An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 18 June 2011 14:02

Wakafi {6}

A bayanin da muke yi kan hukunce-hukuncen wakafi karkashin fatawowin jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatulll... Sayyid Ali Khamene'i {hafizahull...}, a yau ma zamu ci gaba da bijiro muku da hukunce- hukunce ne kan Sharuddan Wakili A Kan Wakafi, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa. Tambaya:- Shin a shari'a ya inganta wadanda aka wakilta su wajen kula da wakafi su dauki matakin tsige wasu daga cikinsu daga kan matsayinsu na masu kula da wannan wakafin?. Amsa:- Baya inganta su dauki matakin tsige wasu daga cikinsu kuma koda sun tsige su, to wannan tsigewar ba ta inganta ba, matukar mai asalin wakafin bai ba su hakkin tsige wasu daga cikinsu ba a lokacin kulla yarjejeniyar wakilcin kula da wakafin. Tambaya:- Idan wasu daga cikin wadanda aka wakilta kan kula da wakafi suka yi da'awar cewa; wani daga cikinsu maha'inci ne, kuma suka dage kan sai sun tsige shi daga kan matsayinsa na wakili, shin a nan mene ne hukuncin shari'a?. Amsa:- Wajibi ne a kansu su gabatar da batun zargin da suke masa na ha'inci ga hakimus-shara'i wato Marja'i da ake komawa gare shi domin yin aiki da fatawowinsa. Tambaya:- Idan mutum ya bada filinsa a matsayin wakafi domin amfanin al'umma kuma ya sanya hakkin kula da wannan wakafin wa kansa matukar yana raye, sannan bayan rasuwarsa ga babban dansa daga cikin maza, kuma ya bashi matsayi na musamman wajen gudanar da wakafin, shin cibiyar gudanar da wakafi da kula da al'amuran taimako tana da hakkin janye dukkanin wadannan matsayi da iko na musamman ko wasu daga cikinsu daga hannun wakilin da ke kula da wakafin?. Amsa:- Wakilin da asalin mai wakafi ya wakilta shi kan kula da wakafi matukar bai kauce daga kan sharuddan gudanar da wakafin ba, to yana da hakkin gudanar da al'amuran wannan wakafin kamar yadda mai asalin wakafin ya furta a lokacin kulla yarjejeniyar wannan wakafin, don haka baya inganta a shari'a a dauki matakin canja akalar ayyukan da asalin mai wakafin ya tsara a lokacin furta yarjejeniyar wakafin. Tambaya:- Mutum ne ya bada wakafin wani yankin filinsa ga masallaci kuma ya sanya wakilcin kula da wakafin ga 'ya'yayensa da zasu fito daga tsatsonsa kuma bayan karewarsu sai al'amarin kula da wakafin ya koma ga wanda ke limanci salloli biyar a wannan masallacin, don haka bayan karewar zuriyar mai asalin wakafin sai malamin da ke jagorantar salla a masallacin na tsawon wani lokaci ya karbi ragamar kula da wakafin, sai dai a halin yanzu yana fama da ciwon zuciya, don haka ba zai iya jagorantar salla a masallacin ba, sakamakon haka sai kwamitin limamai ya gabatar da wani malami domin jagorantar salla a wannan masallacin a halin yanzu, shin nada sabon limami a masallacin yana matsayin shige limamin da ya kamu da rashin lafiya ne daga kan wakilcin wannan wakafin ko kuma har yanzu limamin da bashi da lafiya yana da hakkin wakilta wanda zai wakilce shi wajen gudanar da salla a masallacin kuma yana nan a kan wakilcin kula da wakafin?. Amsa:- Idan aka dauka cewa wakilcin wannan malamin a kan wakafin saboda kasancewarsa limami ne a wannan masallacin, to a halin yanzu wakilcinsa kan wakafin ya kawo karshe sakamakon rashin yiyuwar jagorantar salla a masallacin saboda rashin lafiya da yake fama da shi ko wani dalili na daban.
More in this category: « Wakafi {7} Wakafi {5} »

Add comment


Security code
Refresh