai kula da wakafinsa; shin wannan hukunci ya hada hard a sauran kayayyakin da aka gabatar ga masallacin a matsayin wakafi, misalin kayayyakin da aka gabatar domin gudanar da tarukan juyayi da wa'azzuzzuka da shiryarwa da kuma hukunce-hukuncen shari'a a masallacin da makamantansu? Idan kuma hukuncin ya hada da su dukka, to kasancewar mafi yawan masallatai akwai kayayyakin da aka gabatar da su a matsayin wakafi kuma a bisa doka da tsarin shari'a akwai masu kula da wadannan kayayyakin, har ma cibiyar kula da wakafi tana ma'amala da su a matsayin masu kula da al'amarin wakafin kayayyakin masallaci, shin ya halatta ga masu kula da al'amarin wadannan wakafin su janye hannuwarsu daga kan gudanar da wannan wakafin duk kuwa da cewa a bisa fatawar marigayi Imam Khomeini {r.a} wakili a kan wakafi baya da hakkin janyewa daga kan matsayinsa na mai kula da al'amuran wakafi, kai wajibi ne a kansa ya yi aiki daidai da tsarin da mai wakafin na asali ya shimfida ba tare da tauyaye wani abu ba?. Amsa:- Hukuncin cewa masallaci bashi da wakili da zai kula da wakafinsa hukuncin ya takaita ne kawai a kan masallaci, amma ban da sauran kayayyaki da aka gabatar da su ga masallacin a matsayin wakafi musamman kayayyakin da aka bada su ga masallaci domin koyar da hukunce-hukuncen shari'a da gabatar da wa'azi da shiryarwa da makamantansu, don haka babu matsala a nada wakili da zai kula da al'amarin gudanar da kayayyakin da aka bada su ga wakafi na musamman wato wakafin da aka gabatar ga wasu kebantattun mutane ko bangare, haka nan wakafin da aka bada su ga wasu nau'in jama'a ko bangarori, kai har misalin kayan da aka gabatar domin bukatun masallaci misalin tabarma, dadduma, fitilu da kayayyakin tsabtace masallacin da makamantansu, kuma mutumin da aka wakilta shi kan kula da al'amuran gudanar da wakafin baya da hakkin janyewa daga kan wannan matsayin, kai wajibi ne a kansa ya gudanar da al'amarin wakafin daidai da tsarin da mai wakafin na asali ya shimfida a lokacin gabatar da wakafin, don haka baya halatta ga wani mutum na daban ya dauki matakin takura masa a al'amarin gudanar da wannan wakafin.
More in this category: « Wakafi {8} Wakafi {6} »

Add comment


Security code
Refresh