An Dakatar Da Wannan Shafin. Mun Koma Zuwa Parstoday Hausa
Saturday, 18 June 2011 14:01

Wakafi {5}

A bayanin da muke yi kan hukunce-hukuncen wakafi karkashin fatawowin jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatulll... Sayyid Ali Khamene'i {hafizahull...}, a yau ma zamu ci gaba da bijiro muku da hukunce hukunce ne kan Sharuddan Wakili A Kan Wakafi, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa. Tambaya:- Ma'abuta gidaje da filaye da suke makobtaka da wani masallaci sun gabatar da wasu yankunan filayensu ga masallacin domin fadada shi, don haka limamin wannan masallacin ya dauki matakin rubuta yarjejeniyar wakafin wannan filayen bayan gudanar da shawarwari da sauran malamai, kuma dukkanin mutanen da suka bada filayensu ga masallacin sun amince da wannan mataki, sai dai wanda ya gina masallacin tun da fari yaki amincewa da wannan mataki na liman saboda yana bukatar sanya sabon wakafin cikin tsohuwar yarjejeniyar wakafin masallacin don ya kasance shi ne ke kula da dukkanin wakafin wannan masallacin, shin yana da hakkin neman hakan? kuma wajibi ne a amince da wannan bukatar tasa?. Amsa:- Filayen da aka gabatar da su ga masallaci domin fadada shi, al'amarin wakafinsu da tsara yarjejeniyar wakafin da kuma gabatar da mai kula da wakafin duk hakki ne na wadanda suka bada wadannan filayen a matsayin wakafi, don haka mai kula da wakafin masallacin tun da fari baya da hakkin da zai nuna rashin amincewarsa kan haka. Tambaya:- Idan masu kula da Husainiyya bayan gabatar da shi a matsayin wakafi suka tsara wasu dokokin gudanar da wannan Husainiyyar amma wasu daga cikin tsarin dokokin sun yi hannun riga da manufar gabatar da wannan wakafin, shin a shari'a ya inganta yin aiki da wadannan dokokin? Amsa:- Wadanda aka wakilta su domin kula da wakafin Husainiyyar ba su da hakkin gabatar da wani abu da zai yi hannun riga da manufar gabatar da wakafin kuma a shari'a baya halatta yin aiki da shi.Tambaya:- Idan aka wakilta mutane da dama a kan kula da wakafi, shin a shari'a ya inganta wasu daga cikinsu su dauki matakin gudanar da wakafin ba tare da ra'ayin sauran wakilan ba? Idan kuma aka samu sabanin ra'ayi dangane da batun gudanar da al'amuran wakafin, shin ya halatta ga kowane daga cikinsu ya yi aiki da ra'ayinsa ko kuma wajibi ne a kansu kowa ya ajiye ra'ayinsa gefe guda su koma ga hakimus-shara'i wato Marja'i da ake komawa gare shi domin yin aiki da fatawarsa?. Amsa:- Idan mai asalin wakafin ya wakilta sune dukkaninsu kuma babu wata ishara da ya yi wadda ta bai wa wasu daga cikinsu ko mafi yawansu damar gudanar da wakafin kan ra'ayinsu, to babu wani daga cikinsu koda mafi yawansu ne da ke da hakkin gudanar da al'amarin wakafin bisa ra'ayinsa koda kuwa wani bangare ne na wakafin, don haka wajibi ne a kansu dukkaninsu su gudanar da shawara a tsakaninsu don cimma ra'ayi guda wajen gudanar da al'amuran wakafin. Idan kuma suka samu sabani ko rikici a tsakaninsu, to wajibi ne su koma ga hakimus-shara'i wato Marja'i da ake komawa gare shi domin yin aiki da fatawarsa don hada su a kan ra'ayi guda.
More in this category: « Wakafi {6} Wakafi {4} »

Add comment


Security code
Refresh